Rikicin Boko Haram Da ISWAP: An Kashe Masunta 18, Mutane Da Yawa Sun Bace
Published: 1st, May 2025 GMT
Ƴan ta’addan Boko Haram sun kashe masunta 18, a wani harin da suka kai a yankin Mobbar, wanda ke arewacin Jihar Borno, kusa da iyakar Jamhuriyar Nijar. Harin ya faru ne a kogin Fadana-Garuwa a yankin Duji, lokacin da mayakan suka kai hari cikin ruwan, inda suka zargi masu kamun kifin da haɗin kai da ‘yan ta’addan ISWAP.
A cewar wani mai kamun kifi da ya yi magana da wakilinmu, Boko Haram sun zo da yawan gaske suka yi ta kai hari kan masu kamun kifin, suna zargin su da kai rahoton maɓoyarsu ga ‘yan ta’addan ISWAP. Sun tattara su duka, suka kashe su, sannan suka yi barazanar cewa wannan hukunci ne ga wanda ke aiki tare da ISWAP.
Mayaƙan ISWAP Da Boko Haram 4 Sun Tuba Sun Miƙa Wuya A Borno Talauci Da Rashin Ilimi Ne Ya Sa Ayyukan Boko Haram Ke Dawowa – Gwamnan YobeAn tabbatar da cewa yankin na cikin ikon Boko Haram da sauran ruwan da ke kusa da iyakar Nijar, kuma wannan hari yana da alaƙa da rikicin dake tsakanin bangarorin Boko Haram da ISWAP. An samu gawarwakin mutanen 18, yayin da wasu da dama suka bace. Tuni al’ummar yankin suka gudanar da jana’izar su bisa tsarin Musulunci.
A cikin watannin da suka gabata, duka ɓangarorin Boko Haram da ISWAP sun ƙara yawan hare-haren su kan fararen hula da sansanin Soja a jihohin Borno, Yobe, da Adamawa, wanda ya haifar da ƙarin tashe-tashen hankula a yankin.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Boko Haram ISWAP Boko Haram Da Boko Haram da
এছাড়াও পড়ুন:
An Cafke Ma’aikatan Gidan Marayu Da Suka Sayar Da Yara 4 A Kan Naira Miliyan 3
“Haka kuma an kama wata mata mai shekaru 34 da ake zargi da hannu a lamarin, tare da wasu masu gidan marayu guda biyu da ke Abuja da Jihar Nasarawa, inda aka gano wasu yaran da ake kyautata zaton an yi safarar su. Wasu daga cikin gidajen marayun da aka gano ana amfani da su ne a matsayin cibiyoyin ajiye yara, inda ake jiran ‘kwace’ ko sayar da su da sunan daukar nauyin marayu.”
Ya ce, “An gano gidajen marayu guda hudu da ke Kaigini, Kubwa Edpressway Abuja; Masaka Area 1, Mararaba kusa da Abaca Road; da kuma Mararaba bayan Kasuwar Duniya suna da alaka da wannan kungiya, kuma ana ci gaba da bincike a kansu.”
Ya kara da cewa, daya daga cikin masu korafin ya bayyana cewa ya biya Naira miliyan 2.8 a matsayin kudin daukar yaro, sannan ya biya Naira 100,000 a matsayin kudin shawara ga daya daga cikin ‘yan kungiyar.
Sanarwar ta kara da cewa, “Wani mai korafi ya ce shi ma ya biya Naira miliyan 2.8 kudin daukar yaro da Naira 100,000 kudin shawara ga wani dan kungiyar.
“An canza sunayen yawancin yaran da aka ceto, lamarin da ya kara wahalar da bincike da gano asalinsu,” in ji sanarwar.
Darakta Janar ta NAPTIP, Binta Adamu Bello, ta bayyana damuwarta kan wannan lamari, inda ta ce safarar yara ta zama babbar matsala a kasa.
Ta hanyar Adekoye, DG din ta nuna damuwa game da yadda wasu gidajen marayu ke amfani da raunin jama’a wajen aiwatar da safarar yara.
Ta ce, “Abin takaici ne yadda wasu masu mugunta da ke da sunayen kwararru da matsayi a cikin al’umma, suke amfani da matsayin su wajen yaudarar mutanen da ke cikin mawuyacin hali, su yi safarar ‘ya’yansu, da dama daga cikinsu ma sun tsira ne daga halaka a lokacin rikice-rikicen al’umma ko na manoma da makiyaya, sannan a sayar da su ga iyaye masu neman haihuwa a matsayin daukar yaro ba tare da sahihin izinin iyayensu ba.
“Wannan abin ba za a yarda da shi ba, kuma wadanda aka kama kan wannan mugun aiki za su fuskanci hukuncin doka yadda ya kamata.
“’Ya’yanmu ba kayayyaki ba ne da za a ajiye su a gidajen marayu a sayar ga mai biyan mafi tsada. Wannan dole ya tsaya,” in ji ta.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA