Iran da Nijar sun rattaba hannu kan yarjeniyoyin hadin gwiwa
Published: 1st, May 2025 GMT
Kasashen Iran da Nijar sun gudanar da taron kwamitin hadin gwiwa kan tattalin arziki.
An gudanar da taron ne a gefen taron baje koli na Iran 2025, karo na bakwai na Jamhuriyar Musulunci ta Iran, wanda aka fara a birnin Tehran a ranar Litinin.
Mohammad Atabak, ministan masana’antu, ma’adinai, da kasuwanci na Iran; da Mohammad Ali Dehghan Dehnavi, shugaban kungiyar bunkasa kasuwanci ta Iran; da Sahabi Oumarou, ministan mai na Nijar, ne suka halarci taron.
Da yake jawabi a wajen taron, Atabak ya ce, bayan shafe shekaru 13 da aka shafe ana aikin kwamitin hadin gwiwa tsakanin Iran da Nijar, “Muna fatan inganta dangantakar tattalin arziki tsakanin kasashenmu biyu ta hanyar wannan takardar hadin gwiwa.”
Dehghan Dehnavi ya jaddada cewa, an gudanar da tattaunawa mai zurfi a cikin kwanaki biyun da suka gabata, inda masana suka yi nazari tare da musayar wasu tanade-tanade na hadin gwiwa tsakanin Iran da Nijar.
Ya ci gaba da cewa kwararrun da suka halarci taron sun amince da ci gaba da yin hadin gwiwa tsakanin Iran da Nijar a bangarori da dama.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: Iran da Nijar hadin gwiwa
এছাড়াও পড়ুন:
Amurka Ta Kakabawa Kamfanonin Da Suka Hulda Da Iran Bangaren Man Fetur
A dai-dai lokacin da kasashen Amurka da JMI suke ci gaba da tattaunawa kan shirin makamashin nukliya ta Iran gwamnatin Amurka a jiya Laraba ta dorawa kamfanoni da mutanen da suke mu’amala da JMI a bangaren man Fetur takunkuman tattalin arziki. Da dama daga cikin wadannan kamfanoni na kasar China ne.
Jaridar ‘the Nation’ ta Amurka ta ce tun farkon wannan shekarar ne shugaban Trump ta farfado da takurawar tattalin arziki mafi muni a ka kasar Iran da nufin tilasta mata dawowa teburin tattaunawa ko kuma ta wagaza cibiyoyin Nukliyar kasar.
A halin yanzu dai kasashen biyu zasu ci gaba da tattaunawar ba kai tsaye ba, karo na hudu a birnin Roma na kasar Italiya a ranar Asabr mai zuwa. Kuma mai yuwa daga karshe su samarda sabuwar yarjeniya a tsakaninsu, kuma akwai yiuwar su kasa yin haka.
Wannan kuma zai faru ne idan Amurka ta bukaci JMI ta daina mu’amala da sinadarin Uranium kwatakwata ko kuma ta shigar da wata bukata wacce Iran ba zata amince ba.