Dakarun IRGC Na JMI Sun Kaddamar Da Sabon Kwale-Kwale Mai Cilla Makamai Masu Linzami
Published: 1st, May 2025 GMT
Rear Admiral Alireza Tangsiri babban kwamandan sojojin ruwa na dakarun IRGC ya bayyana haka ne a jiya a bikin ranar “Tekun farisa’ ta kasa.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa kwale-kwalen mai sauran kilomita Knots 116 na ruwa wanda yayi dai-dai da kilomita 215 / a ko wace sa’a yana da kayan aikin cilla makamai masu linzami.
Kwamandan ya kara da cewa, wannan yana daga cikin shirin JMI na karfafa tsoron kasar, kuma sako ne ga makiya su san da haka, sannan sakon zaman lafiya ga makobta da abokai.
An sanya ranar da turawan Portigal suka fice daga tekun farisa da mashigar ruwa ta Hurmus shekaru 1622 da suka gabata, a matsayin ranar tekunfarisa ta kasa.
A lokacinda yake karin bayani kan wannan kwale-kwalen Tangsiri ya cewa sun gina wannan karamin jirgin mai cilla makamai masu linzami, a lokacinda yake gudun saurin kilimita 215 ne don kyautata tsaron taken farisa, da kuma nuna karfin JMI na tabbatar da zaman lafiya a dukkan yanken tekun na farisa.
Yace Iran bata son samuwar sojojin kasashen waje, musamman Amurka dawasu kasashne turai a yankin, don ba abinda samuwarsu suke haddasawa a yankin sai rashin tsaro da zaman lafiya a cikinsu.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
’Yan sanda sun sasanta rikicin asibitin AKTH da KEDCO
Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kano ta shiga tsakani don sasanta rikicin da ya ɓarke tsakanin Asibitin Koyarwa na Aminu Kano (AKTH) da Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Shiyyar Kano (KEDCO).
Rikicin ya samo asali ne daga katse wutar lantarki da asibitin ya zargi KEDCO da yi, inda ya ce hakan ya kawo cikas ga ayyukan lafiya masu muhimmanci a asibitin, ciki har da zargin mutuwar marasa lafiya.
Sasantawar da Kwamishinan ‘Yan Sandan Kano, Ibrahim Adamu Bakori, ya jagoranta ta biyo bayan zarge-zargen cewa katsewar wutar ta haddasa mutuwar wasu marasa lafiya da ke kan na’urar taimakon numfashi a asibitin.
Sai dai KEDCO ya musanta zargin a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin, yana mai cewa asibitin na kokarin bata sunansa ne kawai.
A cewar mai magana da yawun ‘yan sanda na Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa, an gudanar da taron sasancin ne a hedikwatar ‘yan sandan Kano da ke Bompai, inda aka zauna da Shugaban asibitin, Farfesa Abdulrahman Abba Sheshe, da Shugaban KEDCO, Abubakar Shuaibu Jimeta.
Taron ya mayar da hankali ne kan warware tankiyar da kuma dawo da wutar lantarki ga asibitin, wanda ke ya fuskanci matsaloli sakamakon katse wutar.
Sanarwar ta ce, “Bangarorin biyu sun nuna godiya ga matakin gaggawa da ‘yan sanda suka dauka. KEDCO ya amince da dawo da wutar lantarki nan take, alamar cewa rikicin ya zo karshe.”
Kiyawa ya kara da cewa, “Rundunar ‘Yan Sanda ta jaddada kudirinta na kare rayuka da dukiyoyi, tare da tabbatar da ci gaba da aiki ba tare da tangarda ba a bangaren kiwon lafiya.”
Sanarwar ta kuma ce kwamishinan ‘yan sanda ya yaba wa AKTH da KEDCO bisa hadin kai, tare da alkawarin ci gaba da goyon baya don tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar.