Kamala Harris Ta Zargi Trump Da Haddasa Taɓarɓarewar Tattalin Arziƙi
Published: 1st, May 2025 GMT
‘Yar takarar shugaban ƙasar Amurka da ta sha kaye a zaɓen da aka yi, ƙarƙashin jam’iyyar Democrat, Kamala Harris ta zargi shugaba Donald Trump da tunzura abin da ta kira taɓarɓarewar tattalin arziƙin ƙasar.
Ms Harris ta kuma zargi Mr Trump da jefa ƙasar cikin ruɗani da salon mulkin da ke jefa tsoro a zukatan jama’a.
Ta ce abin da suka kasa ganewa shi ne, tsoratarwa ba ita ce kaɗai hanyar magance matsala ba, ƙwarin gwiwa ake buƙata.
Tattalin arziƙin Amurka ya samu koma baya a rububin farko na wannan shekarar, idan aka kwatanta da bunƙasar shi a shekaru hudu na mulkin shugaba Joe Biden.
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Haris
এছাড়াও পড়ুন:
Xi Ya Jaddada Muhimmancin Tsara Nagartaccen Shirin Raya Tattalin Arziki Da Zamantakewar Al’umma Tsakanin 2026-2030
A cewarsa, wajibi ne shirin ya mayar da hankali kan burin cimma zamanantarwa irin ta gurguzu da nufin gina babbar kasa da samun ci gaba wajen farfado da ita. Shirin raya kasa na shekaru biyar-biyar, wanda shi ne daftarin dake zaman jigon jagorantar ci gaba na matsakaici da dogon zango a bangaren tattalin arziki da zamantakewar kasar Sin, yana zayyana baki dayan burikan kasar da manyan ayyuka da manufofin da ake aiwatarwa a dukkan bangarori cikin shekaru 5. (Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp