Ana sa alamar tambayar cewa: Shin gobarar da ta tashi a birnin Kudus… shin sako ne na ranar tunawa da kafuwar gwamnatin ‘yan sahayoniyya?

Gobarar da ta tashi a tsaunin Kudus da aka mamaye ta bazu zuwa manyan yankuna a cikin haramtacciyar kasar Isra’ila, inda ta kewaye wani sansanin soji tare da cinye filayen masu girma da tsayi.

Hakan ya sa hukumomin gwamnatin mamayar Isra’ila suka kafa dokar ta baci tare da neman taimakon kasashen duniya. Yayin da Ministan tsaron cikin gidan Isra’ila Itamar Ben-Gvir yake neman dora wa Falasdinawa, alhakin tashin gobarar.

Gobarar ta kunno kai ne a daidai lokacin da yahudawan sahayoniyya suka fara gudanar da bukukuwan cika shekaru 77 da kafuwar gwamnatinsu ta mamaya a kasar Falasdinawa, gobara mai karfin gaske ta barke a tsaunukan birnin Kudus ta kuma bazu zuwa manyan yankuna masu girma.

Gobarar ta tashi ne a kusa da babbar hanyar da ke tsakanin Kudus da Tel Aviv, lamarin da ya kawo yawaitar cunkoson ababen hawa a manyan tituna. Gobarar ta yi sanadin jikkatar mutane masu yawa, kuma ta tilastawa hukumomin gwamnatin mamaya fara kwashe yahudawan sahayoniyya ‘yan kaka gida daga gidajensu da ma marasa lafiya daga Asibitin Hadassah Ein Kerem da ke birnin Kudus saboda gobarar.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Za a fara yi wa ɗaliban jami’o’i gwajin ƙwaya — Gwamnatin Nijeriya

Gwamnatin Nijeriya ta bayanna cewa za ta soma yi wa ɗaliban jami’o’in ƙasar nan gwajin miyagun ƙwayoyi a wani mataki na daƙile yaɗuwar ta’ammali da ƙwayoyin.

Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya NAN ya ruwaito cewa, Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya tare da haɗin gwiwar Hukumar Yaƙi da Fataucin Miyagun Kwayoyi NDLEA ne za su jagoranci aikin.

Sarkin Gudi na Jihar Yobe, Isa Bunuwo Ibn Khaji ya rasu Gwamnatin Jigawa ta horas da malamai 20,000 fasahar sadarwar zamani

Hakan na zuwa ne bayan ganawar Shugaban Hukumar NDLEA, Birgediya Janar Buba Marwa mai ritaya da kuma ministan ilimin ƙasar, Olatunji Alausa a jiya Laraba.

Ɓangarorin biyu sun kuma amince da ɓullo da daftarin koyar da darasin ilimin ta’ammali da ƙwayoyi a makarantun sakandiren ƙasar.

Buba Marwa wanda ya jagoranci tawagar jagororin hukumar NDLEA ya bayyana cewa gwajin ƙwayar zai shafi duk ɗaliban jami’o’in da sabbin da za su shiga.

Yayin da yake jawabi a wajen ganawar, Buba Marwa ya ce za su mayar da hankali ne kan makarantun ƙasar, waɗanda ya ce akwai miliyoyin yara da ke ƙarƙashin kulawar ma’aikatar ilimin ƙasar.

Buba Marwa ya ce rashin daƙile ta’ammali da miyagun ƙwayoyi daga wajen ƙananan yara ya taimaka wajen jefa matasan ƙasar cikin ayyukan ta’addanci da fashin daji da sauran miyagun laifuka.

Ya bayyana mummunan tasirin shan miyagun ƙwayoyi a kan matasan ƙasar, yana mai cewa yaƙi da miyagun ƙwayoyi yaki ne don ceton rayukan matasan Nijeriya.

Marwa ya ce a yanzu hankalin hukumar zai fi karkata ne zuwa makarantu da cibiyoyin ilimi, yana mai ƙarawa da cewa akwai miliyoyin yaran Nijeriya da ke ƙarƙashin kulawar ma’aikatar ilimi, kuma wannan abu ne mai matuƙar muhimmanci.

Shugaban hukumar ta NDLEAn ya ce a dalilin goyon bayan da suka samu karkashin Gwamnatin Shugaba Bola Tinubu a tsawon shekaru biyu da suka gabata, hukumar ta kama mutane 40,887 da ake zargi da aikata laifuka, ta daure 8,682, kuma ta kwace tan 5,507 na miyagun ƙwayoyi.

A cewarsa, tun daga watan Janairu bara, an ƙwace ƙwayar tramadol da ta wuce ƙwaya biliyan ɗaya, wanda kudinta ya fi naira tiriliyan ɗaya.

Shugaban NDLEA ya jaddada cewa Shugaba Tinubu yana kuma tallafa wa hukumar wajen gina cibiyoyi bakwai na gyaran masu fama da shan miyagun ƙwayoyi, baya ga sauran cibiyoyi 30 da ke karkashin umarnin NDLEA a faɗin ƙasa.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Za a fara yi wa ɗaliban jami’o’i gwajin ƙwaya — Gwamnatin Nijeriya
  • ZAMFARA: APC Ta Bukaci Gwamnatin Tarayya Ta Kawo Dauki Don Matsalar Tsaro Na Kara Tsananta
  • Faransa Za Ta Fara Jefa Kayan Agaji Ta Sama A Gaza
  • Sojojin Yemen Sun Kai Zafafan Hare-Hare Kan Haramtacciyar Kasar Isra’ila Guda Uku  
  • Manyan makarantu 2 ne kacal ke da rajista a Katsina — Gwamnati
  • Tinubu ya naɗa sabon shugaban hukumar kashe gobara ta ƙasa
  •  Yahudawa ‘Yan Share Wuri Zauna Sun Kutsa Cikin Masallacin Kudus
  • Amincewa Da Kasar Falasɗinu: Birtaniya Ta Gindaya Wa Isra’ila Sharuɗɗa
  • Gwamnatin Sakkwato Ta Sayo Manyan Tan-tan 250 Na Sama Da Naira Biliyan 22
  • Ma’aikatar Leken Asirin JMI Ta Ce Ta Gano Shirin Kashe Manyan Mutane 35 a kasar