Radio Nigeria Kaduna Hausa:
2025-05-01@15:54:51 GMT

Inter Milan Ta Je Ta Rike Barcelona A Champions League

Published: 1st, May 2025 GMT

Inter Milan Ta Je Ta Rike Barcelona A Champions League

An tashi 3-3 tsakanin Barcelona da Inter Milan a wasan farko zagayen daf da karshe a Champions League da suka kara a Sifaniya ranar Laraba.

Inter Milan ce ta fara cin ƙwallo a daƙiƙa 30 da take leda ta hannun Marcus Thuram, ya zama na farko da ya ci ƙwallo a ƙanƙanin lokaci a daf da karshe a Champions League.

Daga nan Inter ta kara na biyu ta hannun Denzel Dumfries, wanda ya zama na farko daga Netherlands da ya ci ƙwallo ya kuma bayar aka zura a raga a daf da karshe a Champions League, tun bayan Wesley Sneijder a Inter a karawa da Barcelona.

Dumfries shi ne ya bai wa Thuram ƙwallon farko da Inter Milan ta zura a ragar Barcelona cikin ƙanƙanin lokaci.

Barcelona ta sa namijin ƙwazo a wasan, inda Lamine Yamal ya zare ɗaye a minti na 24 a wasan na hamayya.

Haka kuma ƙungiyar Sifaniya ta farke na biyun ta hannun Ferran Torres, bayan da Raphinha ya samar masa damar zura ƙwallon a cikin raga cikin sauƙi.

Ana tsaka da wasa Inter Milan ta kara na uku ta hannun Denzel Dumfries, sai dai minti biyu tsakani mai tsaron ragar Inter, Yann Sommer ya ci gida.

Kenan ta sanadin Raphinha, wanda shi ne ya buga tamaular – hakan ya sa ya yi kan-kan-kan da Cristiano Ronaldo, wanda yake da hannu a cin ƙwallo 20 a Champions League a 2013/14.

Raphinha, ɗan wasan tawagar Brazil, ya zura 12 a raga ya kuma yi sanadin cin tara a bana a babbar gasar tamaula ta nahiyar Turai.

Barcelona da Inter Milan sun fuskanci juna karo na 17 a babbar gasar zakarun Turai, inda ƙungiyar Sifaniya ta yi nasara takwas da canjaras shida aka doke ta wasa uku.

Barcelona ta yi wasa shida ba tare da an doke ta ba a gida a fafatawa da Inter Milan kenan a Champions League, wadda ta yi nasara biyar da canjaras ta biyu.

Kocin Inter Milan, Simone Inzaghi, ya ja ragamar wasa na 50 a Champions League, ya zama mai horarwa na bakwai daga Italiya da ya yi wannan ƙwazon.

Ranar Talata 6 ga watan Mayu, Inter Milan za ta karɓi bakuncin Barcelona a wasa na biyu zagayen daf da karshe a Champions League a Italiya.

Barcelona ta kawo wannan matakin bayan yin waje da Borussia Dortmund, ita kuwa Inter Milan ita ce ta fitar da Bayern Munich a zagayen kwata fainal.

Barcelona tana matakin farko a teburin La Liga da tazarar maki huɗu tsakani da Real Madrid ta biyu a kakar nan.

Ita kuwa Inter Milan tana ta biyun teburin Serie A da tazarar maki uku tsakani da Napoli mai jan ragamar babbar gasar tamaula ta Italiya.

Inter za ta karɓi bakuncin Verona a gasar Serie A ranar Asabar 3 ga watan Mayu, sannan ta kece raini da Barcelona a Italiya a Champions League ranar Talata.

Barcelona kuwa za ta je gidan Valladolid a gasar La Liga ranar Asabar 3 ga watan Mayu, sannan ranar Talata ta ziyarci Inter a wasa na biyu a Champions League.

উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa

কীওয়ার্ড: Wasani daf da karshe a Champions League Barcelona ta

এছাড়াও পড়ুন:

An dawo da wutar lantarki a Sifaniya da Portugal

An dawo da wutar lantarki a safiyar Talatar nan a Sifaniya da Portugal bayan katsewar da aka samu ta sa’o’i wadda ita ce mafi muni da aka gani a Turai.

A jiya Litinin ce dai miliyoyin mutane suka auka cikin duhu bayan ɗaukewar wutar lantarkin a ƙasashen biyu wadda ke ci gaba da ɗiga ayar tambaya kan abin da ya haifar da ita.

Za a rataye wani soja saboda laifin kashe budurwarsa Boko Haram ta kashe masu zaman makoki 7 a Chibok

Kafofin watsa labarai sun ruwaito cewa ɗaukewar wutar lantarkin ta dakatar da zirga-zirgar jiragen sama da na ƙasa da katse hanyoyin sadarwa ta wayar hannu da kuma rufe na’urorin cire kuɗi na ATM a duk faɗin ƙasashen biyu.

Wata sanarwa da hukumar samar da wutar lantarki a Spain ta Red Electrica ta fitar, ta ce da misalin ƙarfe 7 na safiya agogon ƙasar, an samu nasarar dawo da sama da kashi 99 na wutar lantarki a ƙasar.

Haka nan ita ma takwararta ta Portugal ta ce tun cikin daren jiya Litinin, aka dawo da wutar lantarkin da dukkanin tashoshin wutar ƙasar guda 89.

Bayan ɗauke wutar da aka samu a Spain, jami’an ba da agajin gaggawa sun sanar da nasarar kuɓutar da mutane dubu 35 da suka maƙale a jiragen ƙasa na ƙarƙashin ƙasa.

Har yanzu dai hukumomi ba su bayyana dalilin da ya sa aka samu ɗaukewar wutar lantarkin ba, wanda shi ne karo na biyu da irin wannan mummunar katsewar wutar lantarki ta faru a Turai cikin watanni

 

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Nijeriya Za Ta Karɓi Bakuncin Gasar Karatun Alƙur’ani Mai Girma Ta Duniya
  • Lamine Yamal Ya Buga Wasa 100 A Barcelona
  • Lamine Yamal Ya Huga Wasa 100 A Barcelona
  • Najeriya za ta karɓi baƙuncin Gasar Karatun Alkur’ani ta Duniya a karon farko 
  • Gwamnatin Tarayya ta ayyana hutu gobe Alhamis
  • Yadda ta kaya a wasannin kusa da na ƙarshe na Gasar Zakarun Turai
  • Cinikayyar Hidima Ta Kasar Sin Ta Matukar Bunkasa A Rubu’in Farko Na Nana
  • An dawo da wutar lantarki a Sifaniya da Portugal
  • Arsenal Da PSG: Wa Zai Yi Nasara A Gasar Zakarun Turai A Yau?