Kasar Sin Ta Yi Kiran Kawar Da Makaman Nukiliya Bisa Tsarin Tsaro Na Bai Daya
Published: 1st, May 2025 GMT
Jakadan kasar Sin ya bayyana cewa, kasar tana kiran a samar da hanyar kawar da makaman nukiliya wacce a karkashinta ba za a iya raba tsaro na kashin kai da tsaro na bai daya ba, tare da tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya.
Babban darektan sashen kula da makamai na ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, Sun Xiaobo, ya shaida wa babban taron muhawara na 3 na kwamitin shirya taron koli na yarjejeniyar hana yaduwar makaman nukiliya (NPT) na shekarar 2026 cewa, kasar Sin tana nan a kan bakanta game da kin raba ‘yancin kiyaye tsaro da na sauke nauyin da ya rataya a wuyan kasashe na tsaro, da kafa shugabanci na adalci a kan hana yaduwar makaman nukiliya.
Sun ya yi nuni da cewa, Amurka ta yi imanin cewa, ita daidai ne a wurinta, idan ta nemi zama sawun giwa a kan sauran kasashe, da yin amfani da gwale-gwalen karin haraji da sa takunkumai, da kara matsin lamba, da kambama zalunci, da yin mummunar illa ga ka’idojin kasa da kasa, da tsarin duniya da aka tabbatar a karkashin Majalisar Dinkin Duniya, da sauran al’amura na kyakkyawan tsari da ake bi bisa dokokin kasa da kasa.
Da yake gargadi game da karuwar mamaye komai a karkashin bangare guda, da cin zarafi da siyasar nuna fin karfi kuwa, Sun ya ba da shawarar cewa, ya kamata kasashen duniya su hada kai tare da yin tsayin daka wajen nuna turjiya ga dabi’un da suka saba wa tsarin tarihi, da hana bil’adama komawa rayuwa irin ta namun daji inda masu karfi ke farautar masu rauni. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Gwamna Namadi Ya Bada Motocin Aiki Goma Ga Rundunar ‘Yan Sanda
Daga Usman Muhammad Zaria
Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya ta yi kira ga mazauna jihar Jigawa da su kasance masu bin doka da oda, tare da yin aiki kafada da kafada da rundunar ‘yan sanda domin tabbatar da tsaro da kwanciyar hankali a fadin jihar.
Kwamishinan ‘Yan Sanda na jihar Jigawa, CP Dahiru Muhammad, ne ya bayyana haka lokacin da ya karɓi sabbin motoci 10 kirar Toyota Hilux da Gwamna Umar Namadi ya bai wa rundunar a Dutse, babban birnin jihar.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar, SP Lawan Shiisu Adam, ya fitar, CP Dahiru Muhammad ya yaba da jajircewar Gwamna Umar Namadi wajen tallafa wa hukumomin tsaro domin sauke nauyin da ke kansu a jihar.
Ya bayyana cewa, wannan gudummawa ta nuna cikakken kudirin gwamnatin Gwamna Namadi na ƙara inganta harkokin tsaro da kuma tallafawa Rundunar ‘Yan Sanda ta Najeriya wajen aiwatar da aikinta na kare rayuka da dukiyoyin jama’a a fadin jihar.
Kwamishinan ya nuna cewa, waɗannan sabbin motoci 10 za su taimaka matuƙa wajen rage lokacin da ake ɗauka kafin amsa kiran gaggawa, tare da ƙara inganta aikin rundunar a fadin jihar.
Ya ƙara da cewa, za a yi amfani da motocin yadda ya kamata, tare da kula da su don tabbatar da ingantaccen tsaro.
CP Dahiru Muhammad ya kuma sake jaddada aniyar rundunar wajen ci gaba da tabbatar da zaman lafiya, doka da oda, tare da ƙarfafa haɗin gwiwa da sauran hukumomin tsaro da masu ruwa da tsaki.