Ma’aikatan jihar Ribas sun hallara a sakatariyar kungiyar kwadago ta kasa, NLC da ke Fatakwal domin bikin ranar ma’aikata ta 2025 a ranar Alhamis. Dama kungiyar ta NLC, tuni ta sanar da cewa, ba za ta gudanar da bikin murnar ranar ma’aikata ba kamar yadda aka saba yi a filin shakatawa na Isaac Boro, inda a al’adance kungiyoyin kwadago daban-daban ke gudanar da tattaki a filin domin murnar wannan rana ta 1 ga watan Mayu.

Gobara A Haramtacciyar Wurin Ajiye Man Fetur Ta Ci Rayukan Mutane 5 A Jihar Ribas Aikin Gina Tashar Jirgin Ƙasa A Kano Yana Ci Gaba Gadan-gadan A maimakon haka, ma’aikatan sun taru ne domin nuna goyon bayansu ga Gwamna Siminalayi Fubara da mataimakinsa da ‘yan majalisar dokokin jihar Ribas a sakatariyar kungiyar NLC ta jihar. In ba a manta ba, LEADERSHIP ta rahoto cewa, Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu ya dakatar da Gwamna Siminalayi Fubara da mataimakinsa da ‘yan majalisar dokokin jihar, inda ya mika jihar karkashin kulawar tsohon shugaban sojin Ruwa na Nijeriya. Dukkan kungiyoyin NLC a jihar, sun yi taro a sakatariyar da ke kan titin Igboukwu, D-Line, Fatakwal, inda suka bayyana rashin amincewarsu da abin da suka kira zagon kasa ga mulkin dimokradiyya a jihar Ribas. A halin da ake ciki, Gwamnan Jihar Ribas da aka dakatar, Sir Fubara ya yi kira da a ci gaba da kare hakkin ma’aikata a jihar. Fubara, ya yi wannan kiran ne a cikin sakon hadin kai da jinjinawa da ya bayar a Fatakwal, a daidai lokacin da al’ummar kasar ke bikin ranar ma’aikata ta bana.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: jihar Ribas

এছাড়াও পড়ুন:

Lakurawa Sun Hallaka Jami’in Kwastam A Jihar Kebbi

An garzaya da shi zuwa babban Asibitin Gwamnatin Tarayya da ke Birnin Kebbi, inda daga bisani likitoci suka tabbatar da rasuwarsa.

An yi jana’izarsa a babban masallacin Sarkin Gwandu, sannan aka binne shi a makabartar Dukku da ke kan hanyar Makera zuwa Kangiwa.

Jana’izar ta samu halartar jami’an kwas5tan, ‘yan uwa, abokai da sauran mu5sulmi daga sassa daban-daban na jihar.

Har yanzu al’ummar garin Filgila da kewaye na cikin tashin hankali da fargaba, kasancewar hare-haren Lakurawa na jefa su cikin zulumi.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Kuri’ar Jin Ra’ayin Jama’a Ta CGTN: Baje Kolin Sin Da ASEAN Ya Fadada Matsayar Bai Daya Ta Cudanyar Sassa Daban Daban
  • An Bude Dandalin Tattauna Batutuwan Tsaro Na Xiangshan Karo Na 12 A Beijing 
  • Tinubu ya janye dokar ta-ɓaci da ya sanya a Ribas
  • Yanzu-yanzu: Shugaba Tinubu Ya Ɗage Dokar Ta-ɓaci A Jihar Ribas
  • Lakurawa Sun Hallaka Jami’in Kwastam A Jihar Kebbi
  • Iran Ta Bukaci Musulmi Su Goyi Bayan Yunkurin Kasa da Ka Na Kauracewa Isra’ila
  • Kakakin Majalisar Jigawa Ya Tsallake Rijiya Da Baya, Tawagar Jami’an Tsaronsa Sun Ji Rauni A Wani Hatsari A Jihar 
  • Gwamnatin Neja Ta Musanta Rahoton Hana Da’awa A Jihar
  • Ƴan Bindiga Sun Sace Malamin Krista Na Ɗarikar Katolika A Kogi
  • Dole sai mun tantance wa’azi kafin a yi —Gwamnan Neja