Kungiyar Ansarullahi Ta Yemen Ta Jaddada Goyon Baynata Ga Kungiyar Hizbullahi Ta Kasar Lebanon
Published: 2nd, May 2025 GMT
Jagoran kungiyar Ansarullahi ta kasar Yemen ya jaddada cewa: Suna tsaye kafada da kafada da kungiyar Hizbullah ta Lebanon kan duk wani yunkuri na kokarin tada zaune tsaye daga ‘yan sahayoniyya
Shugaban kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen, Sayyed Abdulmalik Badr al-Din al-Houthi, ya yi gargadin yadda yunwa ke barazana ga Falasdinawa sama da miliyan biyu a zirin Gaza, wadanda ke fuskantar yunwa a idon dukkanin bil’adama.
A jawabin da ya gabatar na zagayowar ranar shelar Falasdinawa kan neman taimakon Falasdinawa dangane da hare-haren wuce gona da irin yahudawan sahayoniyya, Sayyid Al-Houthi ya yi bayani kan sabbin abubuwa da suka shafi wuce gona da iri kan Gaza da kuma al’amuran yanki da na kasa da kasa, inda ya bayyana irin girman bala’in jin kai da al’ummar Falasdinu ke fuskanta a karkashin gwamnatin Amurka da ke mara baya ga gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Falasdinawa 40 Sun Yi Shahada A Cikin Sa’oi 24 A Gaza
A yau Laraba sa jijjifin Safiya an sami shahidai 3 a Gaza da hakan ya kara yawan shahidai zuwa 40 a cikin sa’o’i 24.
Bugu da kari, baya ga shahidan da suke faduwa a kowace rana, ana fama da matsananciyar yunwa a cikin yankin, bayan karewar kayan abincin HKI ta sake komawa yaki kwanaki 44 da su ka gabata.
A cikin sansanin ‘yan hijira na “Nusairat” mutane 3 sun yi shahada da su ka hada da karamar yarinya sanadiyyar harin da sojojin na HKI su ka kai wa yankin.
A gabashin birnin Khan-Yunus ma dai wasu Falasdinawa sun yi shahada.
Daga ranar 7 ga watan Oktoba na 2023 zuwa yanzu adadin wadanda su ka yi shahada sun wuce 52,000,wadanda su ka jikkata kuma sun haura 100,000.