Gobara ta lalata shagunan kasuwar waya a Kwara
Published: 1st, May 2025 GMT
Wata gobara da ta tashi a yammacin ranar Laraba a wata shahararriyar kasuwar wayoyin salula da ke ‘Challenge Market’, a Ilorin babban birnin Jihar Kwara, ta yi mummunar ɓarna.
Gobarar ta tashi ne da misalin ƙarfe 9:06 na dare kuma ana kyautata zaton wutar lantarki ce ta haddasa ta.
Dalilin da ya sa aka samu fashewar abubuwa a barikin Maiduguri – Sojoji ’Yan fashin teku sun sace mata 4 a hanyar ruwa ta BayelsaKasuwar tana da shaguna sama da 120, rumfunan 80, da wasu wuraren kasuwancin wayar da yawa.
A wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar kashe gobara ta Jihar Kwara, Hassan Adekunle ya fitar a ranar Alhamis, ya ce gobarar ta fi shafar shagunan waya da wuraren gyara.
“Nan take jami’an kashe gobararmu suka taru suka isa wurin inda suka tarar da shaguna da dama sun ƙone da wuta,” in ji shi.
“Kasuwar ta ƙunshi shaguna sama da 120, rumfuna 80 da sauran wuraren kasuwanci masu yawa. Ta hanyar shiga tsakani cikin gaggawa, da ƙwararrun dabaru, jami’an sun yi nasarar daƙile yaɗuwar gobarar, tare da taƙaita tasirinta zuwa rumfuna 10 kawai.
“Wuraren da gobarar ya shafa dai sun haɗa da shagunan waya da kuma wuraren gyaran waya, binciken farko ya nuna cewa wutar lantarki ce ta tashi.
“ ’Yan kasuwa da masu ruwa da tsaki a kasuwar sun yabawa hukumar kashe gobara ta Jihar Kwara bisa saurin ɗaukar matakin da suka yi wajen ceto kasuwar daga gobarar da ta ɓarke.”
Daraktan hukumar kashe gobara ta jihar Falade Olumuyiwa ya jajantawa shugabannin kasuwar da ’yan kasuwar da gobarar ta shafa.
Olumuyiwa ya kuma yi addu’ar Allah Ya dawo masu da dukkan asarar da aka samu.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Kwara kashe gobara
এছাড়াও পড়ুন:
‘An Kashe Masu Zanga-zanga Akalla 500 a Tanzania’
Jami’an diflomasiyya a Tanzania sun ce akwai kwararan hujjoji da ke tabbatar da an kashe akalla mutum 500 a cikin kwana biyu da barkewar zanga-zangar kin amincewa da sakamakon zaben da aka gudanar a ranar Laraba.
Sai dai a wani bangaren kuma, alkalumman Yan’adawa sun zarta haka.
Wakiliyar BBC ta ce ministan harakokin wajen Tanzania Mahmoud Kombo Thabit ya musanta rahotannin, amma wani jagoran adawa John Kitoka ya ce ‘yansanda da wasu sojojin haya na kasashen waje ne suka aiwatar da kisan mutane cikin dare.
Majalisar Dinkin Dauniya ta yi kiran gudanar da bincike kan zargin amfani da karfin da ya wuce kima a kan masu zanga-zangar.
BBC