HausaTv:
2025-05-22@17:37:24 GMT

Amurka ta sake kai Hari a yankunan Saada da Hudaidah na Yemen

Published: 1st, May 2025 GMT

Jiragen yakin Amurka sun sake kai hare-hare da dama kan lardunan Saada da Hudaidah na kasar Yemen yau Alhamis.

Wata majiyar tsaro a Yemen ta kara da cewa, an kai wasu hare-hare uku a yankin Kataf da ke lardin Saada, yayin da wani kuma ya afkawa gundumar al-Houk da ke lardin Hudaidah a gabar tekun yammacin Yeman, lamarin da ya janyo hasarar kayayyaki na fararen hula.

Dama a cewar kafar yada labaran kasar Yemen Al-Masirah, jiragen yakin Amurka sun kai hari a gundumar al-Sayl da ke lardin al-Jawf a arewacin kasar Yemen ranar Laraba.

Tun a ranar 15 ga watan Maris da ya gabata ne, kawencen Amurka da Birtaniya ke kai hare-hare ta sama kan kasar Yamen, domin nuna goyon baya ga gwamnatin Isra’ila.

Kafin hakan a ranar Litinin, 28 ga watan Afrilu, Amurka ta kai wani mummunan hari ta sama a birnin Sanaa, inda ta kashe mutane akalla 12 tare da jikkata wasu hudu.

A cikin wata sanarwa da ma’aikatar lafiya ta kasar Yemen ta fitar ta ce an kashe ‘yan kasar Yemen 12 da suka hada da kananan yara, yayin da wasu hudu suka jikkata sakamakon harin da Amurka ta kai kan wasu gidajen zama a yankin Thaqban na birnin Sanaa.

A safiyar litinin jiragen yakin Amurka sun kai harin bam a daya daga cikin wuraren da ake tsare da bakin haure ‘yan Afirka da ke yankin Saada, inda suka kashe mutane 68 tare da jikkata 47.

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: kasar Yemen

এছাড়াও পড়ুন:

Kasar Sin Na Adawa Da Kai Wa Fararen Hula Da Kayayyakin More Rayuwa Hari A Sudan

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Sojojin Yemen Sun Kai Wa Filin Jirgin Saman “Ben Gorion” Hari Sau Biyu A Yau Alhamis
  • Yakin Gaza : Tarayyar Turai za ta sake nazari kan Yarjejeniyarta da Isra’ila
  • Za’a Gudanar Da Tattaunawa Zagaye Na 5 Tsakanin Amurka Da Iran A Ranar 23-Afrilu A Roma
  • Fransa Ta Kira Yi Kasashen Turai Da Sake Bitar Alakarsu Da “Isra’ila”
  • An kashe makiyaya 2 a wani hari a Filato
  • ‘Yan Gwagwarmayar Falasdinawa Sun Halaka Sojojin Sahayoniyya Tare Da Jikkata Wasu A Beit Lahiya
  • Hare-Haren Isra’ila Ya Hallaka Aƙalla Mutum 38 A Gaza Cikin Rabin Sa’a
  • ’Yan bindiga: Zamfara sun koma kwana a jeji
  • Yeman ta yi barazanar killace tashar jiragen ruwan Haifa ta Isra’ila
  • Kasar Sin Na Adawa Da Kai Wa Fararen Hula Da Kayayyakin More Rayuwa Hari A Sudan