2025-10-16@14:46:43 GMT
إجمالي نتائج البحث: 4262
«Zafin rana»:
Duk da yarjejeniyar tsagaita wuta da aka kulla tsakanin kungiyar Hamas da Isra’ila, akalla Falasɗinawa uku sun rasa rayukansu a ranar Alhamis sakamakon hare-haren Isra’ila a Gaza, in ji majiyoyin lafiya a yankin. Wata hukumar gwamnatin Isra’ila ta ce zai yi wuya ta buɗe iyakar Rafah da ke tsakanin Gaza da Masar don zirga-zirgar mutane....
Gwamnatin Jihar Kano ta ce nan ba da jimawa ba za a fara ƙera fanel da sauran kayayyakin samar da wutar lantarki daga hasken ranar a jihar. Hakan a cewar gwamnatin ya biyo bayan samun masu zuba jari a fannin na makamashi, bayan rattaba hannu kan yarjejeniya da kamfanoni biyu da suka shahara a fannin,...
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi a jawabin da ya gabatar a taron tsakiyar shekara ta ministocin harkokin wajen kungiyar yan ba ruwammu wato NAM a birnin Kampala babban birnin kasar Uganda a jiya Laraba, ya jadda bukatar hadin kai da goyon baya a tsakanin kasashen kungiyar, wajen fuskantar rashin mutunta dokokin kasa...
Ma’aikatar masana’antu da ma’adinai ta kasar Iran ta bayyana cewa na sami karin ci gaba a yawan karfen da kasar ke sayarwa ga kasashen waje a rabin farko na wannan shekara ta 2025 zuwa dalar Amurka billion $4. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa duk tare da takunkuman tattalin arzikin da...
Baba-Ahmed, ya bayyana cewa, abin da danginsa suka fuskanta a hannun masu garkuwa da mutane a bara ya tabbatar masa da cewa rashin tsaro a yanzu yana da nasaba da siyasa. Ya kuma danganta kisan jama’ar da aka yi wa mabiya Shi’a a Zariya a shekarar 2015 da wani shiri na gwamnati don murƙushe masu...
Tsohon Gwamnan Jihar Ekiti, Ayodele Fayose, ya ce bai dace a ɗora wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu, laifin rikicin da jam’iyyar PDP ke fama da shi ba. Ya bayyana haka ne yayin hira da gidan talabijin na Channels a ranar Laraba, inda ya ce shugabannin PDP ne suka haddasa matsalolinsu, ba Tinubu ko jam’iyyar APC...
Shugaban Majalisar Dabarun Kula da harkokin waje kuma mamba a Majalisar fayyace manufofin kasar Iran ya bayyana cewa: Iran a shirye take ta tattauna amma ta kin juya akalarta Shugaban majalisar dabarun kula da harkokin waje kuma mamba a majalisar fayyace manufofin Jamhuriyar Musulunci ta Iran Kamal Kharrazi, ya jaddada cewa: Iran a shirye take...
Ministan harkokin wajen kasar Iran da takwaransa na Tunisiya sun jaddada cewa: Warware matsalar Falasdinu na bukatar kawo karshen mamayar da ake yi Ministocin harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran da Tunisiya sun jaddada cewa: Warware matsalar Falastinu na bukatar kawo karshen mamaya da kuma tabbatar da hakkin al’ummar Falastinu na cin gashin kansu. Wannan...

Kasar Afirka Ta Kudu Ta Jaddada Aniyarta Ta Ci Gaba Da Shari’ar Neman Hukunta Isra’ila Kan Batun Gaza
Kasar Afirka ta Kudu tana ci gaba da shari’ar da ta shigar kan gwamnatin mamayar Isra’ila duk da tsagaita bude wuta da aka yi a Gaza Ma’aikatar huldar kasa da kasa da hadin gwiwa ta Afirka ta Kudu ta tabbatar da cewa: Tsagaita bude wuta a zirin Gaza ba zai kawar da laifukan da aka...
Hukumomi a Isra’ila sun ce gwamnatin ƙasar ta yanke shawarar taƙaita shigar da kayan agaji zuwa zirin Gaza, sannan za ta ɗan dakata ta buɗe bakin iyakar zirin daga Rafas. Isra’ila ta ce ta ɗauki wannan matakin ne saboda abin da ta kira jan ƙafa da a cewarta Hamas ke yi wajen mayar da sauran...
Ma’aikatar raya matasa ta jihar Kwara tare da hadin gwiwar Masu Ruwa da Tsaki don horar da matasa kan amfani da fasahar AI don ganin sun kasance masu amfani da dogaro da kai, da kuma samun fasaha. Da yake jawabi a lokacin da tawagar ta ziyarci ma’aikatar a Ilorin, kwamishinan ci gaban matasa na...
Hukumar kula da gidaje ta jihar Kano ta fara wani gagarumin aikin tsaftar muhalli kashi na biyu a birnin Kwankwasiyya, inda ta kara azama wajen gina tsaftataccen muhalli, lafiya da kuma dorewar muhalli a birane. Da yake jawabi yayin aikin, mukaddashin Manajan Daraktan Kamfanin, Engr. Isyaku Umar Kwa, ya bayyana cewa kashi na biyu...
Kakakin Majalisar Nasarawa ya yi Allah-wadai da harin da aka kai wa al’ummar Nindama, in ji Govt. ya dauki matakan da suka dace. Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Nasarawa Dr. Danladi Jatau ya jajantawa al’umma da iyalan harin da wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba suka yi a kauyen Nindama...
Babbar Kotun Jihar Kano ta yanke wa wani kocin ƙungiyar ƙwallon ƙafa hukuncin daurin shekaru takwas ba tare da zaɓin tara ba, kan laifin luwadi da ɗan wasan kulob dinsa mai karancin shekaru. Kotun dai wacce ke ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Musa Dahuru Muhammad a ranar Laraba ta sami kocin mai suna Hayatu Muhammad da...
A yayin shari’ar, wanda ake tuhumar ya musanta zargin, sai dai kotun ta ce masu gabatar da kara sun gabatar da shaida wadda ta gamsar da ita ba tare da wata shakka ba. Mai shari’a Dahiru ya ce laifin ya ci karo da sashe na 284 na kundin laifuffuka, wanda ya haramta yin jima’i...
Majalisar Dattawa za ta tantance Farfesa Joash Ojo Amupitan (SAN) a ranar Alhamis, a matsayin sabon shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC). Daraktan Yaɗa Labarai na Majalisar Tarayya, Bullah Audu Bi-Allah ne, ya tabbatar da hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba. Ba za mu yi sulhu da ’yan...
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abass Araqchi ya bayyana yadda wasu kasashen turai 3 suka yi amfani da yarjejeniyar JCPOA da kuma kwamitin sulhu na majalisar dinkin duniya wajen mayar da kudurin kwamitin da aka soke shi a baya kan kasar iran, wanda ya fuskanci adawa daga kasashe da dama ciki har da mambobin biyu...
Ministan kula da ayyukan soji na HKI Katz ya bayyana cewa dakarun sojin Isra’ila za su koma da kai hare-hare a yankin Gaza, bayan ta kammala karbar dukkan mutanen ta da kungiyar Hamas ta kama, don nuna rashin amincewa da sabuwar yarjejeniyar dakatar da bude wuta da aka cimma tsakanin Hamas da kuma gwamnatin tel...
Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa (NBS), ta bayyana cewa hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya, ta sauka zuwa kashi 18.02 a watan Satumba, 2025, idan aka kwatanta da kashi 20.12 da aka samu a watan Agusta. A cewar rahoton hukumar, hauhawar farashin kayayyaki gaba ɗaya a watan Satumba ta kasance kashi 0.72, yayin da farashin kayan abinci...
Babban hafsan sojojin kasar Iran Manjo Janar Amir Hatami ya bayyana cewa sojojin kasar Iran sun samar da sabbin hanyoyin fuskantar makiya wadanda ta daukosu daga abinda ya faru a yakin kwanaki 12 wanda HKI da Amurka duka dorawa kasar. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto Janar Khatami yana fadar haka a...
Kotun Babban Majistare da ke Yaba ta bayar da umarnin a tono gawarwakin mutane 10 da gobara ta kashe a ginin Afriland Towers da ke Legas a ranar 16 ga Satumba, 2025, domin a gudanar da bincike a kansu. Alkalin kotun, Mai shari’a Atinuke Adetunji ce ta bayar da umarnin a ranar Talata bayan ta...
Kotun Babban Majistare da ke Yaba ta bayar da umarnin a tono gawarwakin mutane 10 da gobara ta kashe a ginin Afriland Towers da ke Legas a ranar 16 ga Satumba, 2025, domin a gudanar da bincike a kansu. Alkalin kotun, Mai shari’a Atinuke Adetunji ce ta bayar da umarnin a ranar Talata bayan ta...
Kasar Iran ta yi Allah wadai da kalaman kin jinin Iran da Trump ya yi a majalisar dokokin Isra’ila ta Knesset Ma’aikatar harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta fitar da sanarwa inda ta yi Allah wadai da zarge-zarge marasa tushe da kuma da’awar rashin gaskiya da rashin kunya da shugaban kasar Amurka Donald Trump...

A Lokacin Yaki, Iran Ta Tarwatsa Wata Cibiyar Leken Asirin Yahudawan Sahayoniyya Da Ke Yankin Farar Hula
Iran ta kai hari a wani sansanin sojan Isra’ila na sirri da ke karkashin wata hasumiya a Tel Aviv Yankin Gray, wani dandali ne na bincike, ya bayyana samuwar wani maboyar sirri na sojan Isra’ila da ke karkashin wani hasumiya a Tel Aviv, wanda ake kyautata zaton yana cikin wadanda aka kaiwa hari da makami...
Shugaban Kasar Columbia Ya Soki Donald Trump Akan Bai Wa Isra’ila Makamai Shugaban na kasar Columbia Gustavo Petro ya ce, Bugun kirjin da shugaban kasar Amurka Donald Trump ya yi na bai wa “Isra’ila” makamai tare da cewa ta yi amfani da su da kyau, ba wani abu ne da ya cancanci a yi...
Babbar Kotun Jihar Kano a ranar Talata ta bayar da umarnin aikewa da Ogugua Christopher zuwa gidan gayarn hali bisa zarginsa da hannu a sata da kuma safarar yara daga jihar Kano zuwa kudancin Najeriya. Ana dai zargin mutumin ne da mallakar wani gidan marayu a jihar Delta ba bisa ka’ida ba, sannan yana amfani...

Ma’aikatar Kasuwancin Sin Ta Yi Kira Ga Amurka Da Ta Shiga Tattaunawar Cinikayya Da Sahihiyar Zuciya
Daga nan sai kakakin ya ce, “Ba zai yiwu bangaren Amurka ya nemi tattaunawa a bangare guda, alhali a daya hannun yana barazanar kaddamar da sabbin takunkumai kan kasar Sin ba. Wannan ba ita ce hanya mai dacewa ta gudanar da cudanya da Sin ba.” (Saminu Alhassan) ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin...
Sayyidi Aliyu ya shaida hakan ne yayin jawabin bankwana da wayar da kan ɗaliban da suka samu gurbin karatun zuwa ƙasar Algeria na shekarar 2025, da ya gudana a cibiyar Sheikh Dahiru da ke Bauchi a ranar Litinin 13 ga watan Oktoba. Ya ce an ɗauki tsawon lokaci ana wayar da kan ɗaliban na...

Sin Tana Adawa Da Matakan Kuntatawa Na Amurka Kan Bangarorin Kasar Da Suka Shafi Harkokin Teku Da Jigila Da Ginin Jiragen Ruwa
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Kowacce Mace Tauraruwa Ce A Kasar Sin October 14, 2025 Daga Birnin Sin Shawarwarin Sin Sun Bude Sabuwar Hanyar Bunkasa Ci Gaban Mata A Duniya October 14, 2025 Daga Birnin Sin Al’ummun Kasashe Daban-Daban Sun Yabawa Shawarwarin Sin Dake Taimakawa Wajen Dunkulewa Don Hanzarta Ci Gaban...
Ministan harkokin wajen kasar Iran ya caccaki Donald Trump kan manufofinsa a yammacin Asiya, yana mai cewa shugaban Amurka ba zai iya da’awar samar da zaman lafiya a yankin ba yayin da yake aiwatar da manufofin wuce gona da iri da kuma hada kai da “masu aikata laifukan yaki.” A cikin wani sako a shafinsa...
Rasha ta kai harin jirage kan ayarin kayan agajin Majalisar Dinkin Duniya a makwabciyarta kasar Ukraine da suka fi shekara biyu suna yaki. Hukumomin Ukraine sun dakarun soji da ke yankin kudancin Kherson da suka mamaye a Ukraine ne suka kai harin a ranar Talata, inda suka lalata motocin Shirin Abinci na Duniya, a yayin...
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya isa birnin Kampala babban birnin kasar Uganda don halattan taron ministocin harkokin wajen kasashen kungiyar yan ba ruwammu karo 19 . Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran za’a gudanar da taron ne tare da neman ‘shi’arin “zurfafa hadin kai da kuma rabon fahintar juna a duniya’....
Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta bayyana cewa jami’an tsaron JMI suna cikin cikken shiri na kare kasar daga makiya, a duk lokacinda ta sake farma kasar da yaki. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na JMI ya nakalto kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Ismael Baghaei yana fadar haka a jiya litinin a taron yan jaridu...
Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta yi tir da maganganun shugaban kasar Amurka Donal Trump a cikin majalisar dokokin HKI a jiya Litinin inda ya bayyana cewa HKI ta sami nasara a yakin da ta kaiwa JMI a cikin watan Yunin da ya gabata, sannan daga karshe ya ce akwai bukatar a cimma yarjeniya da...
Duban dubatan mutane sun gudanar zanga-zangar goyon bayan Falasdinawa da kuma yin tir da kokarin samar da huldar jakadanci da HKI a maida kome kamar ba abinda ya faru. Sun kuma bayyana tsagaita wutan da aka samar da Hamas tana tangal tangal saboda tun farko ba’a gina shi kan yadda zata dore ba. Kamfanin dillancin...
Allah Ya yi wa Shugaban hukumar Zavbe ta Jihar Yobe (SIEC) Dakta Mamman Mohammed rasuwa sakamakon gajeriyar jinya. Marigayi Dokta Mohammed, likita ne kuma ƙwararren ma’aikacin gwamnati. Ya rasu ne a Asibitin Koyarwa na Jihar Yobe da ke Damaturu a ranar Litinin. Za a yi Sallar Jana’izarsa a yau talata 14 ga Oktoba, 2025, a...
Tsohuwar mai bai wa Basshar Asad na Syria shawara, Busaina Sha’aban ta kore gaskiyar labarin da aka rika watsawa na cewa ta yi wata ganawar sirri da jami’an kasashen Iran, Iraki da Lebanon tare da Basshar Asad. Busaina Sha’aban ta kuma ce ba ta yi managa da tsohon shugaban kasar ta Syria Basshar Asad ba...
Mai bai wa shugaban kasar Iran shawarar akan harkokin mata da iyali Malama Zahra Beruz Azar ta gabatar da shawarar a kulla wata yarjejeniya ta tausayawa a tsakanin matan duniya domin samar da damar gina rayuwa ta jin kai da ‘yan’adamtaka mai dorewa. Malama Zahra Behruz Azar ta gabatar da wannan shawarar ne dai a...
Rahotanni sun bayyana cewa wani ƙazamin faɗa ya barke tsakanin wata ƙabilar Palasɗinawa masu ɗauke da makamai da ƙungiyar Hamas a yankin zirin Gaza bayan an kulla yarjejeniyar zaman lafiya da Isra’ila. A ranar Litinin da aka fara musayar fursunoni tsakanin Hamas da Isra’ila ne rahotanni suka ɓulla game da faɗan da ya ɓarke tsakanin...
Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Nijeriya (ASUU) ta mayar da martani kan barazanar gwamnatin tarayya ta “ba aiki, ba a biya”, tana mai cewa ba za ta bari a tsoratar da ita da irin wannan gargaɗi ba. Shugaban ASUU, Chris Piwuna, ya bayyana haka a wata tattaunawa da gidan talabijin na Channels a shirin Politics Today...
Ya ƙara da cewa hukumar ta ƙara himma wajen aikin al’umma (CSR), tana taimakawa hukumomi masu ruwa da tsaki da al’ummomi domin karfafa zaman lafiya da tattalin arziki. A cewar Issa-Onilu, wannan nasara da aka samu a watan Satumba na nuna cewa hukumar Customs ba wai kawai tana cigaba da gyara ba ce, har tana...
Shugaban kasar iran Mas’ud Pezeshkiyan ya bayyana a yau a wajen taron da yayi da gwamnoni jihohin kasar baki daya cewa jamhuriyar musulunci ta iran tana da karfin juriewa duk wata matsin lamba kuma ba zata taba risunawa duk wani nuna karfi ko cin zarafi ba. Yace kasa kamar iran mai makwabta 16 ba abu...
Rahotanni sun bayyana cewa an gano daruruwan gawawwaki a karkashin burabutsai a yankin gaza bayan sanar da dakatar da bude wuta tsakanin isra’ila da kuma kungiyar Hamas, adadai lokacin da tawagar agaji ke ci gaba da gano gawarwaki da suka makale a karkashin duwatsu bayan kwashen shekaru 2 Isra’ila na kisan kare dangi, Majiyar Asibiti...
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar iran Esma’il Baqahea yayi gargadin game da barazanar da ake fuskanta na bazuwar fadan da ake yi a kan iyaka tsakanin kasar Afganistan da kuma kasar Pakistan, a yankin, inda dukkan bangarorin biyu suke musayar wuta a wurare daban daban dake kusa da iyakokin kasashen. Yace babban abin da ke...
Zamu kawo muku cikakken bayani idan sun bayyana. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Rundunar Ƴansanda Ta Kama Gaggan Ƴan Fashi 9 A Kano October 13, 2025 Labarai Magance Bala’o’i: Gwamna Lawal Ya Jaddada Ƙudirin Gwamnatin Zamfara Na Ci Gaba Da Haɗin Gwiwa Da NEMA October 13, 2025 Labarai Ba Bu Dalilin Da...
Majalisar Shura ta Jihar Kano ta fara zama da Malam Lawan Shu’aibu Abubakar (Triumph) kan zargin da wasu kungiyoyi biyar ke masa zargin batanci ga Manzon Allah SallalLahu alaihi Wasallama. Wannan tattaunawa tana gudana ne a cikin sirri a Ofishin Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) kuma ya samu halarcin fitattun malaman Musulunci na Jihar...
A safiyar yau litinin ce majiyar gwamnatin kasar Iran ta bayyana cewa shugaban kasa Masoud Pezeshkiyan ko kuma ministan harkokin wajen kasar ba zasu halarci taron sanyawa yarjeniyar tsagaita wuta tsakanin HKI da Falasdinawa a birnin Sharm sheikh na kasar masar ba. Saboda ba sa son haduwa da shuwagabannin kasashen yamma azzalumai wadanda da makaman...
A safiyar Litinin ɗin nan ƙungiyar Hamas ta saki rukunin farko na ’yan ƙasar Isra’ila bakwai da ta yi garkuwa da su a Zirin Gaza. A ɗaya ɓangaren kuma Falsɗinawa sun yi cincirindo a yankin Gaɓar Yammacin Kogin Jordan domin tarbar ’yan uwansu kimanin 2,000 da Isra’ila za ta sako. Tuni jami’an kungiyar agaji ta...
An kammala kada ƙuri’a da yammacin Lahadi a zaɓen shugaban ƙasa na Kamaru, inda shugaban ƙasa mai shekaru 92, Paul Biya — wanda shi ne tsohon shugaban ƙasa mafi tsufa a duniya — yake neman wa’adi na takwas a mulki. Biya, wanda ya shafe shekaru 43 yana mulkin ƙasar, ya fafata da ’yan takara 11,...
Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana dalilin da ya sa Iran ba za ta halarci taron na Sharm el-Sheikh ba Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya bayyana dangane da rashin halartar jamhuriyar Musulunci ta Iran zuwa taron na Sharm el-Sheikh cewa, ba za su iya tunkarar wadanda suka kaddamar da hare-haren wuce gona...