Gaza: Witfkoff ya yi rangadi a wuraren da Amurka ta kafa domin tallafi
Published: 2nd, August 2025 GMT
Yayin da yakin kisan kare dangi na “Isra’ila” ya shiga cikin wata na 22 a Gaza, wani babban wakilin shugaban kasar Amurka Donald Trump, Steve Witkoff, ya zagaya wuraren raba abinci da Amurka ke da da’awar cewa ta kafa domin taiamakawa wajen ayyukan jin kai, duk da cewa sojojin Isra’ila na ci gaba da kai hare-hare na yau da kullun kan Falasdinawa da ke fama da yunwa babu kakkautawa.
Ziyarar tasa ta zo dai-dai da lokacin fitar da rahotannin hukumomin kasa da kasa da ke nuna irin mawuyacin halin da Israila ta saka al’ummar Gaza, ta hanyar kai hare-hare a kan cibiyoyin bayar da agaji.
A cewar ofishin hukumar kare hakkin bil adama na Majalisar Dinkin Duniya, akalla Falasdinawa 1,373 ne aka kashe yayin da suke neman abinci tun daga ranar 27 ga watan Mayu, ciki har da 859 a kusa da wuraren bada agaji na GHF da Amurka ta kafa, da kuma wasu 514 a kan hanyar ayarin motocin Majalisar Dinkin Duniya da kungiyoyi masu zaman kansu.
Duk da wannan, jakadan Amurka a “Isra’ila” Mike Huckabee, wanda ya raka Witkoff a wannan tafiya, ya yi ikirarin cewa sun yi Magana da rundunar sojin Ira’ila da kuma mutane a Gaza a kan cewa, ayyukan rabon abinci da sauran kayan agaji a sansanoni da Amurka ta kafa a Gaza yana tafiya kamar yadda ya kamata.
“Mafi yawan wadannan kashe-kashen sojojin Isra’ila ne suka aikata su,” in ji MDD, inda ta kara da cewa wadanda suka tsira da rayukansu sun bayyana wuraren da aka kai hare-haren da kuma yadda Isra’ila ta kona sansanonin bayar da agaji ga fararen hula tare da kashe mutanen da suke wuraren.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label Name* Email* Website Label Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka ‘Yan Sudan dama na komawa gida bayan gudun hijira na tsawon shekaru a Masar August 2, 2025 Iran Ta Ce Batun Neman Dakatar Da Tace Uranium Zai Rusa Duk Wata Jarjejeniya Da Ake Son Cimmawa August 1, 2025 Jamhuriyar Musulunci Ta Iran Ta Yi Watsi Da Duk Wani Zarge-Zargen Neman Bata Mata Suna August 1, 2025 Limamin Sallar Juma’a Ya Ce; Iran Zata Mayar Da Isra’ila Kufai Idan Ta Sake Kai Hari Kan Kasarta August 1, 2025 Kasar Slovenia Da Haramta Tura Makamai Zuwa Haramtacciyar Kasar Isra’ila August 1, 2025 Kasar Spain Ta Bayyana Abin Da Ke Faruwa A Gaza A Matsayin Abin Kunya Ga Bil’Adama August 1, 2025 Iran ta yi watsi da zargin gwamnatocin turai na yunkurin kashe wasu mutane a kasashensu August 1, 2025 Mali da Rasha sun tattauna kan hadin gwiwar makamashi August 1, 2025 Afirka ta Kudu na shirin daukar matakan kauce wa tasirin harajin Amurka August 1, 2025 Haaretz: Sojojin Isra’ila 7 ne suka kashe kansu a watan Yuli August 1, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Yawan Mutanen Da Suka Yi Shahada Sakamakon Kisan Kiyashin ‘Yan Sahayoniyya A Gaza Ya Kusaci 65,000
Adadin mutanen da suka yi shahada sakamakon kisan kiyashin da ‘yan sahayoniyya suke yi a Gaza ya doshi 65,000
Adadin mutanen da suka yi shahada sakamakon yakin da yahudawan sahayoniyya suka kakaba wa Falasdinawa a yankin Zirin Gaza ya karu zuwa shahidai 64,871 da kuma jikkatan wasu 164,610 tun daga ranar 7 ga watan Oktoban shekarar 2023.
Bisa kididdigar baya-bayan nan da ma’aikatar lafiya ta Falasdinu ta fitar a zirin Gaza a ranar Lahadin da ta gabata, mutane 12,321 ne suka yi shahada yayin da wasu 52,569 suka samu raunuka tun bayan da gwamnatin mamayar Isra’ila ta sake komawa yaki kan Falasdinawa a ranar 18 ga watan Maris.
A cikin sa’o’i 24 da suka gabata, Falasdinawa 68 ne suka yi shahada tare da jikkatan wasu 68 da aka isa da su zuwa asibitocin Gaza.
Haka nan wasu Falasdinawa 10 sun yi shahada wasu 18 kuma suka jikkata da aka kai su asibitoci, lamarin da ya kawo adadin wadanda hare-haren ta’addancin ya rutsa da su a cikin bala’in neman tallafin abinci suka haura zuwa shahidai 2,494 da kuma wasu fiye da 18,135 da suka samu raunuka.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Gwamnatin Sudan Ta Ce: Babu Sulhu Da ‘Yan Tawayen Kasar Na Kungiyar Rapid Support Forces September 15, 2025 Kasashen Larabawa da na Musulmi na taron gaggawa kan harin Isra’ila a Qatar September 15, 2025 Hamas ta bukaci kasashen musulmi da na Larabawa su dauki mataki mai tsari kan Isra’ila September 15, 2025 Rabin Sojojin Isra’ila da suka ji rauni a yakin Gaza na fama da ciwon damuwa September 15, 2025 Sudan ta soki takunkuman da Amurka ta kakaba mata September 15, 2025 Dakarun Sojin Yamen Sun Kai Hari Kan Filin Jirgin Saman Ramon Na Isra’ila. September 14, 2025 Isra’ila Za ta Gamu Da Mummunar Martani Idan Tayi Gigin Afkawa Iran September 14, 2025 Ministocin Harkokin Wajen Kasashen Larabawa Da Na Musulmi Sun Fara Taro A Qatar. September 14, 2025 Gwamnatin Najeriya Ta Sanar Da Sabon Sharadi Na Bude Asusun Banki September 14, 2025 An Zabi Issa Tchiroma A Matsayin Dan Takara Daya Tilo A Kamaru September 14, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci