2025-09-18@19:17:28 GMT
إجمالي نتائج البحث: 6311

«Karuwa»:

    shugaban kasar Venezuela Nicolas Maduro ya bayyana cewa, Aikewa da sojojin ruwan Amurka a yankin Caribbean itace barazana mafi girma ga al’ummomin yankin a cikin wannan karni. Da yake magana a wani taron manema labarai, Maduro ya ce an jibge jiragen ruwan sojan Amurka guda 8 dauke da makamai masu linzami 1,200 da kuma na...
    Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya ce shi da takwarorinsa na Rasha da China sun aike da wasika ga Majalisar Dinkin Duniya, inda suka yi watsi da matakin da Birtaniya da Faransa da Jamus suka dauka a baya-bayan nan na yunkurin maido da takunkumin kasa da kasa kan Iran a matsayin mataki marar ma’ana....
    Tsohon Ministan Shari’a Abubakar Malami ya tsallake rijiya da baya a garin Birnin Kebbi yayin da wasu matasa suka kai wa tawagarsa hari. Abubakar Malami da tawagarsa, wasu ’yan bangar siyasa sun tare su, a unguwar GRA, inda suka yi amfani da sanduna da addun da sanduna suka farfasa motocin Malami tare da jikkata mutanensa,...
    A yau Litinin shugaban kasar Zimbabwe Emmerson Mnangagwa, ya iso birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin domin halartar bikin cika shekaru 80 da cimma nasarar yakin kin mamayar dakarun Japan, da yakin kin tafarkin murdiyya na duniya. Shugaba Mnangagwa ya sha ziyartar kasar Sin, inda a shekarar da ta gabata ma ya zo birnin Beijing...
    Jami’an Hukumar Sibil Difens (NSCDC) sun cafke wani mutum mai shekaru 48, Ibrahim Haruna, tare da ɗansa mai shekaru 15, bisa zargin yi wa wata yarinya ’yar shekara 13 fyaɗe a unguwar Jekadafari da ke Jihar Gombe. Wakilinmu ya ruwaito cewa an gabatar da waɗanda ake zargin ne a hedikwatar hukumar a ranar Litinin. An...
    Ya bayyana cewa, matan sun fito ne daga jihohin Kano, Katsina, Borno, Jigawa, da Zamfara, inda aka yi musu alkawuran samun ingantattun ayyukan yi a kasar ta Saudiyya.   An kama daya daga cikin wadanda ake zargi da safarar matan mai suna Mohammed Saleh mai shekaru 45 da haihuwa.   Babale ya ce, ana ci...
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya jaddada cewa: Iran da gaske take yi wajen kare muradunta daga bukatun Turai Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Ismail Baqa’i ya yi hira da kamfanin dillancin labaran kasar China Xinhua, inda ya tattauna kan taron kolin kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai (SCO), da yarjejeniyar dogon lokaci da kasar...
    Adadin wadanda suka mutu a girgizar kasar Afghanistan ya haura 800, yayin da ake sa tsammanin karuwar wadanda suka jikkata Hukumomin kasar Afganistan sun sanar da cewa: Adadin mutanen da suka mutu sakamakon girgizar kasar da ta afku a gabashin Afghanistan ya haura 800, yayin da sama da 1,500 suka jikkata, adadin da ake sa...
    Babban magatakardar Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres, wanda ya shigo kasar Sin don halartar taron koli na kungiyar hadin-kai ta Shanghai wato SCO na bana, ya zanta da dan jaridan babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin wato CMG a birnin Tianjin, inda ya ce, Xi Jinping shugaban kasa ne mai sanin ya...
    Rundunar ’yan sandan Jihar Legas ta kama wani dattijo mai shekaru 60, Ajayi Femi, bisa zargin yi wa wata budurwa mai shekaru 24 fyaɗe. Mai magana da yawun rundunar, CSP Benjamin Hundeyin, ya tabbatar da faruwar lamarin a jiya Lahadi. An kashe mutum 5 an sace limamai da hakimi a Sakkwato Simon Ekpa: An ɗaure...
    Gwamna Mohammed Umaru Bago na Jihar Neja ya rushe majalisar kwamishinoninsa. Sakataren Yaɗa Labarai na gwamnan, Bologi Ibrahim, ya ce gwamnan ya sanar da rushe majalisar kwamishinoninsa ne a yayin taron Majalisar Zartarwa ta jihar a safiyar Litinin ɗin nan. Ya kuma yaba musu bisa gudunmawar da suka bayar wajen kawo ci-gaba mai ma’ana a...
    Mashawarcin Shugaban Ƙasa kan harkokin Tsaro, Nuhu Ribaɗu, ya musanta zargin da tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya yi cewa Gwamnatin Shugaba Tinubu tana biyan kuɗaɗen fansa ga ’yan bindiga don sako waɗanda suka sace. El-Rufai ya yi wannan zargi ne a wani shirin talabijin na Channels, inda ya ce matsalar tsaro a Arewacin...
    Gwamnan Neja, Mohammed Umaru Bago, ya sallami dukkan mambobin Majalisar Zartarwa ta Jihar. Gwamnan ya bayyana labari sallamar ta su ne a taron majalisar da aka gudanar a fadar gwamnati da ke Minna, babban birnin jihar, da safiyar yau Litinin 1 ga Satumbar 2025 Girgizar Ƙasa Ta Kashe Sama da Mutune 600 A Afghanistan Daje...
    ’Yan gudun hijira daga sama da kauyukka 10 a Ƙaramar Hukumar Shagari ta Jihar Sakkwato sun rufe hanyar Shagari zuwa Sakkwato domin nuna fushinsu ga gwamnati kan azabar da suke sha hannun ’yan bindiga a yankinsu. Mata da mazan sun buƙaci daukin gwamnati kan abin da ke addabar su, sun rufe babbar hanyar da ta...
    Ana jin tsaron daruruwan mutane ne suka rasa ransa sanadiyyar girgizan kasa mai karfin ma’aunin richter 6 da ta fadawa yankin tsaunuka na kasar Afganistan dake kan iyaka da kasar Pakisatan. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kamfanin dillancin labaran rauters na cewa an jirage masu saukar ungulu suna sauke wadanda suka...
    A safiyar yau litininn ce aka fara jan’izar shugaban gwamnatin kasar Lemen Ahmad Ghalib Arrahwi da ministocinsa da suka yi shahada a hareharen da HKI ta kai kansu a lokacinda suke taro a birnin San’a babban birnin kasar. Tashar talabijin ta al-amayadeen ta kasar Lebanon ta bayyana cewa an gudanar da taron janaizar ne a...
    Hukumomin Afghanistan sun bayyana cewa adadin waɗanda suka mutu a girgizar ƙasa da ta afku a gabashin ƙasar ya haura mutane 610, yayin da aka samu ƙarin mutane 12 da suka mutu a Nangarhar, abin da ya kai jimillar mutuwar zuwa 622. Ma’aikatar cikin gida ta ƙasar ta ce sama da mutum 1,500 ne suka...
    Kungiyar Liverpool ta cimma yarjejeniya da Newcastle domin ɗaukar ɗan wasan gaba na ƙasar Sweden, Alexander Isak, akan zunzurutun kuɗi fam miliyan 125, wanda zai sanya shi zama ɗan wasa mafi tsada a tarihin gasar Firimiyar Ingila. Rahotanni sun bayyana cewa Isak zai yi gwajin lafiya yau Litinin tare da zakarun Firimiya, kafin a kammala...
    Yanzu an fi wata biyu da Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da taraktoci 2,000 da sauran kayan aikin gona domin haɓaka harkar noma, amma manoma sun ce har yanzu ba a raba musu su ba, abin da ke iya jawo asarar daminar bana. Ganin cewa a halin daminar tana gab da ƙarewa, manoma suna ganin lokaci...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Aƙalla mutum 610 ne suka rasa rayukansu yayin da wasu sama da 1,300 suka jikkata sakamakon girgizar ƙasa mai ƙarfi da ta afku a ƙasar Afghanistan. Rahotanni daga hukumomi da kafafen watsa labarai na duniya sun ce ibtila’in ya auku ne a yankin gabashin ƙasar Afghanistan, kusa da iyakarta da Pakistan. Rahoton Hukumar Binciken Ƙasa...
    Ya kuma tuna da tsohon abokin ajinsu wanda ya kasance tsohon Sufeton ƴansanda, marigayi Solomon Arase, wanda ya rasu a ranar Lahadi a Abuja bayan gajeriyar rashin lafiya. El-Rufai ya bayyana shi a matsayin mutum nagari, yana mai cewa tsarin ƴansanda na yanzu ya sha bamban da lokacin da Arase ya jagoranta. Daga ƙarshe, ya...
    Ƙungiyar Musulunci ta Nasrul-Lahi-L-Fatih (NASFAT) ta yi kira ga malamai da mabiya addinin Islama a duniya da su guji yin kalaman ɓatanci ga sahabban Annabi Muhammad (SAW), tana mai cewa yin hakan zunubi ne mai girma kuma ya saɓa wa koyarwar addini. Ƙungiyar ta yi kiran ne bayan rahotannin da ke nuna cewa wasu malamai...
    Jagoran kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen Sayyed Abdul Malik al-Houthi ya yi kakkausar suka kan harin wuce gona da iri da Isra’ila ta kai a birnin San’a wanda ya kai ga shahadar firaministan kasar Yemen da wasu jami’an farar hula da dama. A cikin wani jawabi da ya yi ta gidan talabijin na jinjinawa shahidai,...
    ’Yar Sarkin Katsina, Alhaji Abdulmumin Kabir Usman, Khadijah, wadda aka fi sani da Andijo, ta rasu. Ta rasu a Abuja tana da shekara 35, kuma ta bar ’ya’ya uku. Trust Radio za ta fara watsa cikakkun shirye-shirye a ranar Litinin Gwamnatin Sakkwato za ta fara biyan masallatan Juma’a kuɗi duk wata An yi jana’izarta a...
    Gidan rediyon Trust Radio mallakin kamfanin Media Trust Group, zai fara watsa cikakkun shirye-shiryenta a ranar Litinin, 1 ga watan Satumba, 2025. Wannan na zuwa ne bayan tashar ta kammala gwajin watsa shirye-shiryenta tare da samun amincewar Hukumar Kula da Watsa Shirye-shirye na Ƙasa (NBC). Kilishiyar Waja ta tallafa wa matan gidan yari da kayayyaki...
      Shugaba Xi ya yi imanin cewa, kungiyar SCO za ta ba da karin gudunmawa wajen samun ci gaba, da kara karfafa hadin gwiwa tsakanin kasashe membobinta, da tara karfin kasashe masu tasowa, da kuma taimaka wa ci gaban wayewar kan dan Adam, a karkashin hadin gwiwa na dukkan bangarori.   Kafin liyafar maraba, Shugaba...
    Jagoran juyin juya halin Musulunci ya jaddada muhimmancin aiwatar da yarjejeniyar bisa manyan tsare-tsare tsakanin Iran da China A daidai lokacin da shugaban kasar Iran ya kai ziyarar aiki zuwa kasar China, asusun kula da shafukan sada zumunta na ofishin kula da tsare-tsare da wallafa ayyukan Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei...
    Mataimakin babban kwamandan “IRGC” ya bayyana cewa: Makiya sun kasa cimma wata manufa tasu a tsawon kwanaki 12 da suka yi suna yakar Iran Mataimakin babban kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran Birgediya Janar Ali Fadavi ya tabbatar da cewa: Makiya sun kasa cimma wata manufa tasu a tsawon kwanaki 12 da...
    Kenya ta tono gawarwakin mutane 32 a daidai lokacin da ake ci gaba da nuna bacin ransu kan mace-macen ‘yan darikar addini masu tsattsauran ra’ayi Hukumomin kasar Kenya sun tono gawarwaki 32 a makon da ya gabata a kudu maso gabashin kasar, wani sabon bala’i da ya sake haifar da sukar gwamnatin kasar, wadda a...
      A nata bangaren, darektar kula da yankin Asiya da Fasifik da Gabas ta Tsakiya a ma’aikatar kula da hadin kan Afirka da harkokin wajen kasar Senegal Cathy Diagne Thioye, ta bayyana dandalin FOCAC a matsayin abin koyi a bangaren hadin gwiwa tsakanin kasashe masu tasowa. Ta yi kira ga bangarorin biyu da su ci...
      Ya tabbatar da cewa, an kwashe dukkan fasinjoji 618 da ke cikin jirgin cikin koshin lafiya. 20 sun samu kananan raunuka, yayin da bakwai ke kwance a asibiti amma tuni an sallame su, kuma NRC ce ta dauki nauyin biyan kudaden kiwon lafiyarsu. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da...
      A cewar majiyar, kwale-kwalen zai iya daukar fasinjoji 16 ne kacal, amma a zagaye na Uku cunkoson matafiyar ya yi yawa inda wasu mata biyu suka tilasta wa kansu afkawa cikin jirgin inda suka zama fasinjoji zuwa 18, ana kyautata zaton cewa, wannan ne ya yi sanadin kifewar kwale-kwalen. Daga kanmu, magana ta...
    137- Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissoshi wadanda suka zo cikin alkur’ani mai girma, ko kuma cikin wasu littafan wadanda suka hada da littafin Dastane, Rastan na Aya. Shahid Murtada Muttahari, ko kuma cikin littafin Mathnawa na maulana...
    Mazauna sun lakaɗa wa wata mata duka sannan suka ƙone ta ƙurmus kan zargin yi wa fiyayyen halitta Annabi Muhammadu (SAW) ɓatanci a yankin Kasuwan-Garba da ke ƙaramar hukumar Mariga ta Jihar Neja. Shaidu sun ce, lamarin ya faru ne a ranar Asabar lokacin da wata muhawara ta taso a cikin shagon matar inda take...
    Hadakar ta wuce batun tattalin arziki kadai, domin a bangaren tsaro ma, Rasha ta yi amfani da lalacewar alaka tsakanin kasashen Mali da Burkina Faso da Nijar da kasashen yamma, inda ta samu kutsawa cikinsu.   Ganin yadda yankin ke fama da matsalolin tsaro, sai Rasha ta aika musu da sojojin haya na Wagner domin...
    Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Chelsea ta tabbatar da ɗaukar ɗan wasan gaban Manchester United, Alejandro Garnacho, kan kuɗin da ya kai kusan fam miliyan 85 (£85m). Rahotanni sun bayyana cewa ɗan wasan na ƙasar Argentina ya rattaba hannu kan kwantiragin zama a Stamford Bridge har zuwa shekarar 2032. Hamas ta tabbatar da mutuwar jagoranta a...
    Da ma can an yi ta ba da shawara cewa ya kamata Arsenal ta dauki danwasa mai buga gefen hagu kamar Gabriel Martinelli, amma ba ta ce komai ba har sai yanzu. Bayan da cinikin Eze ya fada, yanzu kuma kungiyar ta Arsenal ta sake mayar da hankalinta wajen sayan dan wasan baya daga kungiyar...
    Ƙungiyar Hamas ta tabbatar da mutuwar Mohammed Sinwar, wanda aka daɗe ana ɗauka a matsayin jagoranta a Gaza. Wannan tabbaci ta Hamas ta bayar na zuwa ne fiye da watanni uku bayan Isra’ila ta ce ta kashe shi a wani harin sama. Mutum 13 sun rasu yayin tsere wa ’yan bindiga a Zamfara  Xi na...
    Ko Mbeumo zai dawo wa United da karsashinta? Dan wasan dan kasar Kamaru Bryna Mbeumo ya zama abin tattaunawa kuma mafi tsada a ‘yanwasan Afirka lokacin da ya koma Manchester United kan fani miliyan 65 daga kungiyar kwallon kafa ta Brentford. Dan kwallon mai shekara 25 ya ci kwallo 20 a gasar da aka kammala...
    Shugaban ƙasar China, Xi Jinping, na karɓar baƙuncin taron ƙungiyar Shanghai Cooperation Organisation (SCO) a birnin Tianjin, inda shugabannin ƙasashe kusan 20 daga yankin Eurasia suke halarta. Taron, wanda zai gudana har zuwa Litinin, ana kallon sa a matsayin wani babban dandalin da ke ƙara tabbatar da matsayin China a tsakiyar harkokin siyasar ƙasashen Eurasia....
    Hakan yana faruwa ne saboda yawan hormones “progesterone” da yake taruwa a jikinta. A wannan gaban ana kiran yanayin da “luteal phase”. Shin wasu lokuta ne za ki tsammaci ganin farin ruwa a gabanki; Idan kin gani ba damuwa bane Yawanci mata suna iya samun bushewar gaba kamar na kwana 3 zuwa 4 kowane bayan...
    Ko za ki fadawa masu karatu dan takaitaccen tarihinki? An haife ni a garin Kano a Bichi LGA, na yi firamare a Bichi ‘Chiranci Primary School’. Amma ban cigaba ba da yake mu fulani ne, daga nan aka yi min aure. Bayan na fita daga gidan mijina, sai na fara koyan wasan dabe (Drama), daga...
    Ma’aikatar harkokin wajen kasar ta yi Allah-wadai da kakkausar murya kan kisan da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta yi wa  wasu daga cikin manyan jami’an kasar Yemen, tare da yin kira ga al’ummar duniya da su tinkari irin wadannan munanan ayyuka  na rashin bin doka da oda. A cikin wata sanarwa da ta fitar, ma’aikatar...
    Fadar shugaban kasar Yemen a Sana’a ta sanar da shahadar firayim minista Ahmed Ghaleb al-Rahwi tare da wasu ministocin kasar, sakamakon harin da Isra’ila ta kai a ranar Alhamis din da ta gabata. Fadar shugaban kasar a cikin wata sanarwa da ta fitar ta kara da cewa, wasu ministoci da dama sun samu raunuka sakamakon...
    Shugaban mayakan RSF a Sudan Mohammed Hamdan Dagalo ya yi rantsuwar shugabatar gwamnati mai kishintar gwamnatin kasar. Sanarwar ta ce Dagalo, wanda aka fi sani da Hemedti, wanda kuma ba kasafai ake ganinsa a kasar Sudan ba tun bayan barkewar rikici na tsawon watanni 28 tsakaninsa da sojojin kasar, an rantsar da shi ne a...
    Matsala ta farko na yi mata take da: 1. Sai Bango Ya Tsage….: Gaskiyar diyan Bawo, da yake cewa, ‘Sai bango Ya tsage, kadangare ke samun wurin shiga. Lallai babu yadda za a yi gwamnati da sauran manyan al’umma suna kallon harshen Hausa a matsayin wani harshe wanda nazartarsa koma baya ne ga al’umma kuma...
    Gwamnonin Jihohin Arewa maso Gabas, sun koka kan matsalolin da suka shafi ayyukan jin-ƙai da kuma gina muhimman ababen more rayuwa duk da ci gaban da aka samu a yaƙin da ta’addanci a yankin. Wannan bayani ya fito ne daga sanarwar ƙarshen taronsu karo na 12 da aka gudanar a Jalingo, Jihar Taraba. Ambaliya: NEMA...
    Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA), ta raba wa mutanen da ambaliyar ruwa ta shafa a Ƙaramar Hukumar Potiskum ta Jihar Yobe, kayan tallafi. Darakta Janar na hukumar, Zubaida Umar, ta amince da fara wannan tallafi a Potiskum, inda ta samu wakilcin Abdullahi Garba, ko’odinetan ofishin NEMA na Maiduguri. An kama direban mota...
    Gwamnatin kasar Denmark ta sanar da cewa: Tana goyon bayan dakatar da yarjejeniyar kasuwanci da haramtacciyar kasar Isra’ila Ministan harkokin wajen Denmark Lars Løkke Rasmussen ya fada a ranar Asabar cewa: Kasarsa tana goyon bayan dakatar da yarjejeniyar kasuwanci da haramtacciyar kasar Isra’ila da nufin kawo karshen yakin Gaza. Ya kara da cewa: Abin da...