An naɗa Remi Tinubu Sarauniyar Yaƙin Akko
Published: 3rd, October 2025 GMT
Lamidon Akko da ke jihar Gombe, Alhaji Umar Muhammad Atiku, ya nada Uwargidan Shugaban Najeriya Sanata Remi Tinubu, sarautar Sarauniyar Yaki a masarautar.
Basaraken dai ya karrama uwargidan shugaban ƙasar ce a ranar Alhamis a wani biki na musamman da ya gudana a fadarsa.
An gudanar da zangar-zangar goyon bayan Kwamishinan ’Yan Sanda a Kano Babu wanda na cewa zan janyewa takara a 2027 — AtikuA cewar basaraken, ya ba ta sarautar ce domin yabawa da gudummawar da take bayarwa wajen kare marasa ƙarfi tare da tallafawa mata da yara a fadin ƙasar nan
A yayin ziyarar kwanaki biyu da ta kai jihar Gombe, Remi Tinubu ta kuma ƙaddamar da shirin Renewed Hope Initiative Flow With Confidence, wani muhimmin shiri na tsaftar al’ada, wanda zai samar da kayan tsaftar jinin al’ada ga ‘yan mata a makarantu, domin rage yawan rasa darussa da suke yi a lokacin al’ada.
Bayan an nada ta a sarautar, Sanata Remi ta bayyana farin cikinta da godiya, tana mai cewa wannan karramawa abar girmamawa ce da kuma ƙarfafa gwiwa a gare ta.
Ta yi alkawarin ƙara yin himma wajen tallafa wa ‘ya‘ya mata musamman a fannonin ilimi da lafiya, tare da roƙon sarakunan gargajiya da su taimaka wajen yada shirye-shiryenta har zuwa yankunansu.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Sarauta
এছাড়াও পড়ুন:
Sanusi ne kaɗai halastaccen Sarki a Kano — Kwankwaso
Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya sake jaddada cewar Muhammadu Sanusi II ne, halastaccen Sarki a hukumance
Ya bayyana haka ne a ranar Asabar, a lokacin bikin yaye ɗalibai karo na huɗu a Jami’ar Skyline University of Nigeria (SUN) da ke Kano.
Babu Janar ɗin da ISWAP ta kama a Borno — Sojoji Sojoji sun kashe ’yan ta’adda, sun kama mutum 94“Muhammadu Sanusi II shi kaɗai ne Sarkin Kano a wajen mutane da gwamnatin jiha. Duk wani da aka naɗa daga wajen jihar ba shi da inganci a idon al’ummar Kano.”
A cewarsa, duk wanda wasu suka naɗa a matsayin Sarki ba shi da ƙima a idon al’ummar Kano da gwamnatin jihar.
Kwankwaso, wanda ya yi takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar NNPP a 2023, ya yaba wa jami’ar saboda samar da ingantaccen ilimi.
Ya shawarci matasa su dage wajen neman ilimi domin nan na gaba za su iya jagorantar ƙasar.
Yayin da yake magana kan rikicin masarauta a Kano, Kwankwaso ya jaddada cewa Muhammadu Sanusi II ne, Sarki halastacce.
Kwankwaso ya nuna damuwa kan hare-haren ’yan bindiga a KanoHaka kuma ya nuna damuwa game da ƙaruwa hare-haren ’yan bindiga daga Jihar Katsina da ke kai wa yankunan Tsanyawa, Shanono, Gwarzo da Karaye hare-hare.
Ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta gaggauta ɗaukar mataki domin magance barazanar.
Ya ce idan gwamnati ba za ta iya kare rayuka da dukiyoyi ba, to lallai sai ta sake nazari kan yadda ta ke jagoranci.
Ya ƙara da cewa matsalar tsaro da ta samo asali a Zamfara ta bazu zuwa Sakkwato, Kebbi, Kaduna, sannan yanzu tana barazanar tsallakowa zuwa Kano da Jigawa.
“Idan gwamnati ba za ta iya kare rayuka da dukiyoyi ’yan ƙasa ba, to lallai dole ta zauna ta sake tunani. Matsalar tsaro da ta fara a Zamfara ta bazu zuwa Sakkwato, Kebbi, Kaduna, sannan yanzu tana barazana ga Kano da Jigawa.”
Kwankwaso, ya nuna yadda ya kashe maƙudan kuɗaɗe don samar da tsaro a lokacin da ya yi gwamna, sannan ya roƙi gwamnati mai ci ta shugaba Bola Ahmed Tinubu da ta ƙara himma wajen kare ’yan Najeriya.
A nasa ɓangaren, Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II, wanda shi ne jagoran Jami’ar, ya shawarci waɗanda suka kammala karatu da su zama masu gaskiya.
Ya ce ilimi ba shi da amfani idan ba a yi amfani da shi wajen kawo canji ba.
Ya nuna farin cikinsa kan samun mata da suka kammala karatu, inda ya yi fatan samun mata a harkokin shugabanci.
Tun da farko, Mataimakin Shugaban Jami’ar, Farfesa Ajith Kumar V.V., ya bayyana cewa ɗalibai 24 daga cikin 180 sun samu sakamako mafi daraja.