Kasar Sin Ta Nuna Takaici Da Matakin Amurka Na Kin Amincewa Da Daftarin Kudurin Gaza
Published: 2nd, October 2025 GMT
Wakilin dindindin na kasar Sin a MDD Fu Cong ya bayyana a jiya Laraba cewa, kasar Sin tana matukar bayyana takaicinta da kuma nadama a kan matakin da kasar Amurka ta dauka a baya, kan daftarin kudirin kwamitin sulhun MDD da aka tsara da nufin magance matsalar jin kai a zirin Gaza.
A jawabin da ya yi kan amfani da hawan kujerar na ki a wajen muhawarar babban taron Majalisar Dinkin Duniya, Fu ya ce, kasashen duniya sun dade suna yin gagarumin kira na tsagaita bude wuta da dakatar da yakin da ake yi a zirin Gaza, wanda ya yi sanadin asarar rayukan fararen hula da haddasa masifar tabarbarewar jin kai, inda hakan ke dakushe lamiri da tausayin bil’adama da kuma dokokin kasa da kasa.
Wakilin ya ce, “Sau da yawa, kwamitin sulhu ya yi ta neman daukar matakai, amma Amurka tana tilasta hana hakan sau da dama,” yana mai cewa, “Idan ba domin kariyar da Amurka take bai wa Isra’ila ba, da ba a yi karan-tsaye ga kudurorin kwamitin sulhun ba da kuma keta hurumin dokokin kasa da kasa”. Ya bayyana hakan ne yayin da yake magana kan yadda Amurka ta yi amfani da hawan kujerar na ki a kan daftarin kudurin ranar 18 ga watan Satumba wanda zai bukaci Isra’ila ta dage dukkan takunkumin da ta sa na hana kai kayan agaji zuwa Gaza cikin gaggawa. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Alummar Kasar Ecodo Sun yi Watsi Da Batun Sake Dawo Da Sansanin Sojin Amurka A Kasar
Tahotanni sun nuna cewa alummar kasar Ecodo sun yi fatali da shawarar bada damar dawo da sansanin sojin Amurka a kasar a wani zaben raba gardama da aka gudanar a kan batun.
Dubban alummar kasar Ecodo ne suka hallar a gaban akwatunan zabe don bayyana ra’ayinsu na amincewa ko rashin amincewa da dawo da sansanin sojojin Amurka a kasar, ko a shekara ta 2008 ma sun yi watsi da kafa sansanin sojin kasashen waje saboda kare martabar kasar.
A zaben da aka gudanar ya nuna cewa kusan kaso 60 cikin dari sun ki amincewa da shirin shugaban kasar Daniel Noboa babban abokin shugaban Amurka Donald trump kuma mai goyon bayan gudanar da ayyukan sojojin Amurka a yankin karebiya da kuma kusa da kasar venuzuwela.
Sakamakon zabe ya dakatar da Amurka na kokarin komawa sansanin sojin sama na manta dake gabar tekun pacific wanda ya kasance wajen gudanar da ayyukan sojin na washington
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Sojojin HKi Sun Kashe Wasu Falasdinawa Guda 2 A Sansanin Yan Gudun Hijira November 17, 2025 Tawagar Wasan Wushu Ta Kasar Iran Ta Samu Lambobin Yabo 4 A Saudiya November 17, 2025 Shugaban Nukiliyar Iran Yace Amurka Da Israila Sun Shiga Sabon Mataki Mai Hadari November 17, 2025 Hamas Da Sauran Bangarorin Falasdinawa Sun yi Watsi Da Shirin Aikewa Da Dakarun Kasashen Waje A Yankin Gaza November 17, 2025 Nukiliya : Iran zata sake duba huldarta da IAEA idan aka dauki wani sabon mataki kanta November 17, 2025 Kwamitin tsaro zai kada kuri’a kan daftarin kudirin Trump kan Gaza November 17, 2025 Ansarullah Ta Yi Allah Wadai Da Sabunta Takunkumin MDD Kan Yemen November 17, 2025 Afirka ta Kudu na Binciken shigar wasu ‘yan gudun hijirar Falasdinu 153 cikin kasar November 17, 2025 Najeriya ba za ta buga kofin duniya ba karo na biyu a jere November 17, 2025 DRC: An Kulla Yarjejeniyar Zaman Lafiya A Tsakanin Gwamnati Da Kungiyar M23 November 16, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci