HausaTv:
2025-11-18@14:20:35 GMT

Colombia ta kori jami’an diflomasiyyar Isra’ila

Published: 2nd, October 2025 GMT

Kasar Colombia ta kori jami’an diflomasiyyar gwamnatin Isra’ila sakamakon harin da Tel Aviv ta kai kan wani jirgin ruwan agaji na kasa da kasa da ke daura da Gaza, yayin da ta bukaci daure shugaban Amurka a gidan yari saboda hadin kan gwamnatin kasar a aiwatar da kisan kare dangi na Isra’ila a zirin Gaza.

Shugaban kasar Gustavo Petro ya ba da umarnin korar dukkanin tawagar diflomasiyyar Isra’ila daga Bogota, bayan da sojojin Isra’ila suka tsare ‘yan fafatukar dake cikin jirgin ruwan na Sumud Flotilla ciki har da wasu ‘yan gwagwarmayar Colombia biyu.

Dama dai Bogota ta yanke huldar diflomasiyya da Tel Aviv a watan Mayun 2024, amma matakin na ranar alhamis ya nuna yadda dangantaka ke kara tsami tsakanin Bogota da Tel-Aviv sakamakon yakin da takeyi a Gaza,wanda ya lakume rayukan Falasdinawa sama da 66,100, galibinsu mata da yara.

Da yake magana da manema labarai, shugaban kasar Columbia, ya ce idan shugaban Amurka Donald Trump ya ci gaba da kasancewa da hannu a kisan kare dangi, kamar yadda yake a yau, bai cancanci komai ba sai gidan yari, kuma kada sojojinsa su yi masa biyayya.

Shugaban na Colombia ya kuma yi barazanar daukar matakin shari’a ta kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa (ICC) kan Washington da Tel Aviv.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka DRC : An yanke wa Joseph Kabila hukuncin kisa kan cin amanar kasa October 2, 2025 Isra’ila ta kashe Falasdinawa 44 a ranar Laraba October 2, 2025 Iran ta bukaci a kakaba wa Isra’ila takunkumi kan kisan kiyashin Gaza October 2, 2025 Mohajerani: Iran ba ta maraba da yaki amma ta shirya don kare kanta October 2, 2025 Sojojin Ruwan Isra’ila sun kai farmaki kan jiragen ruwa na Sumud Flotilla October 2, 2025 Rasha: Dawo Da Tsarin Takunkumai A Kan Iran Ya Saba Wa Dokar MDD October 2, 2025 Gaza: Adadin wadanda suka yi shahada sakamakon hare-haren Isra’ila ya kai 66,148 October 2, 2025 Kotun Afirka ta Kudu ta samu madugun adawa da laifin harba  bindiga a bainar jama’a a 2018 October 2, 2025 Kungiyar RSF Ta Shigar Da Kara A Kotun ICC Kan Kisan Isra’ila A Gaza. October 1, 2025 Kasar Pakistan Tayi Gwajin  Makami Mai Linzami Na Fatah 4 Cikin Nasara. October 1, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Congo ta tsawaita haramcin fataucin ma’adinai a gabashin kasar

Ma’aikatar ma’adinai a Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo ta sanar da tsawaita dokar hana fataucin ma’adinai na tsawon watanni shida daga wuraren hakar ma’adinai da dama a lardunan  Kivu ta arewa da ta kudu da ke fama da rikici.

Sabunta haramcin zai kara kawo tsaiko da cikas wajen samar da wasu ma’adanai a duniya, musamman ma’adaanai irin su  tin, tantalum, da tungsten, mahimman abubuwan da ake amfani da su wajen kera kayan lantarki, motoci, da wasu ayyuka na sararin samaniya.

Haramcin, wanda aka fara aiki da shi a watan Fabrairu, ya ci gaba da aiki na tsawon wannan lokaci, inda shaidun ke nuna cewa kayayyakin da ake amfani da su ba bisa ka’ida ba daga ma’adinan suna tallafawa kungiyoyin masu dauke da makamai a gabashin Congo, a cewar wani bayani mai kwanan wata 3 ga watan Nuwamba mai dauke da sa hannun ministan ma’adinai na kasar, Louis Watom Kampaba.

Bayanin ya kunshi shafuka  38 da ke nuni da cewa haramcin ya shafi abubuwa da dama daga ciki har da coltan, cassiterite, da wolframite,  tin, tantalum, da tungsten.

Har ila yau kungiyar ‘yan tawayen M23 da sauran kungiyoyi masu dauke da makamai sun kwace filaye da dama a gabashin Kongo mai arzikin ma’adinai a cewar Ministan.

Matakin da ma’aikatar ma’adinai ta dauka ya haramta fitar da kayayyaki daga wuraren hakar ma’adinan da ake magana a kai, kuma ta ce za su iya fuskantar bincike mai zaman kansa daga ma’aikatar ko hukumomin kasa da kasa, ciki har da Majalisar Dinkin Duniya da kungiyar hadin kan tattalin arziki da raya kasashen yankin gabashin nahiyar Afirka.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Rasha: An dakile wani yunkurin kisan gilla kan Sakataren Majalisar Tsaron kasa November 18, 2025 Aref: Iran Tana Da Kyakkyawar Alaka Da Mambobin Kungiyar Hadin Gwiwa Ta Shanghai {SCO} November 17, 2025 Na’ini: Jagora Ne Da Kansa Ya Jagoranci Lamurra A Lokacin Yakin Kwanaki 12 Da Aka Kaddamar Kan Iran November 17, 2025 Mahukuntan Gaza Sun Yi Gargadin Bullar Bala’in Jin Kai A Yankin Da Ba A Taba Ganin Irinsa Ba November 17, 2025 Sheikh Na’im: Gwamnatin Lebanon Zata Yi Babban Kuskure Matukar Tabi Hanyar Sassauci November 17, 2025 Rushewar Ramukan Hako Ma’adinai Ta Kashe Mutane 32 A Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango November 17, 2025 Alummar Kasar Ecodo Sun yi Watsi Da Batun Sake Dawo Da Sansanin Sojin Amurka A Kasar November 17, 2025 Sojojin HKi Sun Kashe Wasu Falasdinawa Guda 2 A Sansanin Yan Gudun Hijira November 17, 2025 Tawagar Wasan Wushu Ta Kasar Iran Ta Samu Lambobin Yabo 4 A Saudiya November 17, 2025 Shugaban Nukiliyar Iran Yace Amurka Da Israila Sun Shiga Sabon Mataki Mai Hadari November 17, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Afrika ta Kudu Ta yi Gargadi Game Da Duk Wani Yunkuri Na Fitar Da Falasdinawa Daga Yankin Gaza
  • Tsohon jami’an MDD Yayi Tir Da Amincewa Da Kudurin Amurka A Kwamitin Sulhu Kan Gaza
  • MDD ta amince da kudurin tura dakarun kasa da kasa zuwa Gaza
  • Congo ta tsawaita haramcin fataucin ma’adinai a gabashin kasar
  • Mahukuntan Gaza Sun Yi Gargadin Bullar Bala’in Jin Kai A Yankin Da Ba A Taba Ganin Irinsa Ba
  • Hamas Da Sauran Bangarorin Falasdinawa Sun yi Watsi Da Shirin Aikewa Da Dakarun Kasashen Waje A Yankin Gaza
  • Kwamitin tsaron MDD zai kada kuri’a kan daftarin kudirin Trump kan Gaza
  • Isra’ila Ta Kai Wa Sojojin MDD Hari A Kasar Lebanon
  • Lebanon za ta shigar da kara a kan Isra’ila a MDD game da gina Katanga a iyakarta
  •  An Bayyana Sunayen Kasashen Da Su Fi Sayarwa “Isra’ila” Man Fetur A Lokacin Yakin Gaza