Yawan Yaran Da Ba Sa Zuwa Makaranta Barazana Ce Ga Makomar Nijeriya – Obasanjo
Published: 2nd, October 2025 GMT
Ya ce bambancin Nijeriya na ƙabilu, addinai da al’adu bai kamata a ɗauka a matsayin matsala ba, illa ma ya zama ƙarfin ƙasar.
“Idan aka tafiyar da bambancin nan da kyakkyawan shugabanci, Nijeriya za ta samu girmamawa a duniya,” in ji shi.
Obasanjo ya jaddada cewa ilimi shi ne tushen ci gaba, ba tare da la’akari da ƙabilanci, addini ko al’ada ba.
Ya yaba wa Gwamnan Jihar Sakkwato Ahmed Aliyu, Sarkin Musulmi Sa’ad Abubakar, da kuma Bishop Matthew Kukah saboda jajircewa wajen haɗa kan jama’a da zuba jari a ilimi.
Bishop Kukah ya bayyana cewa cibiyar da mai bayar da tallafi Afe Babalola ya gina za ta bayar da horo kyauta ga kowa a fannin amfani da kwamfuta, ƙirƙirar manhajoji, da ilimin kimiyyar bayanai (data science).
Sarkin Musulmi kuma ya jinjina wa Obasanjo saboda kiransa na ci gaba da haɗin kan ƙasa, inda ya roƙi ‘yan Nijeriya su guji rarrabuwar kai don su fuskanci matsalar tsaro tare da bunƙasa ci gaban ƙasa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Ba da yawuna PDP ta kori Wike ba — Muftwang
Gwamna Caleb Muftwang na Jihar Filato, ya ce ba da yawunsa jam’iyyarsu ta PDP ta kori Ministan Abuja, Nyesom Wike ba.
Yayin da yake nisanta kansa daga matakin da PDP ta ɗauka na korar Wike daga jam’iyyar, ya yi gargaɗin cewa hakan ba zai haifar da ɗa mai ido ba.
Fintiri ya yi watsi da korar Wike daga PDP Tsohon Minista Kabiru Turaki ya zama sabon shugaban PDP na ƙasaA jiya Asabar ce jam’iyyar ta kori ministan, wanda ya daɗe yana rigima da shugabancin jam’iyyar, da sakatarenta na ƙasa Samuel Anyanwu, da tsohon Gwamnan Ekiti Ayo Fayose yayin babban taronta na ƙasa tana mai zargin su da yi mata zagon ƙasa.
Cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa ya fitar, Muftwang ya ce majalisar gwamnonin PDP da kwamatin zartarwa ba su tattauna batun ba kafin a bijiro da shi yayin taron.
Ya ƙara da cewa “korar jiga-jigan jam’iyyar a wannan lokaci mai muhimmanci ba shawara ce mai kyau ba wajen shawo kan rikicin da ya dabaibaye PDP.”
Kalaman Muftwang na zuwa ne jim kaɗan bayan Gwamnan Adamawa Ahmadu Fintiri shi ma ya ce bai goyi bayan korar Ministan Abujan da abokan siyasarsa ba.