Tinubu ya buƙaci ’yan Najeriya du daina yi wa ƙasar mummunan fata
Published: 2nd, October 2025 GMT
Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya roƙi ’yan Najeriya da su daina yin maganganu ɓatancin ga ƙasar.
Ya ce Najeriya ƙasa ce mai girma, mai cike da damar ci gaba.
NAJERIYA A YAU: Abin Da Dokar Kasa Ta Ce Kan Takarar Tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan ’Yan bindiga sun kashe mutum 4, sun sace 9 a NejaShugaban ya yi wannan jawabi ne a daren ranar Talata a Jihar Legas, lokacin da aka sake buɗe Cibiyar Al’adu ta Ƙasa (National Theatre) da aka gyara.
Ya ce dole ne ’yan ƙasa su yi imani da Najeriya kuma su haɗa kai domin gina ta.
“Ku daina yin magana mara kyau game da Najeriya. Mu mutane ne masu alfahari, jarumai, da jajirtattu. Mu gina wannan ƙasa tare, mu sake farfaɗo da ita,” in ji Tinubu.
Ya yaba da arziƙin al’adu da baiwar da Najeriya ke da ita, inda ya bayyana cewa wannan shi ne ɗaya daga cikin manyan ƙarfinta.
Haka kuma ya jinjina wa fitaccen marubuci, Farfesa Wole Soyinka, saboda gudunmawarsa ga adabi da ci gaban ƙasa.
Tinubu ya ce sake farfaɗo da cibiyar alama ce ta ƙarfi da juriyar Najeriya.
Ya ce za ta samar da ayyukan yi, bunƙasa fasaha, da kuma zama cibiyar al’adu a Afirka.
Shugaban ya kuma yaba wa Gwamnan Jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, da sauran waɗanda suka bayar da gudunmawa wajen kammala aikin.
Tinubu, ya nuna ƙwarin gwiwa kan tattalin arziƙin ƙasar: “Idan an tafiyar da shi yadda ya dace, arziƙi bunƙasa.
“Ku yi imani da kanku, ku bai wa mutane dama, ku ba su ƙwarin gwiwa. Najeriya ita ce giwar Afirka, kuma ba za ta durƙush3 a zamanina ba.”
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
PDP za ta sake farɗaɗowa idan shugabanninta suka cire girman kai — Anenih
Tsohuwar Shugabar Mata ta Jam’iyyar PDP, Iyom Josephine Anenih, ta ce jam’iyyar za ta sake yin ƙarfi idan shugabanninta suka cire girman kai suka mayar da hankali kan yi wa jama’a hidima.
Ta bayyana haka ne yayin babban taron PDP da aka gudanar a Ibadan a ranar Asabar.
PDP ta kori Wike, Fayose, Anyanwu da wasu Sanusi II ne kaɗai halastaccen Sarki a Kano — KwankwasoTa ce har yanzu ’yan Najeriya da dama suna sa ran jam’iyyar za ta sake yin ƙarfi domin yi musu jagoranci.
Anenih, ta yi gargaɗin cewa PDP na iya zama tarihi idan ba a gyara matsalolinta ba.
“Idan ba mu fuskanci matsalolinmu ba, PDP za ta zama tarihi, labarin yadda sakaci da girman kai suka lalata babbar jam’iyyar siyasa mafi girma a Afirka,” in ji ta.
Ta ƙara da cewa rikicin cikin gida, rashin ladabi, da cin amanar juna ne suka raunana jam’iyyar.
“Mambobinmu su ne ƙarfin PDP na gaskiya. Sun yi tsayin daka duk da matsalolin da ake fuskanta. Wannan babban taro dole ne ya girmama jajircewarsu,” ta ce.
Anenih, ta roƙi shugabannin jam’iyyar su kawo ƙarshen rigingimu da suka dabaibaye ta hanyar haɗa kai don sake gina jam’iyyar.
Ta ce Najeriya na buƙatar jam’iyyar adawa mai ƙarfi, wacce za ta kawo ƙarshen talauci da rashin tsaro da ake fama da su.