An tura wani mutum kurkuku saboda dabge da naman Dawisu
Published: 1st, October 2025 GMT
Wata kotu a Jihar Florida da ke ƙasar Amurka ta aike da wani mutum Craig Vogt mai shekaru 61 gidan waƙafi, bayan samunsa da laifin yanka tsuntsayen Dawisu guda biyu, sannan ya yi dabge da naman su.
Hukumomin Hudson, wani yanki da ke Florida, sun cafke mutumin ne bayan an samu rahoton abin da ya aikata, wanda ya ta da hankalin maƙwabta da ya shaida musu cewa ya yanka tsuntsayen kuma ya soya har ya ɗebi dabgen.
Rahotanni sun bayyana cewa, mutumin ya amince da laifinsa, yana mai cewa ya aikata hakan ne saboda ɓacin ran da yake ciki da maƙwabciyarsa wacce ta saba ciyar da tsuntsayen a kusa da gidansa.
Mutumin ya ce ya sha nanata mata cewa ba ya buƙatar ganin wani yana kula da tsuntsayen da mallakinsa ne, amma duk da haka maƙwabciyar na ci gaba da zuba musu abinci, lamarin da ya ce ya ƙara fusata shi.
Sai dai duk da an yanke masa hukunci, mutumin ya sha alwashin cewa zai kashe sauran tsuntsayen da ya ajiye a gidan, da zarar ya fito daga gidan waƙafi, idan har maƙwabtan ba su daina ciyar da su ba.
Kodayake kotun ta aike da shi gidan waƙafi, amma yanzu ba a bayyana matakin da za a dauka kan sauran tsuntsayen ba, musamman la’akari da barazanar da ya yi.
A Amurka, tsuntsayen irin Dawisu na daga cikin dabbobin da ake kula da su sosai, kuma a wasu jihohi, akwai dokoki da ke haramta kashe su ko cutar da su.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Ƴan Bindiga Sun Sace Mutane 14 A Wani Sabon Hari A Zamfara
A halin yanzu, masu sa ido na ƙauyen tare da wata tawagar tsaro ta haɗin gwuiwa daga tsohuwar tasha da Ruwan Doruwa sun fara aikin neman wadanda har yanzu ba a samu ba.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA