Aminiya:
2025-11-18@12:33:42 GMT

‘’Yan Najeriya ba su mance da badaƙalar da aka tafka a gwamnatin Jonathan ba’

Published: 30th, September 2025 GMT

Fadar Gwamnatin Nijeriya ta sanar da cewa duk da tana maraba da tsayawa takarar tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan a Zaɓen 2027, amma ya kwana da sanin cewa har yanzu ’yan ƙasar ba su mance da badaƙalar da aka tafka a lokacin gwamnatinsa ba.

Wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga ya fitar da yammacin ranar Litinin, ta ce ’yan Najeriya na sane da “rashin takaɓus” a mulkin Jonathan ɗin na shekarun baya.

Jama’ar gari sun kama ’yan bindiga 3 a Kastina An yi garkuwa da tsohon Shugaban SUBEB na Jihar Neja

Sanarwar da Fadar Shugaban Ƙasar ta fitar mai taken “Muna maraba da tsohon shugaban ƙasa zuwa takarar shugabancin ƙasa”, “amma ’yan Najeriya na sane da munanan ayyukansa lokacin yana mulki.”

Fadar shugaban ƙasar ta kuma bayyana yunƙurin jam’iyyar PDP na tsayar da Jonathan takara, a matsayin “raguwar dabara” sakamakon rawar da ya taka wajen ruguza tattalin arziki Najeriya, a tsawon shekaru 16 da PDPn ta kwashe tana mulkin ƙasar.

Sanarwa ta ce matuƙar Jonathan ya yanke shawarar tsayawa takarar, zai fuskanci matsalolin kundin tsarin mulki da bai ba shi damar sake tsayawa takara ba, la’akari da cewa an taɓa rantsar da shi har sau biyu a matsayin shugaban ƙasa, a gefe guda kuma ga ƙalubalen jama’a.

Wannan dai na zuwa ne a matsayin martani ga kalaman da tsohon ministan yaɗa labarai kuma jigo a jam’iyyar PDP, Farfesa Jerry Gana, ya yi wanda ya nuna cewa Jonathan zai iya komawa kan mulki a ƙarƙashin inuwar PDP.

A baya-bayan nan ne Jerry Gana, ya bayyana cewa tshohon shugaban ƙasar wanda ya sha kaye a hannun marigayi Shugaba Muhammadu Buhari a 2015, shi ne ɗan takara ɗaya tilo da ka iya kayar da Tinubu a zaɓen da ke tafe na 2027.

Sai dai fadar shugaban ƙasar ta yi watsi da batun na Farfesa Gana, inda ta bayyana shi a matsayin mafarki irin na siyasa, har ma ta gaargaɗi Jonathan da ya ankare da makamantan waɗannan kalamai da ke fitowa daga bakin ’yan PDP ɗin da suka watsar da shi tsawon shekaru 12, kar su kai shi su baro.

Goodluck Jonathan ya mulki Najeriya a daidai lokacin da ƙungiyar Boko Haram ke kan ganiyarta wajen ƙaddamar hare-hare kan fararen hula.

A baya-bayan nan dai akwai ƙaruwar kiraye-kiraye tsakanin wasu ’yan jam’iyyar hamayya ta PDP kan tsohon shugaban ƙasar ya fito takara a Zaɓen 2027.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Zaɓen 2027 shugaban ƙasar

এছাড়াও পড়ুন:

Ba da yawuna PDP ta kori Wike ba — Muftwang

Gwamna Caleb Muftwang na Jihar Filato, ya ce ba da yawunsa jam’iyyarsu ta PDP ta kori Ministan Abuja, Nyesom Wike ba.

Yayin da yake nisanta kansa daga matakin da PDP ta ɗauka na korar Wike daga jam’iyyar, ya yi gargaɗin cewa hakan ba zai haifar da ɗa mai ido ba.

Fintiri ya yi watsi da korar Wike daga PDP Tsohon Minista Kabiru Turaki ya zama sabon shugaban PDP na ƙasa

A jiya Asabar ce jam’iyyar ta kori ministan, wanda ya daɗe yana rigima da shugabancin jam’iyyar, da sakatarenta na ƙasa Samuel Anyanwu, da tsohon Gwamnan Ekiti Ayo Fayose yayin babban taronta na ƙasa tana mai zargin su da yi mata zagon ƙasa.

Cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa ya fitar, Muftwang ya ce majalisar gwamnonin PDP da kwamatin zartarwa ba su tattauna batun ba kafin a bijiro da shi yayin taron.

Ya ƙara da cewa “korar jiga-jigan jam’iyyar a wannan lokaci mai muhimmanci ba shawara ce mai kyau ba wajen shawo kan rikicin da ya dabaibaye PDP.”

Kalaman Muftwang na zuwa ne jim kaɗan bayan Gwamnan Adamawa Ahmadu Fintiri shi ma ya ce bai goyi bayan korar Ministan Abujan da abokan siyasarsa ba.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Hauhawar farashi ya ƙara raguwa a Nijeriya — NBS
  • Tsohon Firaministan Japan Ya Soki Kalaman Takaichi Dangane Da Batun Yankin Taiwan
  • NAJERIYA A YAU: Matsayar Doka Kan Taron Da Jam’iyyar PDP Ta Gudanar
  • Ɗan Najeriya ya kashe mahaifinsa, ya yanki ƙannensa da wuƙa a Amurka
  • Tsaro: Na kan yi kuka duk lokacin da na ji an kashe wani — Akpabio
  • Gwamnatin Gombe ta bai wa alƙalai da Khadi-Khadi kyautar sabbin motoci 16
  • Ba da yawuna PDP ta kori Wike ba — Muftwang
  • Tsohon Minista Kabiru Turaki ya zama sabon shugaban PDP na ƙasa
  • AU ta sake nanata cewa “Babu kisan kare dangi a arewacin Najeriya
  • Sanusi II Kaɗai Muka Sani A Matsayin Halataccen Sarkin Kano – Kwankwaso