HausaTv:
2025-11-18@11:02:18 GMT

Iran: An zartar da hukuncin kisa a kan wani dan leken asirin Isra’ila

Published: 30th, September 2025 GMT

An zartar da hukuncin kisa a kan daya daga cikin manyan ma’aikatan leken asiri a Iran da ke aiki da hukumar leken asiri ta gwamnatin Isra’ila, Mossad, kamar yadda ma’aikatar shari’a ta Iran ta tabbatar.

An zartar da hukuncin ne a kan Bahman Choubi-Asl a ranar Litinin bayan samunsa da laifin haɗa  kai tare da hukumar  leƙen asiri ta  Isra’ila a fagen tattara bayanai.

Ya kasance kwararre kan harkokin bayanai wanda ya shigo cikin muhimman ayyukan sadarwa na kasar ta hanyar kasancewarsa a wani kamfani na ayyukan kimiyya da fasaha.

Saboda kwarewarsa ya kasance a matsayin manaja a cikin dukkanin ayyukan kamfanin kuma yana da damar samun mahimman bayanai na kasar.

A cewar rahotannin bangaren shari’a, jami’an Mossad sun fara gano Choubi-Asl a lokacin da yake halartar kwas na ƙwararru a wata ƙasa a yankin tekun Farisa. Wani jami’in Mossad, wanda ke aiki a karkashin sunan wani kamfani  mai suna “ESMI,” daga baya ya tuntube shi.

Da farko an umurci wanda ake tuhuma da ya tafi Armenia, ko da yake daga baya aka canza wurin ganawarsu zuwa Indiya tare da ba da umarnin ya kawo kwamfutar tafi-da-gidanka da yake gudanar da ayyukansa.

A yayin wannan tafiya, jami’an Mossad wadanda suke a matsayin shugabannin wani kamfani sun biya dukkan kudaden balaguron, sun ba da lamuni na kudi, kuma sun sanya shi cikin azuzuwan horar da fasaha don haɓaka kara kwarewa a fagen aikinsa.

Hakan ya biyo bayan wani gagarumin shirin horo na musamman na kwanaki 45 a Ireland, inda wani mai magana da harshen Farisanci ya yi masa bayani kan muhimman abubuwan more rayuwa na Iran da ayyukan adana bayanai.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Axios: Netanyahu ya nemi afuwar Qatar kan harin da Isra’ila ta kai a kan Doha September 30, 2025 Larijani: Iran a shirye take don tallafawa Lebanon da gwagwarmaya a kowane mataki September 30, 2025 Takunkumin makamai na Turai ya haifar da mummunar illa ga tattalin arzikin sojojin Isra’ila September 30, 2025 Kungiyar Yan Gudun Hijira Na Kasar Noway Tace Akwai Babbar Damuwa Game Shiru Kan Gaza September 29, 2025 Shugaban Iran: Yunkurin Durkusar Da Alummar Iran Bashi Da Maraba Da Mafarki. September 29, 2025 Kwamitin Tsaro A Majalisar Dokokin Iran Ta Gama Tsara Ficewar Kasar Daga NPT September 29, 2025 An Kashe Sojan HKI Guda A Harin Maida Martani A Yankin Yamma Da Kogin Jordan September 29, 2025 Shugaban Kasar Iran Ya Bayyana Cewa Bukatun Amurka Daga Iran Ba Mai Yuwa Ba Ne September 29, 2025 Shugaban Majalisar Dokokin Kasar Iran Yace SnapBack Baya Bisa Ka’ida September 29, 2025 Jami’an Tsaro A kasar Burtaniya Sun Tsare George Gallowy Da Matarsa Na Wani Lokaci September 29, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Rushewar Ramukan Hako Ma’adinai Ta Kashe Mutane 32 A Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango

Rushewar ramukan hako ma’adinai ta kashe ma’aikata 32 a kudancin Jamhuriyar Demokradiyyar Congo

Akalla ma’aikatan hakar ma’adinai 32 ne suka mutu a ranar Asabar sakamakon zaftarewar ƙasa a wani ma’adinan cobalt a kudancin Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo, yayin da ake ci gaba da neman waɗanda har yanzu ba a same su ba a yankin.

Zaftarewar ƙasa ta faru ne a wurin Kalandu da ke cikin ma’adinan Mulundu kusa da Kolwezi, wani wuri da kamfanin Bajiklem ke gudanar da shi a hukumance.

Ministan harkokin cikin gida na lardin, Rui Kawumba Mayondi, ya ce “masu hakar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba sun kai hari kan wurin duk da haramcin da aka sanya saboda ruwan sama mai ƙarfi da kuma haɗarin zaftarewar ƙasa,” ya ƙara da cewa “hawa da suka yi cikin gaggawa ya sa gadar da suka gina a kan wani rami da ambaliyar ruwa ta mamaye ta ruguje.”

Jami’in ya bayyana cewa zuwa yanzu ƙungiyoyin ceto sun gano gawawwaki 32 daga cikin tarkacen, kuma ana sa ran adadin waɗanda suka mutu zai ƙaru.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Alummar Kasar Ecodo Sun yi Watsi Da Batun Sake Dawo Da Sansanin Sojin Amurka A Kasar November 17, 2025 Sojojin HKi Sun Kashe Wasu Falasdinawa Guda 2 A Sansanin Yan Gudun Hijira November 17, 2025 Tawagar Wasan Wushu Ta Kasar Iran Ta Samu Lambobin Yabo 4 A Saudiya November 17, 2025 Shugaban Nukiliyar Iran Yace Amurka Da Israila Sun Shiga Sabon Mataki Mai Hadari November 17, 2025 Hamas Da Sauran Bangarorin Falasdinawa Sun yi Watsi Da Shirin Aikewa Da Dakarun Kasashen Waje A Yankin Gaza November 17, 2025 Nukiliya : Iran zata sake duba huldarta da IAEA idan aka dauki wani sabon mataki kanta November 17, 2025 Kwamitin tsaro zai kada kuri’a kan daftarin kudirin Trump kan Gaza November 17, 2025 Ansarullah Ta Yi Allah Wadai Da Sabunta Takunkumin MDD Kan Yemen November 17, 2025 Afirka ta Kudu na Binciken shigar wasu ‘yan gudun hijirar Falasdinu 153 cikin kasar November 17, 2025 Najeriya ba za ta buga kofin duniya ba karo na biyu a jere November 17, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Ministan tsaron Iran na Ziyara a UAE don karfafa dangantakar tsaro tsakanin kasashen yankin
  • Congo ta tsawaita haramcin fataucin ma’adinai a gabashin kasar
  • Na’ini: Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Da Kansa Ya Jagoranci Yaki Kwanaki 12 Da Aka Kaddamar Kan Iran
  • Rushewar Ramukan Hako Ma’adinai Ta Kashe Mutane 32 A Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango
  • An Yanke Wa Tsohuwar Shugabar Bangladesh Hukuncin Kisa
  • Nukiliya : Iran zata sake duba huldarta da IAEA idan aka dauki wani sabon mataki kanta
  • Isra’ila Ta Kai Wa Sojojin MDD Hari A Kasar Lebanon
  • IRGC ta kama wani jirgin ruwan dakon mai a gabar tekun kudancin Makran
  • Lebanon za ta shigar da kara a kan Isra’ila a MDD game da gina Katanga a iyakarta
  • Ma’ariv: Netanyahu Yana Tsoron Hukuncin  Da Kotu  Za Ta Yanke Akansa