Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp.

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Ɗan shekara 2 ya rasu bayan faɗawa rijiya a Kano

Wani yaro ɗan shekara biyu mai suna Danjuma Salman, ya rasu bayan ya faɗa cikin rijiya a Jihar Kano.

Lamarin ya faru ne a Ƙaramar Hukumar Gwale.

Gwamnatin tarayya ki amince damu a matakin ƙasa – Bijilanti Ma’aikacin jinya ya kashe marasa lafiya 10 saboda aiki ya masa yawa

Rahotanni sun nuna cewa yaron ya zame ne sannan ya faɗa cikin rijiyar wadda murfinta ya lalace.

Mai magana da yawun Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano, ACFO Saminu Yusif Abdullahi, ya bayyana cewa sun samu kiran gaggawa da misalin ƙarfe 10:05 na safe daga wani mai suna Saminu Dayyabu, wanda ya sanar da su cewa wani yaro ya faɗa cikin rijiyar.

“A lokacin da jami’anmu suka isa wajen, sun tarar da yaro ɗan shekara biyu, Danjuma Salman, wanda ya faɗa cikin wata rijiya da murfinta ya lalace,” in ji sanarwar.

Abdullahi, ya ce jami’an hukumar sun fito da yaron, amma daga bisani aka tabbatar da rasuwarsa.

An miƙa gawar yaron ga mahaifinsa, Salman Dayyabu, bayan an fito da shi daga rijiyar.

Daraktan Hukumar Kashe Gobara na jihar, Alhaji Sani Anas, ya miƙa ta’aziyyarsa ga iyayen yaron.

Ya kuma yi kira ga mazauna unguwanni da su riƙa rufe rijiyoyi da sauran wuraren ruwa yadda ya kamata domin guje wa irin wannan iftila’i.

Haka kuma ya shawarci iyaye da su riƙa kula da yaransu sosai, musamman a wuraren da ke da hatsari.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Tanzania: ‘Yan sanda sun kama wani babban jigon adawar siyasa
  • Kasashen Afirka Bakwai Da Sojojin Amurka Suka Shiga
  •  Ukraine: Fiye Da ‘Yan Afirka 1000 Ne Suke Taya Rasha Yaki Da Kasar Ukiraniya
  • Majalisa Ta Ƙaryata Karɓar Dala Miliyan 10 Don Daƙile Tantance Shugaban NERC
  • Tarayyar Afirka Ta Yi Kiran Da A Girmama ‘Yancin Kai Na Najeriya Da Rashin Tsoma Baki A Harkokin Gidanta
  • Gidauniyar Tunawa Da Sardauna Ta Jinjinawa Gwamna Namadi Bisa Ayyukan Cigaban Jihar Jigawa
  • Limamin Juma’ar Tehran: Tsayin Dakan ‘Yan Gwagwarmaya Daga Koyi Ne Da Alkur’ani Mai Girma
  • Ɗan shekara 2 ya rasu bayan faɗawa rijiya a Kano
  • Za Mu Ƙara Ƙaimi Wajen Kai Wa ‘Yan Bindiga Hare-Hare Ta Sama – Hafsan Sojin Sama
  • Putin : zamu dauki mataki idan Amurka ta koma gwajin makaman nukiliya