Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi kira da hada karfi da karfe wajen gina kyakkyawar kasar Sin, da kuma sa kasar ta kara zama kore shar ta hanyar dasa itatuwa.

Xi wanda kuma shi ne babban sakataren kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, kana shugaban kwamitin koli na sojan kasar, ya bayyana hakan ne yayin da yake halartar aikin sa kai na dashen itatuwa a nan birnin Beijing a yau Alhamis.

Yana mai cewa, a halin yanzu, yawan gandun daji na kasar Sin ya zarce kashi 25 bisa dari, wanda ya ba da gudummawar kusan kashi 25 cikin dari na sabon koren yanki na duniya. Kana yanayin muhalli yana ci gaba da ingantuwa, kuma mutane na ganin hakan a zahiri. A sa’i daya kuma, ya kamata a lura cewa, har yanzu akwai karancin gandun daji da ciyayi a kasar Sin, kuma ingancinsu da kyansu ba su wadatar ba. Ya kamata a magance matsalolin da ke kasa, kuma a yi kokarin kara kyautatawa kowace shekara. (Mohammed Yahaya)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Babu Wata Karamar Hukumar Dake Ƙarƙashin Ikon Ƴan Ta’adda A Filato -Gwamna Mutfwang

Gwamnan Jihar Filato, Barr. Caleb Mutfwang, ya bayyana cewa babu wata ƙaramar hukuma a cikin jihar da ƴan ta’adda ko ƴan bindiga ke da iko da ita. Ya bayyana hakan ne a yayin wata ganawa da ƴan jarida da aka gudanar a sabon gidan gwamnati da ke Little Rayfield, Jos, a ranar Talata.

Gwamna Mutfwang ya ce gwamnatinsa ta ƙara ƙaimi wajen yaƙi da matsalar tsaro, musamman ta hanyar farfaɗo da rundunar tsaron cikin gida ta jihar wato Operation Rainbow, domin tallafa wa sauran hukumomin tsaro wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

Ana Ci Gaba Da Alhinin Mutuwar Malam Adamu Fika Sojoji Sun Ƙi Karɓar Cin Hancin Miliyan 13 Daga Ƴan Ta’adda A Filato

Ya ƙara da cewa, gwamnatinsa ba za ta yi ƙasa a gwuiwa ba wajen ganin an dawo da zaman lafiya a sassan jihar da rikice-rikicen ƙabilanci ko na addini suka taɓa. Ya ce gwamnati na aiki tare da hukumomin tsaro da shugabannin gargajiya domin tabbatar da fahimtar juna da daidaiton al’umma.

Gwamnan ya sake jaddada buƙatar kafa ƴansandan jiha, yana mai cewa hakan zai taimaka wajen rage matsalolin tsaro a faɗin Nijeriya. Ya ce kafa ƴansandan jiha zai bai wa gwamnatocin jihohi damar yin tsari da ɗaukar matakan da suka dace da yanayin tsaron yankunansu.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Wasan Kwallon Mutum-Mutumi Ya Nuna Yadda Sin Ta Shirya Wa Karbar Bakuncin Wasanninsu Na Duniya
  •  Girgizar Kasa Mai Karfi Ta Kada Yankin Kamtashatka Na Kasar Rasha
  • Fiye Da Kamfanoni 30,000 Masu Zuba Jari Daga Waje Aka Kafa A Sin A Rabin Farkon Bana
  • Babu Wata Karamar Hukumar Da Ke Ƙarƙashin Ikon Ƴan Ta’adda A Filato -Gwamna Mutfwang
  • Babu Wata Karamar Hukumar Dake Ƙarƙashin Ikon Ƴan Ta’adda A Filato -Gwamna Mutfwang
  •  Kasar Holland Ta Hana MInistocin HKI Biyu Shiga Cikin Kasarta
  • An Gudanar Da Taron Dandalin Tattaunawar Neman Sabon Tunani Na Asali Na 2025
  • Sin: Ya Kamata A Warware Sabanin Tattalin Arziki Da Cinikayya Ta Hanyar Tattaunawa
  • Sin Za Ta Ba Da Tallafin Kula Da Yara A Fadin Kasar
  • Amurka Ta Dakatar Da Bai Wa ‘Yan Kasar Nijar Bisa Shiga Cikin Kasarta