Gwamnatin Kwara Ta Bullo Da Shirin Habbaka Kiwon Dabbobi Da Raya Karkara
Published: 4th, April 2025 GMT
Gwamnatin jihar Kwara ta kaddamar da wani shiri na sauya fasalin noma domin habbaka kiwon dabbobi da bunƙasa yankunan karkara a fadin jihar.
Jami’in shiri na musamman kan harkar noma wato Special Agro Industrial Processing Zone (SAPZ) a turance, Dr. Busari Isiaka ne ya bayyana hakan ga manema labarai.
Ya ce wannan shiri ne da aka samar ta hanyar haɗin gwiwa tsakanin gwamnatin jihar da Bankin Raya Musulunci (IsDB) na Saudiyya domin kafa ingantattun abubuwan more rayuwa ga masu zuba jari da manoma a fannin sarrafa nama da madara.
Dakta Isiaka, wanda ya jaddada muhimmancin wannan aiki, ya bayyana cewa wannan ne karon farko da wani gwamna mai ci ke jagorantar kwamitin da ke kula da irin wannan babban shiri.
Ya bayyana cewa aikin zai gudana na tsawon shekaru biyar, tare da haɗin gwiwar kuɗi daga gwamnatin jihar da Bankin Raya Musulunci (IsDB).
Dakta Isiaka ya nuna cewa jihar Kwara ta nuna jajircewarta ga shirin tun da wuri ta hanyar biyan kuɗin haɗin gwiwa cikin gaggawa, wanda hakan ya sa ta zama jihar ta farko da ta kuɗaɗen da aka wajabta mata.
Ya jaddada cewa manufar wannan shiri shi ne inganta kayayyakin more rayuwa na fannin noma, musamman a ɓangaren kiwon dabbobi, tare da mayar da hankali kan inganta rayuwar al’ummomin karkara.
ALI MUHAMMAD RABIU
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Kwara
এছাড়াও পড়ুন:
UNICEF Ya Ba Da Tallafin Kayayyakin Aiki Ga Cibiyoyin Lafiya A Kirikasamma
A wani yunkuri na inganta kula da mata masu juna biyu da sauran ayyukan kiwon lafiya a jihar Jigawa, Asusun Kula da Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF tare da hadin gwiwar Karamar Hukumar Kirikasamma sun mika kayayyakin aiki da wasu muhimman kayayyaki ga cibiyar kiwon lafiya ta farko a Kirikasamma.
Mai kula da cibiyar kiwon lafiya ta farko, Kabiru Musa, ya bayyana cewa kayayyakin sun haɗa da gadajen haihuwa, zannuwan gado, kayan aikin jinya, matashin kai da sauransu, kuma za a rarraba su zuwa wuraren kiwon lafiya a fadin karamar hukumar.
A cewarsa, kayan da UNICEF da karamar hukumar suka samar za su inganta yadda ake gudanar da ayyukan kiwon lafiya a yankin.
Yayin mika kayayyakin ga mai kula da cibiyar kiwon lafiya, shugaban karamar hukumar Kirikasamma, Alhaji Muhammad Maji Wakili Marma, ya bukaci ma’aikatan lafiya da su tabbatar da gaskiya da adalci a lokacin rabon kayan.
Haka kuma, ya yaba da kokarin Gwamna Umar Namadi da sauran abokan hulda wajen gyara cibiyoyin kiwon lafiya da gina gidajen Ungozoma a Kirikasamma da kuma fadin jihar domin inganta ayyukan kiwon lafiya.
Usman Muhammad Zaria