Cibiyar Yaƙi da Ta’addanci ta miƙa Janar Tsiga da wasu ga NSA
Published: 3rd, April 2025 GMT
Cibiyar yaƙi da ta’addanci ta ƙasa (NCTC) ta miƙa tsohon Darakta-Janar na masu yi wa ƙasa hidima (NYSC), Birgediya Janar Maharazu Tsiga (mai ritaya) ga mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro (NSA), Nuhu Ribadu.
Tsiga, wanda aka kuɓutar bayan ya kwashe kwanaki 56 a tsare, a ranar Laraba an miƙa shi ne tare da wani tsohon Ambasada da sauran waɗanda ’yan ta’addan suka yi garkuwa da su.
Aminiya ta ruwaito yadda aka yi garkuwa da tsohon shugaban Hukumar NYSC daga mahaifarsa a ƙaramar hukumar Bakori ta Jihar Katsina, a ranar 5 ga Fabrairu, 2025.
Da yake jawabi gabanin miƙa su a hukumance, Shugaban Cibiyar NCTC, Manjo-Janar Adamu Laka, ya bayyana cewa jami’an tsaro daga sojoji, jami’an DSS, ’yan sanda da sauran hukumomin sun yi aiki ba dare ba rana domin ganin an ceto su.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Maharazu Tsiga
এছাড়াও পড়ুন:
Uganda Ta Sanar Da Kawo Karshen Ebola Da Ta Barke A Kasar
Ma’aikatar kiwon lafiya ta kasar Uganda ta sanar da cewa, an kawo karshen Ebola da ta bulla a kasar bayan da aka dauki kwanaki 42 ba tare da an sami mutum daya wanda ya sake kamuwa da ita ba.
A wani bayani da ya fito daga hukumar kiwon lafiya ta duniya ( WHO), ta bayyana cewa, a lokacin bullar cutar an gabatar da mutane 14 masu dauke da ita, an tabbatar da 12 daga cikinsu, sai wasu biyu da ba a same ta a tare da su ba.”
Haka nan kuma hukumar lafiyar ta ce, an sami mutuwar mutane 4 daga cikin wadanda su ka kamu da cutar ta Ebola, wasu mutane 10 kuma sun warke.”
Watanni 9 da su ka gabata ne dai aka tabbatar da bullar cutar a birnin Kamfala bayan da wani mutum da yake dauke da ita ya rasu.
Dajukan da kasar ta Uganda take da su, suna a matsayin matattarar cutar ta Ebola ce, wacce a karon farko ta bulla a cikin kasar a 2000.
A yankin yammacin Afirka cutar Ebola ta kashe fiye da mutane 11,000 a tsakanin 2013 zuwa 2016.