Tinubu ya kaddamar da aikin sake gyaran titin Abuja zuwa Kano
Published: 14th, April 2025 GMT
Shugaban Kasa Bola Tinubu ya kaddamar da aikin sake gyaran babban titin Abuja-Kaduna-Zariya-Kano, wadda ke da matukar muhimmanci ga tattalin arzikin Arewacin Najeriya.
Da yake jawabi a taron kaddamarwar a Kagarko, Jihar Kaduna, Gwamna Uba Sani, ya bayyana yadda aka yi watsi da hanyar da kuma irin mummunan tasirin da hakan ya yi ga rayuka da ci-gaban tattalin arziki.
Gwamna Uba Sani, ya yaba wa Tinubu bisa farfado da aikin, yana mai nuni da muhimmancin hanyar a matsayinta na mafi yawan zirga-zirgar ababen hawa a Arewa.
Da yake ba da tabbacin kamma aikin a cikin watanni 14, Tinubu wanda Ministan Ayyuka, Sanata David Umahi, ya ce za a gina titin ne da kankare, kamar babbar hanyar Legas zuwa Kalaba.
An kama kwayoyin N300m da mutane 650 a Kano An sake kama wasu mafarauta ’yan Kano a Jihar Edo Badaƙalar Miyagun Ƙwayoyi: Kotun Amurka ta ba da umarnin fitar da bayanai kan binciken TinubuMinistan ya kara da cewa aikin zan dangana har zuwa filin jirgin sama na Kano, kuma za a sanya kyamarorin CCTV gaba daya a tsawon titin, wanda sabon dan kwangila ne zai aiwatar.
Ya ce, shugaban kasa ya amince da naira biliyan 252 don muhimman sassan aikin, inda aka riga aka biya kashi 30%, yanan mai yaba muhimmiyar rawar da Gwamna Uba Sani ya taka a aikin.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: aikin gyara
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnonin Arewa sun yi Allah-wadai da sace ɗalibai mata a Kebbi
Ƙungiyar Gwamnonin Arewa (NGF) ta bayyana matuƙar damuwa kan harin da aka kai Makarantar Sakandiren Mata da ke Maga a ƙaramar hukumar Danko/Wasagu ta Jihar Kebbi, wanda ya yi sanadin sace ɗalibai mata da dama tare da kashe jami’an makarantar.
Shugaban ƙungiyar, kuma Gwamnan Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya bayyana lamarin a matsayin abin takaici da rashin hankali, yana mai cewa ci gaba da kai hare-hare kan makarantun Arewa barazana ce ga zaman lafiya da makomar ilimi a yankin.
Barau FC ta doke Enugu Rangers a Firimiyar Najeriya Anthony Joshua zai yi dambe da tauraron YouTube Jake Paul a DisambaA madadin sauran gwamnonin Arewa, Gwamna Inuwa ya jajanta wa Gwamnatin Jihar Kebbi, iyalan waɗanda aka sace da kuma waɗanda suka rasa rayukansu, tare da tabbatar wa Gwamna Nasir Idris da cikakkiyar goyon bayan ƙungiyar.
A wata sanarwa da Babban Daraktan Yaɗa Labarai na Gwamnatin Jihar Gombe, Isma’ila Uba Misilli, ya fitar, ƙungiyar ta buƙaci a gaggauta haɗa kai tsakanin jami’an tsaro domin ceto ’yan matan da aka sace da kuma kamo waɗanda suka aikata laifin.
Gwamnonin Arewa sun jaddada aniyarsu ta yin aiki kafada da kafada da Gwamnatin Tarayya da hukumomin tsaro domin tabbatar da tsaron makarantun yankin.
Gwamna Inuwa ya yi addu’ar Allah Ya dawo da ’yan matan lafiya, tare da kira ga al’umma da su kasance masu sa ido da bayar da goyon baya ga jami’an tsaro.