Radio Nigeria Kaduna Hausa:
2025-04-18@21:55:39 GMT

Hajjin 2025: Shirye-shirye Sun Yi Nisa A Jihar Jigawa

Published: 13th, April 2025 GMT

Hajjin 2025: Shirye-shirye Sun Yi Nisa A Jihar Jigawa

Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Jigawa ta ce shirye-shirye sun yi nisa game da aikin Hajjin shekarar 2025 a jihar.

Daraktan Hukumar, Alhaji Ahmed Umar Labbo, ne ya bayyana hakan ga Radio Nigeria a hedikwatar hukumar da ke Dutse.

A cewarsa, zuwa yanzu hukumar ta mika sunayen maniyyata fiye da dubu ɗaya da suka kammala biyan kuɗin aikin Hajji daga jihar zuwa ga Hukumar Kula da Aikin Hajji ta Ƙasa (NAHCON).

Ya ce tuni aka fara shigar da waɗanda suka kammala biyan kuɗin cikin tsarin neman biza.

Labbo ya bayyana cewa hukumar ta biya Hukumar Hajji ta Ƙasa kuɗi naira biliyan takwas a madadin  alhazan jihar na shekarar 2025.

Alhaji Ahmed Umar Labbo ya ce ana gudanar da tarukan bita ga maniyyata a kullum, a kananan hukumomi 27 na jihar, ta hannun wasu malamai don ilmantar da su game da aikin hajjin.

Ya ƙara da cewa hukumar za ta raba jakunkuna da za su daukin nauyin  kilo 8 da unifom ga jami’an yankuna da cibiyoyi domin rabawa mahajjatan.

Shugaban hukumar ya ja hankalin maniyyatan da su riƙa halartar traon bita saboda muhimmancinsa.

Ya yaba wa Gwamna Umar Namadi bisa goyon baya da haɗin kai da yake ba hukumar domin samun nasarar gudanar da aikin hajji ba tare da wata tangarda ba.

Radio Nigeria ta ruwaito cewa Hukumar Hajji ta Ƙasa (NAHCON) ta ware kujeru sama da 1,800 ga jihar domin aikin hajjin bana.

Usman Muhammad Zaria

উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa

কীওয়ার্ড: Jigawa

এছাড়াও পড়ুন:

Gwamnatin Jigawa Za Ta Yi Garambawul A Fannin Kiwon Lafiya

Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya sake jaddada kudurin gwamnatinsa na yin garambawul a fannin kiwon lafiya ta hanyar sanya tubalin gina sabbin cibiyoyin lafiya guda uku, da suka hada da Cibiyar Gwaji ta zamani, da Cibiyar kula da lafiyar Zuciya, da cibiyar samar da iskar numfashi  (Cryo-Oxygen Plant) a Fanisau, da ke Dutse, babban birnin jihar.

Wadannan ayyuka, wadanda za su ci biliyoyin nairori, wani bangare ne na hangen nesan gwamnatin na mayar da Dutse cibiyar yawon bude ido kan kiwon lafiya a yankin.

A yayin bikin, Gwamna Namadi ya bayyana cewa wannan rana ta shiga kundin tarihi a ci gaban jihar.

Ya bayyana cewa an tsara wadannan cibiyoyin ne domin kara karfin jihar wajen samar da ingantaccen kula da lafiya da rage dogaro da wasu jihohi ko kasashen waje, domin neman lafiya.

 

Namadi ya bayyana wasu daga cikin nasarorin da gwamnatinsa ta samu da suka hada da shigar da  mutane masu bukata ta musamman sama da dubu 143 cikin shirin inshorar lafiyar al’umma, da kuma farfado da asibitocin matakin farko da na biyu.

Malam Namadi ya bayyana cewa kudin farko zai fito ne daga baitul malin jihar, amma a tsawon lokaci, ana shirin tafiyar da cibiyoyin a karkashin hadin gwiwa tsakanin gwamnati da masu zaman kansu (PPP).

Ya ce wannan tsari zai tabbatar da dorewa mai inganci, tare da kawar da bukatar tafiye-tafiye zuwa wasu jihohi domin yin gwaje gwaje kamar su MRI da ke nuna hoton jikin mutum baki daya da kuma cutar da ke damunsa da kuma yin gwajin cutar sankarar Mama wato mammography.

Malam Namadi ya ce masana’antar samar da iskar numfashi ta Cryo-Oxygen za ta rika samar da kashi 100 bisa 100 na iskar oxygen mai tsafta don asibitoci, da kuma na  nitrogen don amfani a masana’antar takin zamani a Najeriya.

Gwamnan ya kuma yi bayanin wasu ayyuka da ake yi a fannin lafiya da suka hada da asibitin kashi na Gumel, da asibitocin kwararru a Hadejia da Kazaure, da kuma fadada ayyukan wanke koda kyauta.

Ya bayyana cewa gwamnati ta amince da bayar da magani kyauta ga masu ciwon siga, da hawan jini, da masu cutar sikila.

Dangane da inganta ma’aikata, Gwamna Namadi ya sanar da daukar ma’aikatan lafiya sama da 920 a matakin farko, da ma’aikatan jinya 200, tare da na wucin gadi 1,000.

Ya bukaci ma’aikatan lafiya da su nuna kishi da sadaukarwa, inda ya gargadi cewa ba za  lamunci sakaci da aiki da rashin da’a ba.

Gwamnan ya kuma yaba wa manyan abokan cigaban jihar kamar su UNICEF, WHO, USAID, FCDO, da gidauniyar Bill & Melinda Gates, tare da shugabannin gargajiya da na addini bisa goyon bayan da suke ci gaba da bayarwa wajen wayar da kan jama’a a fannin lafiya a fadin Jihar Jigawa.

Usman Muhammad Zaria 

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gwamna Umar Namadi Ya Dauki Matakan Kai Jihar Jigawa Babban Matsayi
  • Gwamnatin Trayya Zata Zamantar da Kayayyakin Watsa Labaran ta
  • Hukumar NSCDC ta tura jami’an tsaro 415 domin aikin Easter a Zamfara.
  • Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Gombe Ta Bada Tabbacin Tsaro A Bukin Ista
  • Jagora: Iran a shirye take domin aiki kafada da kafada tare da  Saudiyya
  • An Fara Bada Horo Ga Masu Horas da Maniyatan Bana A Jigawa
  • An Fara Bada Horo Ga Masu Horas da Mabiyan Bana A Jigawa
  • Hukumar Alhazai ta Jigawa Ta Shirya Bitar Ga Malaman Bita na Kananan Hukumomi 27
  • Hukumar EFCC Ta Kama Mutane 40 da Ake Zargi da Damfarar Intanet
  • Gwamnatin Jigawa Za Ta Yi Garambawul A Fannin Kiwon Lafiya