Sojojin Yemen Sun Kai Hari Kan Filin Jirgin Saman Lod Da Ke Jaffa Da Makami Mai Linzami
Published: 30th, July 2025 GMT
Sojojin Yemen sun sanar da cewa sun kai hari kan filin jirgin saman Lod da makami mai linzami
Sojojin kasar Yemen sun sanar a yammacin jiya talata cewa sun aiwatar da wani matakin soji mai inganci a kan tashar jirgin saman Lod da ke yankin Jaffa da aka mamaye, ta hanyar amfani da makami mai linzami na “Palestine 2” mai karfin gaske, suna masu jaddada cewa aikin ya samu nasarar cimma manufofinsa.
A cikin wata sanarwa da suka fitar sun bayyana cewa: Harin makami mai linzamin ya dakatar da ayyukan tashar jirgin gaba daya tare da haifar da firgici, lamarin da ya sa miliyoyin mazauna garin neman mafaka a karkashin rami.
Sojojin Yemen sun tabbatar da cewa wannan farmakin na zuwa ne a matsayin mayar da martani ga laifukan da gwamnatin mamayar Isra’ila ke aikatawa kan al’ummar Falastinu da kuma kare mutanen da ke fama da yunwa a zirin Gaza. Sun kuma jaddada cewa, kasar Yemen za ta ci gaba da gudanar da ayyukanta har sai an dakatar da hari kan Gaza, sannan kuma a daina kai hare-haren wuce gona da iri kan Falasdinawa.
Har ila yau, sun jaddada goyon bayan al’ummar kasar Yemen ga al’ummar Falastinu da gwagwarmayarsu, bisa la’akari da abin da suke yi a matsayin ayyuka da wajibai na ɗabi’a da addini da ba za a yi watsi da su ba.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Faransa Ta Bayyana Wuce Gona Da Irin ‘Yan Sahayoniyya Kan Falasdinawa Da Ayyukan Ta’addanci July 30, 2025 Jagora: Iran Ta Bayyana Karfinta Da Jajircewarta A Yakin Kwanaki 12 Ga Duniya July 29, 2025 Mutum daya Yayi Shahada 4 Sun Ji Rauna Sanadiyar Hare-Haren HKI A Lebanon July 29, 2025 EU Tace Zata Dakatar Da HKI Daga Cibiyar Bincikenta Saboda Gaza July 29, 2025 Ma’aikatar Leken Asirin JMI Ta Ce Ta Gano Shirin Kashe Manyan Mutane 35 a kasar July 29, 2025 Najeriya: Likitoci a Lagas Sun Shiga Yajin Aiki July 29, 2025 Wani Dan Majalisar Iran Ya Yi Kira Ga A Yi Siyasar Kin Gabatar Da Bayanai A Tattaunawa Da Kasashen Turai July 29, 2025 Sojojin HKI Sun Ci Gaba Da Kashe Kawunansu July 29, 2025 Kasar Holland Ta Hana MInistocin HKI Biyu Shiga Cikin Kasarta July 29, 2025 Manjo Janar Musawi: Ko Kadan Ba Mu Yarda Da Amurka Ba July 29, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
M D Duniya Tayi Gargadi Game Da Gwajin Nukiliya Da Amurka Ta Sanar Za ta yi
Rahotanni sun bayyana cewa majalisar dinkin duniya ta yi gargadin game da barazanar hadarin gwajin makamanin nunkiliya bayan da shugaban Amurka Trump ya bada umarnin a fara gwajin makaman nukiliya, Tace wannan matakin barazana ne ga tsaro da zaman lafiyar duniya.
Farhan Haq mataimakin kakakin majalisar dinkin duniya ya shaidawa manema labarai a birnin New York cewa sakataren janar din majalisar Antunio Guteress ya jaddada cewa hatsarin da makamin nukiliyar yake da she a halin yanzu yana ishara game da muhimmancin rashin daukar mataki akanshi don kaucewa babbar matsalar da zai haifar
Har ila yau Guterres ya gaya wa duniya irin bala’in da gwajin da makamin nukiliyar ya jawo wanda aka yi na nukiliya 2000 a shekaru 80 da suka wuce, yace bai kamata a bari a sake irin wannan gwajin ba ta ko wane hali,
Kokarin da ake yi na shawo kan yaduwar makamai na kara ja baya sosai saboda takaddamar siyasa da ake yi, wanda hakan ke rage amincin dake tsakanin kasashen da suka mallaki makamin nukiliya, da kuma dakatar da tattaunawa kan dokar kwance dammarar makaman,
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Sudan Ta Yi Kira Ga Kwamitin Tsaro Da Ya Ayyana RSF A Matsayin Kungiyar ‘Yan Ta’adda October 31, 2025 Araqchi: Gwajin Makaman Nukiliya Na Amurka Babbar Barazana Ce Ga Duniya October 31, 2025 Masar da Eritrea Sun Tattauna Bukatar Tallafawa Kasar Sudan October 31, 2025 Shugaban Lebanon Ya Umarci Sojoji Da Su Fuskanci Kutsen Na Isra’ila A Kudancin Kasar October 31, 2025 Madagascar Ta Sanar da Kafa Sabuwar Gwamnati Tare da Manyan ‘Yan Adawa October 31, 2025 Iran ta yi fatali da kalamman IAEA Kan Shirin Nukiliyarta October 30, 2025 Trump Ya Umarci Ma’aikatar Yakin Amurka Ta koma gwajin makaman nukiliya October 30, 2025 Isra’ila ta amince da fadada matsugunai a Yammacin Kogin Jordan October 30, 2025 Gaza: hare-haren Isra’ila sun kashe mutane 100 Cikin Kwanaki Biyu October 30, 2025 Sudan : Kasashen duniya na tir da cin zarafi a El-Fasher October 30, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci