DAGA LARABA: Dalilan al’ummomi na rungumar gwaji kafin aure
Published: 30th, July 2025 GMT
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba
Wasu al’ummomi sun bayyana dalilan da suka sa suka karbi tsarin yin gwajin lafiyar ma’aurata kafin a daura musu aure.
A wasu lokutan, akan samu matsaloli sakamakon rashin gwajin jini kafin a hada mace da na miji aure. Matsalolin sun hada da yaduwar cututtuka, samun ‘ya’ya marasa lafiya da sauran wasu matsalolin.
Shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi nazari ne kan dalilan da suka sa wasu alummomin suka rungumi yin gwajin jini kafin aure.
Domin sauke shirin, latsa nan
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: gwajin jjini
এছাড়াও পড়ুন:
Majalisa ta ba NNPCL mako uku ya yi mata bayanin inda tirilyan 210 ta shiga
Kwamitin Majalisar Dattawa na bin Diddigi ya ba Kamfanin Mai na Kasa (NNPCL) wa’adin mako uku ya amsa tambayoyi kan rashin ba da ba’asi kan Naira tiriliyan 210 da ba a san inda suka shiga ba daga shekarar 2017 zuwa 2023.
An dai bayar da wa’adin ne ga shugaban kamfanin na kasa, Bayo Ojulari, wanda ya bayyana a gaban kwamitin ranar Talata, bayan ya bayar da hakuri kan rashin bayyanarsa yayin gayyatar da kwamitin ya yi masa a baya.
Yadda ’yan bindiga sun tarwatsa ƙauyuka sama da 10 a Katsina Gwamnatin Tinubu ta mayar da Arewa saniyar ware – ACFKwamitin, wanda ke karkashin jagorancin Ahmed Wadada Aliyu (Nasarawa), ya tsaya kai da fata cewa dole kamfanin ya bayyana inda kudaden suka shiga.
Ojulari dai ya ba kwamitin hakuri, inda ya ce yana bukatar karin lokaci kafin ya iya amsa tuhumar da aka yi masa har guda 19.
Ya kuma ce, “Da kadan na haura kwana 100 a matsayin shugaban wannan kamfanin. Ina bukatar karin lokaci kafin na iya zakulo bayanan da kuka bukata. Wannan kuma na zuwa ne a daidai lokacin da sauran tarin ayyuka ke jira na.
“Ni kaina ina bukatar fahimtar abubuwan da kaina kafin na iya bayar da amsa a kansu. Amma zan je na zauna da sauran ma’aikatana da suka dace mu tattauna domin bayar da abin da ake bukata,” in ji shugaban na NNPCL.
Kodayake mako hudu ya bukata, amma kwamitin ya ba shi mako uku ne domin ya gabatar da bayanan.
Da yake karin haske a kan kudaden, Sanata Wadada ya ce kudaden da ake magana a kan su rubi biyu ne, akwai Naira tiriliyan 103 da kuma Naira tiriliyan 107 da suke bukatar bayanan a kan su.
“Amma fa ba mu ce wadannan kudaden da ake magana a kan su sace su aka yi ko kuma sun bace ba. Abin da kwamitinmu kawai yake kokarin yi shi ne bincike domin gano yadda aka yi tusarrufi da su,” in ji Sanata Wadada.