Kasashen Iran Da Rasha Sun Tattauna Batun Hadin Gwiwar Kafofin Watsa Labarai A Tsakaninsu
Published: 30th, July 2025 GMT
Iran da Rasha sun tattauna kan inganta hadin gwiwar kafofin yada labarai da yaki da labaran karya
Jakadan kasar Iran a birnin Moscow Kazem Jalali ya gana da mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Rasha Maria Zakharova a jiya Talata inda suka yi musayar ra’ayi kan bunkasa hadin gwiwar kafofin yada labarai.
Bangarorin biyu sun tattauna batutuwan baya-bayan nan da suka hada da yiwuwar gudanar da harkokin yada labarai, da nazarin yiwuwar bunkasa hadin gwiwar kafofin watsa labaru, da hanyoyin yin tasiri a kafofin watsa labaru, da matakan hadin gwiwa don kara fahimtar ra’ayin jama’a a kasashen biyu.
Bangarorin biyu sun yi tsokaci kan yadda kafafen yada labarai ke yada jita-jita da nufin yin zagon kasa ga dangantakar kasashen Iran da Rasha tare da tattauna hanyoyin yaki da labaran karya da yada labarai marasa tushe ko madogara.
A farkon taron, jakadan Iran ya yi tsokaci kan karairayi da kafafen yada labaran yammacin duniya ke yadawa, musamman Axios, dangane da alakar da ke tsakanin kasashen biyu, ya kuma mika godiyarsa ga ma’aikatar harkokin wajen kasar Rasha kan wannan batu.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka MDD Zata Aiwatar Da Hanyar Warware Rikicin Falasdinawa Da Yahudawan Sahayoniyya July 30, 2025 Birtaniya Ta Yi Barazanar Amincewa Da Kasar Falasdinu A Watan Satumba Idan Yanayin Gaza Bai Canza Ba July 30, 2025 Sojojin Yemen Sun Kai Hari Kan Filin Jirgin Saman Lod Da Ke Jaffa Da Makami Mai Linzami July 30, 2025 Faransa Ta Bayyana Wuce Gona Da Irin ‘Yan Sahayoniyya Kan Falasdinawa Da Ayyukan Ta’addanci July 30, 2025 Jagora: Iran Ta Bayyana Karfinta Da Jajircewarta A Yakin Kwanaki 12 Ga Duniya July 29, 2025 Mutum daya Yayi Shahada 4 Sun Ji Rauna Sanadiyar Hare-Haren HKI A Lebanon July 29, 2025 EU Tace Zata Dakatar Da HKI Daga Cibiyar Bincikenta Saboda Gaza July 29, 2025 Ma’aikatar Leken Asirin JMI Ta Ce Ta Gano Shirin Kashe Manyan Mutane 35 a kasar July 29, 2025 Najeriya: Likitoci a Lagas Sun Shiga Yajin Aiki July 29, 2025 Wani Dan Majalisar Iran Ya Yi Kira Ga A Yi Siyasar Kin Gabatar Da Bayanai A Tattaunawa Da Kasashen Turai July 29, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: yada labarai
এছাড়াও পড়ুন:
Samia Suluhu Hassan ta lashe zaben shugaban kasa a Tanzaniya
Hukumar zaben kasar Tanzaniya ta bayyana shugabar kasa mai ci Samia Suluhu Hassan a matsayin wadda ta lashe zaben shugaban kasar.
Shugaban hukumar zaben ya ce Shugaba Samia ta yi nasara a zaben da kashi 98% na jimillar kuri’un da aka kada.
Bayanai sun ce manyan ‘yan takarar adawa ba su shiga ba, wasu kuma an tsare su ko kuma an hana su tsayawa takara, wanda hakan ya haifar da tashin hankali.
Jam’iyyar adawa ta kasar ta ce daruruwan mutane ne suka mutu sanadiyyar zanga-zangar da aka kwashe kwanaki ana yi tun bayan zaben na ranar Laraba.
Wani mai magana da yawun jam’iyyar adawa ta Chadema ya shaida wa AFP cewa kimanin mutane 700 ne suka mutu, a alkalumman da aka tattara daga asibitoci.
Gwamnatin Shugaba Samia ta musanta duk wani “yin amfani da karfi fiye da kima,” yayin da Ministan Harkokin Waje Mahmoud Thabit Kombo ya shaida wa Al Jazeera cewa babu “bayani” kan adadin wadanda suka mutu.
Hukumomin sun katse hanyar intanet, sun sanya dokar hana fita, kuma sun takaita ‘yan jarida, wanda hakan ya takaita samun bayanai.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Najeriya ta musanta ikirarin Trump, na cewa Kristoci na fuskantar babbar barazana a kasar November 1, 2025 Majalisar Dinkin Duniya ta damu da hare-haren Amurka a Caribbean da Pacific November 1, 2025 Israila Ta Kai Hari Kan Ofishin kungiyar UNICEF Dake Gaza A November 1, 2025 Amurka Na Shirin Kai Hari Kan Kasar Venzuwela A Kowanne Lokaci November 1, 2025 Iran Ta Sanya Da Ranar 30 Ga Watan Nuwamba A Matsayin Ranar Kasa Ta Tsibirai 3 October 31, 2025 Isra’ila Na Ci Gaba Keta Yarjejeniyar Dakatar Da Bude Wuta A Gaza October 31, 2025 An Tube Yarima Mai Jiran Gado Na Birtaniya Bayan Da Aka Tabbatar Da Laifinsa October 31, 2025 Kasashen Pakistan Da Afghanistan Sun Tsawaita Yarjejeniyar Dakatar Da Bude Wuta October 31, 2025 M D Duniya Tayi Gargadi Game Da Gwajin Nukiliya Da Amurka Ta Sanar Za ta yi October 31, 2025 Sudan Ta Yi Kira Ga Kwamitin Tsaro Da Ya Ayyana RSF A Matsayin Kungiyar ‘Yan Ta’adda October 31, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci