Aminiya:
2025-07-30@04:33:49 GMT

Bello Turji ya kashe manoma 11 a wani sabon hari a Sakkwato 

Published: 3rd, April 2025 GMT

Ƙasurgumin ɗan bindiga, Bello Turji, da mayaƙansa sun kai mummunan hari garin Lugu da ke Ƙaramar Hukumar Isa a Jihar Sakkwato, inda suka kashe manoma 11.

Rahotanni sun nuna cewa harin ya faru ne yayin da Turji ke dawowa daga wata ziyarar sallah da ya kai yankin.

Najeriya ta yi kuskuren barin Boko Haram ta yi ƙarfi — Muftwang NAJERIYA A YAU: Ƙalubalen Da Iyaye Ke Fuskanta Wajen Tarbiyyar ‘Ya’yansu

Wani mazaunin Isa, Basharu Altine Giyawa, ya ce, “Tun a ranar Asabar muka samu bayanai cewa Turji zai ziyarci Gatawa, kuma mun sanar da hukumomi.

“Duk da haka, shi da mutanensa sun bi ta ƙauyukanmu, sun yi bikin sallah, sannan suka kashe manoma 11 a hanyarsu ta komawa Fakai.”

Ɗan majalisar dokokin Jihar Sakkwato mai wakiltar yankin, Hon. Aminu Boza, ya tabbatar da samun rahoton harin.

Amma ya ce: “Turji bai ziyarci kowace unguwa a yankina domin yin sallah ba. Mun ɗauki matakin gaggawa bayan samun bayanai, wanda hakan ka iya zama dalilin da ya sa ya mayar da martani kan waɗannan manoman a Isa.”

Mazauna yankin sun bayyana damuwa kan yadda hare-haren ‘yan bindiga ke ci gaba da ƙaruwa, duk da ƙoƙarin jami’an tsaro.

Sun yi kira ga gwamnati da ta ƙara ƙaimi wajen magance matsalar domin kare rayuka da dukiyoyinsu.

Hukumomin tsaro har yanzu ba su fitar da wata sanarwa kan harin ba, amma majiyoyi sun bayyana cewa sojoji na bin sahun Turji domin daƙile ayyukansa a yankin.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Ɗan Bindiga hari Sakkwato

এছাড়াও পড়ুন:

Arewa za ta kayar da Tinubu a zaɓen 2027 —Babachir

Al’ummar Arewacin Najeriya na shirin kayar da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu a zaɓen 2027 saboda ƙuncin rayuwa da kuma tsare-tsaren gwamnatinsa da suka mayar da yankin saniyar ware.

Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Babachir David Lawal  ne ya bayyana haka, yana mai cewa gamayyar shugabanni da ’yan siyasar Arewa na haɗa ƙarfi da ƙarfe domin tsayar Da ɗan takara da nufin yaƙar gwamnatin Tinubu a zaɓen 2027.

Babachir David Lawal ya bayya cewa shugabannin siyasar Arewa na aiki tare da Kungiyar Kare Muradun Arewa (ACF) da Kungiyar Dattawan Arewa (NEF) domin cin ma wannan manufa, kuma “Babu yadda za a yi mutum ya ci zaɓe na tare da samun goyon bayan waɗannan ƙungiyoyin ba.”

Ya ƙara da cewa tsare-tsaren Tinubu ciki har da cire tallafin mai da tsadar rayuwa sun jefa ’yan Najeriya cikin matsanancin rayuwa, don haka shugabannin siyasar Arewa ke ƙoƙarin fito da ɗan takararsu a zaɓen da ke tafe.

Matsalar Lantarki: Ga tsada ga rashin wuta An gano gawar mutum 15 bayan hatsarin kwalekwale a Neja

Ya bayyana haka ne a yayin wata tattaunawa da shi aka yi a tashar Talabijin ta Trust TV, inda ya bayyana cewa.

A cewarsa, “Maimakon saukaka wa al’umma halin da suke ciki, sai wannan gwamnati ta ɓige da ƙirƙiro abubuwan da ke ƙara jefa ’yan Najeriya cikin tsanani. Saboda haka dole a tsayar da ita.”

Game da muƙaman da Tinubu ya yi nada ’yan Arewa a baya-bayan nan, wanda ake tunanin ya yi ne domin lallashin yankin, Babachir ya bayyana naɗe-naɗen a matsayin shafe-shafe.

Ya ce, “Ni ne na fata yaƙar takarar Musulmi da Musulmi a wancan lokacin. Yanzu kuma da na ga ya naɗa Kirista a matsayin Shugaban Jam’iyya, na shan Musulmi zai ƙara ɗauka a matsayin mataimakinsa.”

Ya yi zargin Tinubu ya yi naɗe-naɗen ne domin ya raba kan masu zaɓe, “Amma Musulmin da suka zaɓe shi ma ya yi watsi da su, ya kawo musu koma baya, ya mayar da su saniyar ware.”

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gwamnatin Sakkwato Ta Sayo Manyan Tan-tan 250 Na Sama Da Naira Biliyan 22
  • Gwamnatin Zamfara ta amince da naɗin sabon Sarkin Katsinan Gusau
  • ’Yan bindiga sun kashe mutum 5 a sabon hari a Alkaleri
  • Gwamna Lawal Ya Naɗa Sabon Sarkin Gusau
  • Mutanen Sweida Na Kasar Siriya Suna Fama da Rashin Abinci da Ruwa
  • Arewa za ta kayar da Tinubu a zaɓen 2027 —Babachir
  • Harin Ta’addanci A Wani Coci Ya Lashe Rayukan Mutane Fiye Da 21 A Gabashin Kongo
  • Gwamnan Bauchi Ya Sulhunta Rikicin Manoma Da Makiyaya A Darazo
  • Gwamna Bauchi ya sasanta manoma da makiyaya a Darazo
  •  An Kashe Sojojin HKI 3 A Yankin Khan-Yunus Na Gaza