Leadership News Hausa:
2025-11-02@19:46:02 GMT

Darussa Daga Tafsirin Ramadan Daga Masu Bibiya (1)

Published: 4th, April 2025 GMT

Darussa Daga Tafsirin Ramadan Daga Masu Bibiya (1)

Na ji dadi da yadda ka yi kira ga sauran Malamai da su zama masu kwadaitar da neman Ilimi a kowanne fanni, sannan su kaurace wa furta haramci a kan abubuwan da Shari’a ba ta yi haramci a kai ba. Tabbas, ayoyin Alkur’ani suna nan kamar yadda aka saukar kuma ba za su sauya ba har duniya ta nade, amma fahimtarsu tana sauyawa daidai da zamani, don haka, bai dace a yi watsi da kimiyya da fasahar zamanin nan ba da ake ganin na turawa ne kawai, matukar ba a samu fiye da tasu ba.

Akramakallah, gaskiya ne, ya dace Malamai su rika ba da fatawa da ta yi daidai da zamaninsu da kuma fahimtar da al’ummar Musulmai Isharori na Alkur’ani, domin kamar yadda ka yi bayani, cewa, Suratul Bakara wacce ake ce mata “Surarar Saniya”, ba ta tsaya a kan saniya kawai ba, tana nufin Fadin Ilimi gaba dayansa, domin babu wani Ilimi a Alkur’ani face sai an ga wani abu na bayaninsa a cikin Suratul Bakrah.

Haka nan, misalin da ka bayar na cewa, a wannan zamanin Suratul Ankabuti, da ake fassara ta da “Surar Yanar Gizo-Gizo”, ya fi kyautatuwa a wannan lokacin a fassara ta da “Surar Website”.

Kazalika, Suratun Namli, da ke nufin “Surar Tururuwa”, ita kuma tana koya mana bin tsari, da abun da yake mai amfani da mara amfani da dai sauransu.

A gaskiya, na ji dadin karuwa da wannan ilimi daga tafsirin, Allah ya saka da alkhairi, ya kara ilimi da hikimomi na fahimtar Alkur’ani mai girma, amin.

Sako daga Ibrahim Sulaiman Muhammad

-Nau’o’in Halittar Allah Da Abubuwan Da Suka kunsa Hikima Ce Babba

Salam. Ya Sayyadi muna gabatar maka da gaisuwa ta amincin Allah, da fatan an yi Sallah lafiya. Allah ya saka muku da alkhairi. Bayan haka, muna mika godiya da irin karatun da muka ji game da hikimomin da Allah ya zuba a cikin dukkan sassan halitta, ta yadda komai ya zama littafi na ilimi mai zaman kansa. Hakika mun karu da bayani dalla-dalla da ka yi a game da matakan ilimi a matsayin KITABU, da abubuwan da suke kunsa.

A yanzu na fahimci cewa, hatta ruwan sama littafi ne saboda fannoni na haduwar ilimi ke samar da shi da kuma amfanin da yake yi. Don haka, idan mun sa lura, za mu ga cewa duk wani abu samamme yana zaman littafi ne sai dai ban da samuwar RABBUL IZZATI.

Allah ya saka muku da alkhairi da wannan wayar da kai da kake wa al’ummar Musulmi. Allah ya kara fahimta mai yawa ta isar da sakon Annabi (SAW).

Sako daga Abdullahi Jejiba Kaduna

-Alkur’ani Ba Shi Da Shamaki, Tabbas Ya Game Ko Ina Kuma Na Kowa Da Kowa Ne

Salamullahi alaikum. Ya Shehi, muna mika ziyararmu ta musamman, Allah ya saka muku da alkhairi. Farin ciki ya sa ni aiko da wannan sako a kan bayanin da ka yin a cewa, Alkur’ani mai girma littafi ne na duk duniya da Allah ya aiko Annabi Muhammadu (SAW) da shi, ba na musulmi ba ne kawai. Mun fahimci cewa duk wata kwarewa da ake takama da ita a duniya tana nan a cikin Alkur’ani kuma kowa zai iya amfana da Alkur’ani ya samar da ci gab awa kansa da garinsa da kuma duk duniya ma baki daya.

Haka nan, mun kara fahimtar ma’anar littafi da yadda ake fahimtar ilimomi da ke kunshe a karkarshin sunan littafi da harshen larabci na “Kitabu” ko “Khaddu” da sauran kalmomi irin su “Kataba”, musamman wadanda suka zo a cikin Alkur’ani mai girma. Bayanin da ka yi dangane da batun abubuwan da suka shafi “Hukunci” da wadanda karfin ikon hukunci yake hannunsu sun kara wayar mana da kai a game da yadda aka cakuda abubuwa a cikin addinin nan namu daga wadanda suka biye ma son ransu. Haka nan karin hasken da ka yi game da abin da ya shafi “Mutashabihun” da ma’aunin da ake ganewa sun kara mana ilimi sosai. Wallahi tafsirinka na rana ta uku ya ilmantar da mu sosai, Allah ya saka muku da alkhairi.

Sako daga Usman Yahaya Nuhu Goron Dutse.

-Manzon Allah (SAW) Ya Wayar Wa Duniya Kai A Kan Tsarin Zaman Madina

Salam. Ya Shehi, muna muku barka da ganin lokacin watan Azumin Ramadan na bana. Da fatan Allah ya karba mana da falalarsa. Allah ya kara muku koshin lafiya, ya kara hikima da basira ta wayar da kan al’ummar Musulmi. Hakik ana ji dadi da bayanan da na samu a cikin Tafsirinka na bana na rana ta hudu wanda muka fahimci Manzon Allah (SAW) ne ya fara kawo wayewar kai game da tsara daftarin hukuncin, watau ‘Consultation’ a duniya, a zamantakewar birnin Madina. Mutane da yawa suna wa tsarin zamantakewar jama’a bahaguwar fahimta, to amma wannan ya kara nuna mana yadda addinin Musulunci ya koyar da zama na birni wanda duk wani mai tutiyar wayewa zai fahimci daga tsarin Musulunci ne aka koya.

Har ila yau, hukunce-hukuncen da ka kawo na kyawawan dabi’u guda 38 da Allah ya kawo a cikin Alkur’ani, da yadda suke a cikin daftarin hukuncin na zamantakewa a Madina da Manzon Allah (SAW) ya tsara, wanda ya bai wa mace hakkokinta da tabbatar da tausayi da kuma girmama rayukan bil’adama, sun isar da kyakkyawan sako ga duk wani mai son sanin gaskiyar tsarin addinin Musulunci.

Mun kuma karu da bayanin da ka yi a kan hukunce-hukunce guda goma da Annabi  Isah (AS) ya dauka daga cikin Attaurar Annabi Musa (wasaayal Ashri) wadanda dukkansu hukunce-hukunce ne na hani masu zafi.

Ya Shehi, muna godiya da tsokacin da ka yi a kan hukunce-hukunce talatin da takwas (38) da ake kira da “Muhkamatu”, wadanda suka zo a cikin ayoyi takwas na Alkur’ani wadanda dai duk su ne na farko da suke a kan allon Attaura.

Muna kuma godiya da wayar mana da kai a game da cewa, babu kashe-kashen rayukan mutane da sunan addini a Musulunci, kasancewar duk yakokin da Annabi ya yi da sahabbansa, ya yi su ne domin kariyar kai ko kuma mayar da martani ga masu bore daga cikin al’umma.

Ya kamata lallai malaman addini da su gyara wa’azinsu game da hukuncin kisa a addini domin samun tabbataccen zaman lafiya, da yin kira ga al’umma a kan aikata kyawawan ayyuka nagari da kuma guje ma munanan ayyuka na duk nau’o’in alfasha. Allah ya saka muku da alkhairi. Mun gode.

Sako daga Aminu dahiru Rafindadi

-Mun Fahimci Bambancin Zaman Birni Da Na kauye, Akramakallah

Assalamu alaikum, Allah gafarta Malam, Allah ya saka maka da alkhairi. Tabbas tafsirinka na rana ta biyar ta fayyace mana abin da ya sa ake samun ci gaba a zaman birni saboda kasancewar nan ne matattarar mutane daban-daban don haka ake samun habaka da samun ci gaba irin na zamani saboda rungumar sauyin zamani. Sabanin kauye wanda su ba su yarda da kawo sauyi ko bakon abu. Tabbas, karamin gari ba ya rungumar sauyin zamani, yana nan a kan yadda yake duk da kuwa dimbin alkhairai da zamani ke tahowa da su, saboda haka ne ma ya sa, sai ka ga hatta mazauna garin sun fara ficewa, har wata rana a nemi kowa a rasa ko kuma a nan ne aka fi musunta sakon Ubangiji har a kai wani lokacin da Allah yake halakar da kauyen.

Halayyar kauye na tattare komai da kin yarda da sabbin abubuwa na ci gaba ko kin amincewa da kishiya tamkar musharaka ce da shirka, domin Allah Ta’ala ne ba ya son kishiya. Dole idan aka samu duhun kai irin wannan sai jarrabawa ta hau kan masu yi.

Mun gode wa Allah, da Shari’ar Annabi Muhammad (SAW), ta zama ta duniya ce baki daya (International), don haka ta zama mai sauki saboda duk abin da ya shafi duk duniya, ba wata al’umma daya ba, dole ne ya zama mai sauki.

Shari’ar Manzon Allah (SAW), Rahama ce ga dukkan Al’umma. Don haka, ya dace Malamai su rika kwadaitar da al’ummar Annabi (SAW) Rahamar Ubangiji, da kore haddi da Shubuha, domin Allah Ta’ala da ya sanya dokoki masu matukar wuya kawo shaidun haddin Zina wacce bulala ce sakamakonta, ba zai zama hikima ba kuma a ce ya bar haddin zubar da jini a fili sakaka.

Muna godiya da tarihin da ka bayar na kafuwar dimokuradiyya a Musulunci da aka faro daga kan khalifancin Sayyidina Aliyu (Karramallahu Wajhahu). Allah ya kara fikira da fahimta Albarkar Annabi (SAW).

Sako daga Abdullahi Mustapha Bauchi.

Alhamdu lillah, duk muna godiya da sakonninku masu bibiyarmu, Allah ya saka wa kowa da alkhairi. In sha Allahu za mu kawo ragowar sakonnin a gaba. Mun gode.

 

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: Dausayin Musulunci Allah ya saka muku da alkhairi da Allah ya

এছাড়াও পড়ুন:

Kotu ta tsige dan majalisar da ya sauya sheka zuwa APC

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta tsige dan majalisar wakilai, Abubakar Gummi daga kujerarsa saboda sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa APC.

Gummi yana wakiltar mazabar Gummi/Bukkuyum ta Jihar Zamfara a majalisar wakilai.

An raba wa iyalan jami’an ’yan sandan da suka rasu a bakin aiki a Borno N63.4m An sake kama shi a cikin ’yan fashi kwana 5 da fitowa daga kurkuku

Mai shari’a Obiora Egwuatu ne, ya yanke hukuncin, inda ya umarci kakakin majalisar wakilai, Tajudeen Abbas, da ya daina amincewa da Gummi a matsayin dan majalisar da ke wakiltar mazabar Gummi/Bukkuyum.

Haka kuma ya umarci hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) da ta shirya sabon zabe cikin kwanaki 30 domin cike gurbin kujerar dan majalisar.

Jam’iyyar PDP tare da shugaban ta na jihar Zamfara, Jamilu Jibomagayaki, ne suka shigar da karar dan majalisar.

Sun ce bai dace Gummi ya ci gaba da zama a kujerar ba bayan barin jam’iyyar da ta tsayar da shi takara.

Gummi, ta bakin lauyansa ya ce ya fice daga PDP ne saboda rikicin cikin gida da jam’iyyar ke fama da shi a matakin kasa da kuma a mazabarsa.

Amma kotu ta yi watsi da wannan hujjar, inda ta bayyana cewa babu takaddama da za ta ba shi damar ya sauya sheka.

A hukuncin da ya yanke, Mai shari’a Egwuatu ya ce ’yan siyasa dole su mutunta zabin jama’ar da suka kada musu kuri’a a karkashin jam’iyyar da ta tsayar da su takara.

Ya ce doka ba ta yadda da dan siyasa ya bar jam’iyyar da ta taimaka masa wajen lashe zabe sannan ya koma wata jam’iyya ba tare da ajiye mukaminsa ba.

Ya kara da cewa kuri’un da aka kada don dan takarar na jam’iyya ne, ba nasa ne na kashin kansa ba.

“Idan mutum yana son sauya sheka, ka da ya dauki amanar jama’ar da ta zabe shi ya tafi da ita,”  in ji alkalin.

Kotu ta kuma umarci Gummi da ya daina karbar albashi da wasu hakkoki a matsayin dan majalisa, tare da mayar da duk kudaden da ya karba daga ranar 30 ga watan Oktoba, 2024, zuwa ranar da aka yanke hukuncin.

Haka kuma, ya gabatar da hujjar mayar da kudaden ga kotu cikin kwanaki 30.

Mai shari’a Egwuatu ya kuma ci Gummi tarar Naira N500,000, domin biyan PDP kudaden da ta kashe wajen shigar da kara.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gwamnatin Isra’ila Tana Ci Gaba Da Hana Masu Jinya Zuwa Kasashen Waje Neman Magani Daga Gaza
  • Shin Mene Ne Matsalar Liverpool A Wannan Kakar?
  •  Gaza: Daga Tsagaita Wuta Zuwa Yanzu Fiye Da Mutane 200 Ne Su Ka Yi Shahada
  • ‘An Kashe Masu Zanga-zanga Akalla 500 a Tanzania’
  • An Cafke Ma’aikatan Gidan Marayu Da Suka Sayar Da Yara 4 A Kan Naira Miliyan 3
  • Ministan Wajen Malawi: Tsarin Ci Gaban Kasar Sin Ya Samar Da Darussa Ga Kasashe Masu Tasowa
  • ’Yan bindiga sun sace fasinjoji a cikin motocin bas a Kogi
  • Kotu ta tsige dan majalisar da ya sauya sheka zuwa APC
  • Allah Ya Kai Manzon Allah (SAW) Muƙami Na Babban Yabo A Cikin Komai
  • An sake kama shi a cikin ’yan fashi kwana 5 da fitowa daga kurkuku