2025-10-16@08:14:12 GMT
إجمالي نتائج البحث: 2937
«rasuwa»:
Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya fada a jiya Talata cewa ya bayar da umarnin aikewa da jiragen ruwa masu ninkaya a karkashin ruwa dake dauke da makaman Nukiliya da su karaci gabar ruwan kasar Rasha, a matsayin kandagarko. Trump ya kara da cewa; A cikin kwanakin bayan an aiko mana sakon barazana daga Rasha,...
Kungiyoyin gwgawarmaya na Hamas da Jihadul-Islami sun sanar da kai hari akan sojojin HKI da suke yin kutse a cikin yankin Gaza’ Rundunonin soja na “Al-Kassam” na Hamas da ‘Sarayal-Qudus” na Jihadul-Islami sun ce sun kai hare-haren ne akan sojojin mamayar da su ka shiga cikin yankunan Arewa da kudancin Gaza. A jiya Talata dakarun...
Sojojin na Yemen sun sanar da kai hari wani jirgin ruwa mai suna: MINERVAGRACHT’ saboda ya keta dokar hana zuwa tasoshin jiragen ruwan Falasdinu dake karkashin mamaya. Janar Yahya Sari ne ya yi wannan sanarwa yana mai kara da cewa; An kai harin ne akan ruwan tekun Aden ta hanyar amfani da wani makami mai...
Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, ya yaba wa ’yan Najeriya bisa abin da ya kira ‘hakurinsu, juriya da kwazo’ duk da tsananin matsin tattalin arziki da rashin tsaro da suke fama da shi. A cikin sakonsa na murnar cikar Najeriya shekaru 65 da samun ’yancin kai da ya aike ga ’yan kasa, Atiku ya...
Wata kotu a Jihar Florida da ke ƙasar Amurka ta aike da wani mutum Craig Vogt mai shekaru 61 gidan waƙafi, bayan samunsa da laifin yanka tsuntsayen Dawisu guda biyu, sannan ya yi dabge da naman su. Hukumomin Hudson, wani yanki da ke Florida, sun cafke mutumin ne bayan an samu rahoton abin da ya...
Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya jinjina wa ’yan Najeriya bisa abin da ya kira “juriya, haƙuri da ƙarfin halin da suke nunawa duk da matsin tattalin arziki da matsalolin tsaro” da ƙasar ke fuskanta. A cikin saƙonsa na taya ’yan Nijeriya murnar zagayowar ranar samun ’yancin kai da ƙasar ta yi shekaru 65...
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya yi kira ga daukacin jama’ar kasar Sin da su yi aiki tukuru, tare da ingiza wanzar da zamanantarwa irin ta Sin. Xi, wanda kuma shi ne sakataren kwamitin kolin JKS, kana shugaban hukumar zartarwar rundunar sojojin Sin, ya yi kiran ne yayin taron bikin cika shekaru 76 da kafuwar...
Gwamnatin Jihar Gombe ta ƙaddamar da wani shiri na rajistar yara kyauta domin rage adadin waɗanda ke zaune gida ba tare da zuwa makaranta ba. Bincike ya nuna cewa fiye da yara 787,000 ne ba sa zuwa makaranta a faɗin jihar, wanda hakan ya sanya gwamnatin ta tashi tsaye wajen kawo sauyi a ɓangaren ilimi....
Mataimakin shugaban kasar Iran ya bayyana cewa; Yakin kwanaki 12 da aka kaddamar kan Iran, gwaji ne na karfinta a fagen kimiyya da fasaha Mataimakin shugaban kasar Iran na farko Mohammad Reza Arif ya bayyana cewa: Wani bangare na ci gaban Iran a fannin kimiyya da fasaha na da nasaba da mayar da takunkuman da...

Janar Safawi; Iran Ta Kashe Matukan Jirgin Saman Isra’ila 16 A Yakin Kwanaki 12 Da Aka Yi A Tsakaninsu
Mai ba da shawara ga Jagoran juyin juya halin Musulunci Janar Safawi ya bayyana cewa: An kashe matukan jirgin saman yakin Isra’ila 16 a harin da aka kaddamar kan Iran Mai ba da shawara ga Jagoran juyin juya halin Musulunci Manjo Janar Yahya Rahim Safawi ya sanar da cewa: Iran ta harba makamai masu linzami...
Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas, ta ce kawo yanzu bata samu ba ta samu rubutaccen shirin zaman lafiya na shugaban Amurka Donald Trump kan Gaza ba. Mahmoud Mardawi wani babban jami’in kungiyar ta Hamas ya bayyana cewa har yanzu kungiyar ba ta samu daftarin shirin, wanda kafofin yada labaran Amurka suka wallafa bayanansa. Amma ya...
Shugaban kasar Madagaska Andry Rajoelina ya sanar da korar daukacin mambobin gwamnatinsa biyo bayan mummunar zanga-zangar da aka shafe kwanaki ana yi a kasar. A wani jawabi da ya yi na tsawon mintuna 17, ranar Litini, , Andry Rajoelina ya sanar da cewa ya ji kiran matasa tare da korar firaministansa da gwamnatinsa. Ya fara...
Gwamnatin tarayya ta soke bikin faretin da aka shirya gudanarwa domin murnar cikar Najeriya shekaru 65 da samun ‘yancin kai a ranar Laraba, 1 ga watan Oktoba. Wannan sanarwar ta fito ne a ranar Litinin daga Ofishin sakataren gwamnatin tarayya. “Soke faretin bikin ƴancin kai da gwamnati ta shirya gudanarwa a ranar Laraba, 1 ga...
Gwamnatin Tarayya ta sanar da gobe Laraba a matsayin ranar hutu a ƙasar somin bikin cikar ƙasar shekara 65 da samun ƴancin kai. Cikin wata sanarwa da ministan cikin gida na ƙasar, Olibunmi Tunji-Oja ya fitar, ya taya ƴan Najeriya murnar cimma wannan ”babban matsayi”. Ministan ya kuma buƙaci ƴanƙasar su ci gaba da nuna...
Shugaban hukumar kula da fice ta kasa iran frud askari ya bayyana cewa yawan adadin huldar kasuwancin na kasashen waje na kasar iran yana ci gaba da gudana tsakaninta da fiye da kasashen duniya 100. Kuma yawansa ya kai dala biliyan 54.311a cikin wata shidan farko na wannan shakarar. Da yake hira da manema labarai...
A ranar Talatar nan ake sa ran ci gaba da tattaunawa tsakanin Ƙungiyar Manyan Ma’aikatan Man Fetur (PENGASSAN) da Kamfanin Matatar Man na Ɗangote kan taƙaddamar da ke tsakaninsu. Ana sa ran za a ci gaba da zaman sulhun, wanda Gwamnatin Tarayya ta kira domin sasanta ɓangarorin ne zuwa da yamma. Hakan ta faru ne...
Fira Ministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya ba wa Gwamnatin ƙasar Qatar haƙuri kan harin da ƙasarsa ta kai a birnin Doha, wanda ya yi ajalin wani jami’in tsaron Qatar. Netanyahu ya bayar da haƙuri ne a yayin wata tattaunawa da shugaban Amurka, Donald Trump ya shirya tsakaninsu da Fira Ministan Qatar, Mohammed Al-Thani. A saƙon...
An zartar da hukuncin kisa a kan daya daga cikin manyan ma’aikatan leken asiri a Iran da ke aiki da hukumar leken asiri ta gwamnatin Isra’ila, Mossad, kamar yadda ma’aikatar shari’a ta Iran ta tabbatar. An zartar da hukuncin ne a kan Bahman Choubi-Asl a ranar Litinin bayan samunsa da laifin haɗa kai tare da...
Ali Larijani, sakataren majalisar koli ta tsaron kasar Iran, wanda ya ziyarci kasar Lebanon domin halartar bikin zagayowar shahadar Sayyid Hassan Nasrallah, ya gana da babban sakataren kungiyar Hizbullah Sheikh Naim Qassem. Babban labarin jaridar Pars Today na cewa, Ali Larijani, sakataren majalisar koli ta tsaron kasar Iran ya gana da babban sakataren kungiyar Hizbullah...
A wata hira da gidan talabijin din Aljazeera yayi da sakataren cibiyar kula da yan gudun hijira a kasar Nowy ya fadi cewa babban abin da yake damunsu shi ne inda duniya ta yi shiru kan abubuwan da ke faruwa a Gaza inda israa’ila ke kisan kiyashi. Dubban daruruwan alummar Gaza ne suka tarwatse da...
Shugaba Bola Tinubu ya amince da sabon tsari da ya danganci rajistar masu bautar ƙasa (NYSC) da manufofin hukumar da ke tattara bayanai kan ilimi wato NERD. A yanzu dai babu ɗalibin Nijeriya – daga jami’a ko kwalejin kimiyya da fasaha ko kwalejin ilimi, ko jami’o’in ƙasashen waje – wanda za a amince don samun...
Gwamnatin Nijeriya ta ayyana ranar Laraba, 1 ga watan Oktoba, 2025 a matsayin ranar hutu albarkacin cikar ƙasar shekaru 65 da samun ’yancin kai. Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwa da Ministan Harkokin Cikin Gida, Dakta Olubunmi Tunji-Ojo, ya fitar a madadin Gwamnatin Tarayya. Ɗalibar jami’ar IBB ta faɗi ta rasu FERMA ta ƙaddamar da...
Wata ɗalibar aji biyu a sashen nazarin ƙwayoyin halittu da sunadarai na Jami’ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBBU), Lapai da ke Jihar Neja ta riga mu gidan gaskiya. Aminiya ta ruwaito cewa, Fatima Adamu Muhammad, ta rasu ne bayan ta yanke jiki ta faɗi a wani matsuguninta da ke wajen makarantar. ASUU ta bayar da wa’adin...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
’Yan sanda sun kama miyagun kwayoyi da kudinsu ya kai Naira miliyan 165.4 a watan nan na Satumba a Jihar Kano. Daga ciki, jami’an rundunar sun kama kwayoyin da kudinsu ya kai Naira miliyan 82.7 a unguwar Rimin Auzinawa, suka mika ga Hukumar Yaki da Ta’ammali da Miyagun Kwayoyi (NDLEA) domin kammala bincike da gurfanarwa...
Kwamitin harkokin waje da tsaron kasar Iran ya kammala dukkan shirye shirye na ficewar kasar daga yarjeniyar NPT ta hana yaduwar makaman nukliya ko na kissan kare dangi. Isma’il Riza’e shugaban kwamitin ya fadawa ya fadawa tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran kan cewa, kwamitinsa ya kammala shiri na dukkan takardu da tsare-tsaren da...
Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkiya ya bayyana cewa bukatun gwamnatin Amurka daga kasar Iran ba abar amincewa ba ne. Shugabany a bayyana haka ne a ranar Asabar kafin ya bar birnin Newyork zuwa Tehran bayan ya halarci taron babban zauren MDD na shekara shekara. Yace: Bamu daidaita da su kan snapback ba, sai Amurka tace...
Mohammad Bakir Qalibof kakakin majalisar dokokin kasar Iran ya bayyana cewa abinda kasashen turai uku suka yi na amfani da Snapback baya bisa ka’ida kuma Iran ba zata kiyayesu ba. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Qalibaf yana fadar haka a jiya Lahadi ya kuma kara da cewa kasashen Rasha da China...
Gwamnatin Tarayya ta tabbatar wa da ƴan Nijeriya cewa za a ci gaba da samun isasshen man fetur duk da barazanar shiga yajin aiki da ƙungiyar PENGASSAN ta yi kan taƙaddama da matatar man Dangote. Wannan na zuwa ne bayan raɗe-raɗin cewa matatar ta dakatar da tsarin siyar da ɗanyen mai da ake biya sa...
A ranar Laraba, 1 ga watan Oktoba, 2025, jirgin ƙasan da ke jigilar fasinja tsakanin Abuja zuwa Kaduna zai dawo aiki. Hukumar Sufurin Jiragen Ƙasa ta Najeriya (NRC) ta ce jirgin farko a ranar zai baro tashar Idu da ke Abuja da ƙarfe 8.45 na safe, ya iso Kubwa 9.05 sannan ya sauka a tashar...
A jiya Lahadi ne masu tafiyar da ayarin jiragen ruwan dake son keta killace Gaza ” Sumud” su ka sanar da cewa, tsakaninsu da yankin Gaza bai wuce kilo mita 825 Ba. Ayarin jiragen ruwan dai yana kunshe da kananan jiragen da sun kai 50, sun fuskanci hare-hare da jiragen sama marasa matuki na HKI...
A wani taron da jakadun kasashen Fransa, Jamus da Ingila su ka yi, sun yi wa Rasha gargadin cewa, za su rika kai wa jiragenta na yaki hari, idan su ka keta hurumin samaniyar daya daga cikin kasashen mambobi na Nato. Kamfanin dillancin labarun “Blumberg” ya watsa wani rahoto da a ciki ya bayyana cewa;...
Al’ummar unguwar Kuntau da ke Ƙaramar Hukumar Gwale a Jihar Kano, sun shiga jimami bayan rasuwar wani matashin limami, Salim Usman, wanda ake zargin ya rasu a hannun ’yan sanda. An kama Salim mai shekara 24 a gidansa a ranar 22 ga watan Satumba, jim kaɗan bayan jagorantar sallar Magariba. 2027: APC za ta ƙwace...

Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Ta Jaddada Aniyarta Ta Rashin Amincewa Da Duk Wani Takunkumi Kan Iran
Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ta jaddada cewa: Ba za a yarda da ƙoƙarin maido da kudurori da suka ƙare ba kan Iran Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta tabbatar da cewa: Yunkurin da kungiyar Tarayyar Turai Troika da Amurka ke yi na maido da kudurorin Majalisar Dinkin Duniya da suka kare kan Iran, ba abu...
Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran ya jaddada cewa; Ba dole ba ne Iran ta bi hukunce-hukuncen da ba bisa ka’ida ba Shugaban Majalisar Dokokin kasar Iran Mohammad Baqir Qalibaf ya tabbatar a cikin jawabinsa yayin zaman majalisar a yau Lahadi cewa: Iran ba ta daukar kanta a matsayin wajibcin aiwatar da kudurorin kwamitin sulhun...
Yayin da yake bayani kan muhimmancin wannan shiri, Kwamishinan Yada Labarai na Jihar Kaduna, Malam Ahmed Maiyaki, ya ce: “Wannan Cibiyar wata gagarumar alama ce ta kudurin Gwamnatin Jihar Kaduna na bunkasa koyon sana’o’i, karfafa matasa, da haɓaka tattalin arziki. Yace An zaɓi fannonin sana’o’i 14 ne cikin hikima domin su magance manyan bukatun...
Majalisar Dinkin Duniya ta sake ƙaƙaba wa Iran takunkumai na karayar tattalin arziki bayan gaza cimma matsaya a tattaunawar ƙarshe kan shirin nukiliyarta da manyan ƙasashen yammacin Turai. Birtaniya, Faransa da Jamus ne suka bijiro da batun maido da waɗannan takunkuman a taron kwamitin Sulhu na Majalisar Ɗinkin Duniya, wanda aka yi kan saɓa yarjejeniyar...
Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya ce kasarsa za ta gwammace ta fuskanci mayar da takunkumin da aka kakaba mata, maimakon ta mutunta bukatar Amurka da ke neman Iran din ta mika dukkanin tataccen Uranium da take da shi. Da yake zantawa da manema labarai kafin ya bar birnin New York zuwa birnin Tehran, Pezeshkian...
Babban sakataren kungiyar Hizbullah Sheikh Naim Qassem ya tabbatar da cewa gwagarmaya ba za ta bari a kwance damarar ta ba, kuma za ta shiga fada irin na Karbala idan hakan ya kama, ya kara da cewa: “Za mu fuskanci duk wani aiki da zai yi wa Isra’ila hidima, ko da kuwa an mayar da...
Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta sake jadda yin Allah-wadai da kisan tsohon shugaban kungiyar Hizbullah Sayyed Hassan Nasrallah, inda ta bayyana cewa, matakin ya kasance karara a matsayin keta dokokin kasa da kasa da kuma tsarin Majalisar Dinkin Duniya. An fitar da sanarwar ne a wannan Asabar, a daidai lokacin da ake bukin cika...
Wani ɗalibi mai suna Ogbeche, ya kashe malaminsa Oshen, a makarantar sakandire da ke garin Ugboro, da ke Ƙaramar Hukumar Bekwarra a Jihar Kuros Riba. Rahotanni sun nuna cewa malamin ya yi ƙoƙarin raba faɗa tsakanin Ogbeche da wani ɗalibi. Ma’aikatan jinya sun tsunduma yajin aiki a Zamfara Matatar Ɗangote ta dakatar da sayar da...
Yayin da aka ce jam’iyyun siyasa a jamhuriya ta farko, sun fi karkata kan yanki, an yi yunkurin kafa jam’iyyun kasa a jamhuriya ta biyu da gangan. A wancan jamhuriyar (1979–1983), manyan jam’iyyun siyasar Nijeriya su ne GNPP, NPN, NAP,NPP, PRP, da kuma UPN. Duk da cewa, jam’iyyun sun banbanta a akida; amma ana ganin...
Aƙalla mutum bakwai ne suka rasu, yayin da wasu guda biyar suka ji rauni bayan wata tirela ta murƙushe motoci biyu a yankin Madalla, da ke kan hanyar Abuja zuwa Kaduna, a Jihar Neja. Hatsarin ya auku ne da misalin ƙarfe 11:30 na safiyar ranar Juma’a, lokacin da wata tirela ta samu matsalar birki, ta...
A cewarsa, rahotannin farko daga Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) sun nuna cewa Jihar Kaduna da Arewa maso Yamma na baya a yawan masu rajista, lamarin da ya jawo hankalin Gwamnatin Tarayya. Ya bayyana cewa an faɗaɗa taron ne da gangan don haɗa shugabannin ƙananan hukumomi, sarakuna, shugabannin addini, da ‘yan...
Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin mummunan lamari ga fararen hula a Gaza yayin da sojojin Isra’ila suka tsananta kai hare-hare ta sama kan yankin da aka yi wa kawanya. Da yake ambato ofishin kula da ayyukan jin kai na OCHA, kakakin MDD Stephane Dujarric, ya shaidawa manema labarai cewa “Sojojin Isra’ila sun zafafa kai...
Mutum huɗu sun rasa rayukansu sakamakon ruftawar da ramin da suke hakar ma’adanan ya yi, a Unguwar Dura da ke Ƙaramar hukumar Jos ta Kudu a Jihar Filato. Mai taimaka wa gwamnan Filato Caleb Mutfwang kan harkokin ma’adanai, Solomon Dung ya bayyana cewa, “Daga abin da aka gaya min, wasu matasa maza suna aiki a...
Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya sauka a Lagos a jiya Juma’a domin ziyarar aiki yayin da ƙasar ke shirin bikin cikar shekaru 65 da samun ƴancin kai daga turawan mulkin mallaka. A cewar kakakin shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, Tinubu ya tafi Legas ne bayan ya halarci naɗin sabon Olubadan na Ibadanland, Oba Rashidi Ladoja,...
Wakilan ƙasaahen duniya sun ƙaurace wa jawabin Shugaban Ƙasar Isra’ila Benjamin Netanyahu, a taron Majalisar Ɗinkin Duniya domin su nuna goyon bayansu ga al’ummar Palasɗinawa. Fiye da rabin wakilan da suka halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya (UNGA) sun miƙe tare da ficewa daga zauren taron ne a yayin da Mista Netanyahu yake shirin gabatar...
Gwamnatin Jihar Kano ta miƙa ƙorafe-ƙorafen da aka yi a kan Malam Shu’aibu Abubakar, wanda aka fi sani da Triumph, ga Kwamitin Shura na Jihar don ɗaukar matakin da ya dace. Sakataren Gwamnatin Jihar ne, ya tura ƙorafe-ƙorafen a ranar Juma’a, inda kwamitin ya fara zama domin sauraronsu. ’Yan Najeriya da tauraronsu ya haska a...
Sakataren Majalisar Koli ta Tsaron kasar Iran ya bayyana cewa, Tehran za ta katse yarjejeniyarta da take yi da hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya IAEA, tare da daina bada hadin kai ga binciken makamai na kasa da kasa, idan har aka aiwatar da tsarin “sake dawo mata da takunkuman Majalisar Dinkin Duniya. Sakataren...