Jigajigan Majalisar Ribas 17 Sun Sauya Sheƙa Daga PDP Zuwa APC
Published: 6th, December 2025 GMT
Kakakin Majalisar Dokokin jihar Ribas, Martin Amaewhule tare da mambobin majalisar su 15 sun sanar da sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa APC.
Amaewhule ya bayyana shawarar ’yan majalisar ne a zaman majalisa na ranar Juma’a, inda ya ce akwai abin da ya kira “rarrabuwar kai a fili” a cikin PDP wanda ya sa suka yanke wannan shawara.
Yayin da yake bayyana dalilin sauya sheƙar, Amaewhule ya ce sun bar PDP ne saboda rikice-rikicen cikin jam’iyyar.
Bugu da ƙari, a wani mataki da ake ganin na ƙoƙarin kaucewa gabatar da kasafin kuɗin shekarar 2026 daga Gwamna Siminalayi Fubara ne, Kakakin ya sanar da dage zaman majalisa har zuwa watan Janairu 2026.
Ayyukan majalisar a kwanakin baya-bayan nan sun nuna cewa har yanzu tsugune ba ta ƙare ba tsakanin bangaren zartarwa da majalisar jihar.
A watan Maris 2025, Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya ayyana dokar ta-baci a jihar bayan rikicin da ya ɓarke tsakanin gwamna da majalisa wanda kusan ya jawo rugujewar tafiyar da mulki a jihar.
Shugaban ƙasa ya kuma tsige Gwamna Fubara, mataimakinsa da kuma dakatar da majalisar jihar.
Sai dai an dawo da gwamnan da ’yan majalisar a jihar bayan an ɗage dokar ta-bacin a watan Satumba, tare da fatan cewa zaman lafiya ya dawo tsakanin bangarorin biyu.
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Sauya Sheka
এছাড়াও পড়ুন:
Ƙudirin dokar hukuncin kisa ga masu satar mutane ya tsallake karatu na biyu
Majalisar Dattawa ta amince da wani sabon ƙudiri da ke neman a gyara dokar yaƙi da ta’addanci, domin a ɗauki garkuwa da mutane a matsayin babban laifi na ta’addanci.
Ƙudirin, wanda Sanata Opeyemi Bamidele ya gabatar, ya tanadi hukuncin kisa ga duk wanda aka kama da laifin satar mutane, ba tare da wata zaɓin tara ba.
Tsaro: Gwamnatin Kano za ta fara amfani da jirage marasa matuƙa a iyakokinta Gobara ta ƙone kasuwar katako a AbujaSanata Bamidele, ya ce ƙudirin ya yi daidai da yunƙurin gwamnati da majalisa na kawo ƙarshen matsalar tsaro a ƙasar nan.
Yayin gabatar da ƙudirin, ya ce garkuwa da mutane na ƙara yawaita, kuma ƙungiyoyin miyagu na amfani da shi wajen tara k6udi, abin da ke jefa jama’a cikin tsoro da kuma daƙile karatun yara a jihohi da dama.
Sanatoci da dama sun goyi bayan hukuncin kisa, inda suka bayyana cewa hakan zai zama gargaɗi ga masu aikata wannan mummunan laifi.
Wasu kuma sun nemi a hukunta bankunan da ke taimakawa wajen aikewa ko karɓar kuɗaɗen fansa, yayin da wasu suka ce ya kamata a daina yi wa ’yan ta’adda afuwa.
Majalisar ta tura ƙudirin zuwa kwamitoci na musamman domin bincike, tare da umarnin su kawo rahoto cikin makonni biyu.