Radio Nigeria Kaduna Hausa:
2025-12-06@10:26:15 GMT

Yaƙin M23 Ya ci Gaba a Congo Duk da Sulhu da Rwanda

Published: 6th, December 2025 GMT

Yaƙin M23 Ya ci Gaba a Congo Duk da Sulhu da Rwanda

Bayan da ƙasashen biyu maƙwabtan juna na Congo da Rwanda suka sanya hannu a yarjejeniyar zaman lafiya da Donald Trump ya bayyana a matsayin mai cike da tarihi, jagoron na Amurka ya jinjinawa shugabannin ƙasashen biyu waɗanda ya ce sun yi hangen nesa wajen amincewa da kawo ƙarshen zubar da jinin dubban mutane tsawon shekaru.

An dai haska wannan zaman sanya hannu kai tsaye ta gidajen talabijin, inda shugabannin biyu wato Felix Tshisekedi na Jamhuriyyar Congo da Paul Kagame na Rwanda suka rattaɓa hannu a yarjejeniyar a gaban idon Donald Trump can a birnin Washington.

A cewar Trump shugabannin biyu sun ajje banbance-bambancen da ke tsakaninsu wajen rungumar zaman lafiya don jama’arsu.

Sai dai an sanya hannu a yarjejeniyar can a Washington dai dai lokacin da ake ganin ci gaban yaƙi tsakanin Sojin Congo da mayaƙan M23 da Rwanda ke marawa baya a kudancin lardin Kivu.

Babu dai wakilcin M23 a wannan tattaunawa ta Washington, hasalima basu aminta da yarjejeniyar da ka cimma a zaman ba, maimakon haka suna halartar nasu taron na daban wanda Qatar ke jagorantar sulhunta su da Congo a birnin Doha.

Masu sharhi na ganin  abu ne mai matuƙar wahala, yarjejeniyar ta birnin Washington ta yi tasiri wajen kawo ƙarshen wannan yaƙi na shekaru.

Yarjejeniyar na zuwa a dai dai lokacin da Amurka ke son zuba jari a ɓangaren haƙar ma’adinai a Congo inda a gefe guda itama Qatar ke faɗaɗa shirinta na zuba jari a ƙasashen Afrika.

 

উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa

কীওয়ার্ড: Rwanda Yaƙin M23 a yarjejeniyar

এছাড়াও পড়ুন:

Amurka ta Faɗaɗa Jerin ƙasashen Afrika Da ta Sanya wa Takunkumin Visa

Amurka ta faɗaɗa yawan ƙasashen da ta sanyawa haramcin samun bizar shiga ƙasar zuwa 32 ƙarƙashin jagorancin Donald Trump da ke tsaurara matakan shiga wannan ƙasa ta yammacin duniya saboda abin da ya kira barazanar ƙasashen ga tsaron Washington da kuma kange kwararar ƴan cirani.

Sakatariyar tsaron cikin gida ta Amurka Kristi Noem yayin wasu kalamanta a shirin kai tsaye ta gidan talabijin, ta ce dole ne Amurka ta dakatar da bizar ga duk wata ƙasa da ke turo mata baragurbi waɗanda ke wargaza tsaro da zaman lafiyarta.

Duk da cewa Noem bata bayyana sunayen ƙasashen ba, amma wasu bayanai da suka fita daga ma’aikatar sirrin ƙasar sun ce galibinsu ƙasashe ne na Afrika ciki kuwa har da Kenya da Angola da Masar da Habasha da Ivory Coast sai kuma Najeriya a gaba-gaba.

Wasu majiyoyi sun ce, daga cikin dalilan da ya sanya Amurka saka haramcin visa kan ƙasashen har da yadda wasunsu suka ƙi amincewa da karɓar ƴanciranin da Washington ke tisa ƙeyarsu, sai kuma batutuwa masu alaƙa da rashin isassun takardun shaida daga ƴan ƙasashen kana rashin inganci fasfo.

A cewar Noem yanzu haka ana ci gaba da tantance waɗannan ƙasashe don fitar da jerinsu, matakin da ke zuwa bayan tun a ranar 28 ga watan Nuwamban da ya gabata shugaba Trump ya sanya haramci visa kan mutanen da ke shigowa Amurkan daga ƙasashe matalauta ko masu fama da yaƙi.

Matakin na Amurka na zuwa bayan harin ranar 26 ga watan na jiya, da ya kai ga kisan wani Soja guda, harin da ake zargin wani ɗan ƙasar Afghanistan da kaiwa wanda aka ce ya shiga Amurkan don neman mafaka a shekarar 2021.

Ko a watan Yuni Amurka ta sanya haramcin visa kan ƙasashen Chadi da Congo da Equatorial Guinea da kuma Eritrea baya ga Libya da Somalia da kuma Sudan.

A wani mataki na daban kuma gwamnatin ta Amurka ta buƙaci tsauri kan matafiyan da ke shiga ƙasar daga Burundi da Saliyo da kuma Togo.

 

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Amurka ta Faɗaɗa Jerin ƙasashen Afrika Da ta Sanya wa Takunkumin Visa
  • Iran da Rasha sun rattaba hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna guda 20, kwangilolin haɗin gwiwa na fasaha guda biyar
  • Jigajigan Majalisar Ribas 17 Sun Sauya Sheƙa Daga PDP Zuwa APC
  • Dorinar Ruwa ta Yi Ajalin Mutane Biyu, ta Raunata Shida a Gombe
  • Akwai hannun ƙasashen waje a rashin tsaron Najeriya —Sheikh Gumi
  • Jami’an tsaro sun kama masu garkuwa da mutane 7 a Gombe
  • Trump Ya Yabawa Rwanda Da Kongo DMK Kan Sulhuntawa A Yakin Gabancin Kongo
  • Ziyarar Putin a Indiya alama ce da ke nuna cewa New Delhi na yin watsi da gargadin Trump?
  • Isra’ila Ta Hana Motocin Agaji 6000 Shiga Gaza Duk Da Yarjejeniyar Dakatar Da Bude Wuta