2025-10-14@05:34:59 GMT
إجمالي نتائج البحث: 2152
«ranar matasa ta duniya»:
Wakilan ƙasaahen duniya sun ƙaurace wa jawabin Shugaban Ƙasar Isra’ila Benjamin Netanyahu, a taron Majalisar Ɗinkin Duniya domin su nuna goyon bayansu ga al’ummar Palasɗinawa. Fiye da rabin wakilan da suka halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya (UNGA) sun miƙe tare da ficewa daga zauren taron ne a yayin da Mista Netanyahu yake shirin gabatar...
Rahotanni da suke fitowa daga Jahar Zamfara a arewacin Nigeria sun ce, mutanen da sun karaci 100 ake fargabar mutuwarsu saboda ruftawar ramin hako ma’adanai. Shedun ganin ido sun fada wa kamfanin dillancin labarun “Reuters” cewa; ramin hako ma’adanan wanda yake a yankin Kaduri dake karamar hukumar Maru ya fada akan ma’aikatan dake ciki. Lamarin...
Da dama daga cikin tawagogin da suke halartar taron babban zauren MDD na shekara-shekara sun fice a yayin da Fira ministan HKI ya fara jawabi, domin nuna kin amincewa da kisan kiyashin yankin Gaza. A jawabin nasa wanda tsirarun mutane su ka saurare shi, ya soki kasashen Faransa, Birtaniya, Australia da Canada da su ka...
Gwamnatin Jihar Kano ta miƙa ƙorafe-ƙorafen da aka yi a kan Malam Shu’aibu Abubakar, wanda aka fi sani da Triumph, ga Kwamitin Shura na Jihar don ɗaukar matakin da ya dace. Sakataren Gwamnatin Jihar ne, ya tura ƙorafe-ƙorafen a ranar Juma’a, inda kwamitin ya fara zama domin sauraronsu. ’Yan Najeriya da tauraronsu ya haska a...
Sakataren Majalisar Koli ta Tsaron kasar Iran ya bayyana cewa, Tehran za ta katse yarjejeniyarta da take yi da hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya IAEA, tare da daina bada hadin kai ga binciken makamai na kasa da kasa, idan har aka aiwatar da tsarin “sake dawo mata da takunkuman Majalisar Dinkin Duniya. Sakataren...
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya jaddada cewa: Mallakar makamashin nukiliya hakkin Iran ne, kuma tattaunawa da Amurka ya kai ga toshasshiyar hanya Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya gabatar da jawabinsa ta gidan talabijin, inda ya yi jawabi kan batutuwan cikin gida da na shiyya da kuma kasa da kasa....

Pezeshkian: Martanin Iran Zai Yi Daidai Da Sabon Halin Da Ake Ciki Kan Shirinta Na Makamashin Nukiliya
Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa; Martanin Iran zai yi daidai da sabon halin da ake ciki idan aka sake dawo da tsohon takunkumi kan kasarsa Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian a wata ganawa da ya yi da shugaban kasar Bolivia Luis Arce Catacora a birnin New York na kasar Amurka, ya jaddada cewa Iran...
Tashar ta jihar Legas na da natukar mahimmanci a tsarin jigilar shofar da kaya a kasar nan wadda kuma ta kasance a kan gaba wajen kara bunkasa fannin tattalin arzikin kasar nan. A hirar da da manema labarai Manajin Darakta na TTP Jama Onwubuariri ya bayyana cewa, wasu daga cikin nasarorin da aka samu a...
Dakarun Yaman sun sanar da cewa, sun kai wani harin soji mai inganci ta hanyar amfani da makami mai linzami na “Falasdinawa 2” mai dauke da kawuna da dama, kan wasu hare-hare da Isra’ila ta kai a yankin Jaffa da ta mamaye. A cikin wata sanarwa da mai magana da yawunta Birgediya Janar Yahya Saree...
Majalisar Dokokin Jihar Jigawa ta amince da ƙarin kasafin kuɗi na shekarar 2025 na Naira biliyan 75 na kasafin kuɗin jihar da ƙananan hukumomi. An amince da kasafin kuɗin ya zama doka ne a yayin zaman majalisar wanda mataimakin Shugaban Majalisar Hon. Sani Isiya ya jagoranta. Ana zargin mai shagon kemis da ya yi wa...
Har kullum Sin tana nacewa shawarwari, da tuntubar juna a matsayin muhimman matakan kyautata hadin gwiwa dake share fagen inganta cudanya. Tare da hakan, Sin na fatan Amurka za ta kaucewa kokarin dakile ci gabanta. Kuma duk wasu matakai na matsin lamba daga bangare guda kan kasar Sin, ba za su taba yin nasara ba,...
Dangin wata yarinya ’yar shekara 14 a unguwar Gangare da ke Karamar Hukumar Jos ta Arewa a Jihar Filato, sun nemi a bi musu haƙƙi bisa zargin fyaɗen da wani mazaunin unguwar ya yi mata. Bayanai sun ce tun farko an cafke mutumin da ake zargi, Ibrahim Rawi, wanda da fi sani da Baban Siyama,...
Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya bayyana cewa tattaunawa da kuma diblomasiyya basa da amfani idan har kasashen E3 sun maida takunkuman tattalin arziki a kan kasarsa. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto shugaban yana fadar haka a lokacinda yake ganawa da shugaban kasar Swiss Karin Keller-Sutter a gefen taron babban zauren...
An gurfanar da wasu malamai biyu na wata makaranta ta Zariya Children School da ke yankin GRA Zariya, a gaban kotun majistare da ke Tudun Wada bisa zargin lalata wata ɗalibar makarantar mai shekaru 11. Jami’in da ke gabatar da ƙara a gaban kotun, ASC Mustapha Abdulkadir, ya ce malamai biyu tare da wasu uku...
Shugaban Hukumar Alhazzan Jihar Yobe, Alhaji Mai Aliyu Usman Biriri ya bayyana cewar sun gudanar da aikin Hajjin 2025 cikin nasara da kwanciyar hankali. Mai Aliyu ya bayyana hakan ne ranar Laraba a tattaunawarsa da manema labarai a babban ɗakin taron Hukumar da ke garin Damaturu dangane da yadda suka gudanar da aikin hajjin bara. An...
Masu kula da jirgin ruwan agaji na keta killace Gaza ( Sumudu) sun sanar da samun gargadi daga kasashen duniya da dama akan cea Isra’ila tana shirin kai musu hari. Jiragen ruwan dake son kawo karshen killace sun kai 50, suna kuma dauke da kayan agaji HKI ta aike da jiragen sama marasa matuki wadanda...
Shugaban hukumar makamashin Nukiliya ta kasar Iran Muhamamd Islami ya bayyana cewa nan gaba kadan Iran za ta rika samar da megawatti 5000 na wutar lantarki daga tashar Nukiliya dake Bushehr. Kamfanin dillancin labarun “Mehr’ ya ambato shugaban hukumar makamashin Nukiliyar na Iran yana cewa; Ba da jimawa ba, tashar ta Nukilkiya dake Bushehr za...
Hukumar Binciken Manyan Laifuka ta Amurka (FBI) ta sanya la’adar Dala 10,000, kwatankwacin Naira miliyan 15 ga duk wanda ya bayar da bayanin da zai kai ga kama wani ɗan Najeriya mai suna Olumide Adebiyi Adediran. Ana dai neman Olumide ne a Amurka ruwa a jallo bisa zargin aikata laifukan zamba da dama. ’Yan bindiga...
A ƙarshe, Shugaban ya ce matakan da gwamnati ta ɗauka kamar cire tallafin mai da sauya tsarin kuɗi, duk duk sanya shan wahala amma wajibi ne domin tabbatar da cigaba. Ya jaddada cewa Nijeriya za ta ci gaba da kare haƙƙin ɗan Adam, da haɗin kai da zaman lafiya, inda ya gargaɗi duniya da cewa...
Gwamnatin jihar Kano, ta raba wa daliban da suka kamala karatun Furamare takardun gurbin karatu zuwa manyan makarantun sakandare a fadin jihar. Da yake jawabi yayin bikin kaddamarwar a makarantar sakandiren ’yan mata ta Maryam Aloma da ke Kano, Kwamishinan Ilimi na Jihar, Dakta Ali Haruna Makoda, ya ce shirin ya nuna yadda gwamnati...
Fadar shugaban kasar Rasha ta Kremlin ta yi watsi da kalaman da Shugaban Amurka Donald Trump ya yi kan yakin Ukraine. Mai magana da yawun shugaban Rasha, Dmitry Peskov, ya ce Rasha na nan a kan matsayinta na zakanyar kasa, kuma tana cikin kwanciyar hankali ta fannin tattalin arziki. Peskov ya tabbatar wa manema labarai...
Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya yaba da buɗe ofishin Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan a Majalisar Dattawa, inda ya ce haɗin kai ya yi nasara a kan zalunci. A ranar Talata ne Majalisar ta buɗe ofishinta, bayan rufe shi da aka yi tun daga 6 ga watan Maris, 2025, lokacin da aka dakatar da ita...
Jiya Talata 23 ga wata ne firaministan kasar Sin Li Qiang, ya halarci babban taro kan shawarar samar da ci gaba ga duniya baki daya, tare da gabatar da jawabi a hedikwatar Majalisar Dinkin Duniya dake birnin New York na kasar Amurka. A gun taron da kasar Sin ta dauki nauyin shiryawa, firaminista Li ya...
Darajar Naira ta ɗan ƙaru a kasuwanni, bayan Babban Bankin Najeriya (CBN), ya sanar da rage kuɗin ruwa daga kashi 27.5 zuwa kashi 27. Wannan mataki, a cewar masana tattalin arziƙi, na nufin gwamnati na ƙoƙarin rage matsin tattalin arziƙi da farashin kayayyaki ga ’yan ƙasa. ’Yan bindiga sun kashe mai juna biyu, sun sace...
Fitaccen mawakin nan na kudancin Najeriya David Adeleke, wanda aka fi sani da Davido, ya ba matarsa Chioma kyautar sabuwar motar alfarma kirar Mercedes-Benz G-Wagon ta shekarar 2025. Wannan motar mai tsada, wadda aka kaddamar da ita kwanan nan a kasuwar duniya, tana da farashin sama da $150,000 (kimanin Naira miliyan 240). Yada labaran karya...
Kamfanin GTCO, mamallakin bankin GT, ya bayyana samun ribar Naira biliyan 601 a watanni shida na farkon shekarar 2025. Sai dai bankin ya ce duk da haka ribar tasa raguwa ta yi a kan ta Naira tiriliyan daya da ya ci a farkon shekarar da ta gabata. Kotun Indiya ta daure dan Najeriya shekara 10...
Jagoran juyin juya halin Musulunci a cikin jawabinsa ya bayyana cewa: Dangane da hadin kan al’ummar Iran, batu na farko shi ne cewa a lokacin yakin kwanaki goma sha biyu, hadin kai da hadin kan al’ummar Iran ya sanya makiya kunya. Jagoran ya jaddada cewa tun tsakiyar tsakiyar yakin makiya sun gane cewa ba za...
Ali Larijani, sakataren majalisar koli ta tsaron kasa, ya rubuta a daren Talata a wani sako da ya wallafa a dandalin sada zumunta na X:“Da farko dai Amurka ta fice daga JCPOA, sannan Turai ta kasa cika alkawuran da ta dauka, a karshe ma sun kai harin bama-bamai, yanzu haka jam’iyyu suna yin kamar su...
Ministan harkokin wajen kasar Iran ya tattauna da fira ministan Norway game da alakar kasashen biyu da ci gaban kasa da kasa Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi wanda ke ziyara a birnin New York domin halartar taron shekara shekara na Majalisar Dinkin Duniya ya gana da fira ministan kasar Norway Jonas Gahr Støre. A...
Babban daraktan hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa ya sanar da cewa: Masu binciken hukumarsa suna kan hanyarsu ta zuwa Iran Babban daraktan hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa Rafael Grossi ya bayyana cewa: Masu sa ido na hukumar IAEA na kan hanyarsu ta zuwa Iran. Rafael Grossi ya...
Rundunar ’yan sanda a Jihar Kano ta sanar da cafke wani mutum da ke yi mata sojan-gona yana yaudarar jama’a domin karɓar musu kuɗi. An cafke wanda ake zargin ne a ranar Lahadi, 21 ga Satumbar 2025 a yankin Kofar Dawanau, sanye da kayan ’yan sanda, wanda bayanai suka ce ya daɗe yana aika-aikar. An yi...
Firaministan kasar Sin Li Qiang, ya isa birnin New York na Amurka da yammacin jiya Litinin, don halartar babban taron mahawara na MDD karo na 80. Yayin da yake birnin na New York, Li zai halarci wasu jerin ayyuka da Sin ta tsara, ciki har da taron manyan jami’ai game da shawarar tsarin shugabancin duniya,...

Kuri’ar Jin Ra’ayoyi Ta CGTN: Guguwar Amincewa Da Kasar Falasdinu Ta Nuna Yadda Amurka Da Isra’ila Suka Zama Saniyar Waren Da Ba A Taba Gani Ba
Ya zuwa ranar 23 ga watan Satumba agogon Beijing, kasashe 152 cikin 193 na Majalisar Dinkin Duniya sun amince da Falasdinu a matsayin kasa. A cikin kasashe biyar masu kujerun dindindin a kwamitin sulhun MDD, Amurka ce kadai ba ta amince da kafuwar kasar Falasdinu ba. Wannan guguwar ta amincewa da kafuwar kasar Falasdinu ta...
Yarima mai jiran gado na Masarautar Saudiyya, Sheikh Muhammad bin Salman, ya jagoranci sallar jana’izar fitaccen malamin addini, Sheikh Abdulaziz bin Abdullah bin Muhammad Al-Sheikh. Shafin Inside Haramain ya ruwaito cewa an gudanar da jana’izar ce a Masallacin Imam Turki bin Abdullah da ke birnin Riyadh. CBN ya rage kuɗin ruwa zuwa kashi 27 cikin...
Kwamitin da ke kula da tsare-tsare da manufofin kuɗi na Babban Bankin Najeriya (CBN) ya zaftare maki 60 daga nauyin kuɗin ruwa da ke kan masu karɓar basussuka. Wannan dai shi ne karo na farko cikin shekaru biyar da aka samu babban bankin ya yi rangwamin kuɗin ruwa a ƙasar. CBN ɗin ya ce kwamitin a...
Allah Ya yi wa Babban Mai Ba da Fatawa na kasar Saudiyya, Sheikh Abdulaziz bin Abdullah bin Mohammed Al Al-Sheikh, rasuwa. Hukumomin ƙasar Saudiyya sun sanar da cewa Sheikh Abdulaziz bin Abdullah bin Mohammed Al Al-Sheikh ya rasu yana da shekara 82 a duniya. Fadar Masarautar ƙasar da kuma Shugaban Majalisar Malaman Masallata Haraman Makkah...
Tawagar jami’an diflomasiyyan Falasɗinu ta gudanar da bikin ɗaga tutar ƙasar a Litinin ɗin nan a birnin Landan kamar yadda kafar labarai ta DW ta ruwaito. Bikin ɗaga tutar na zuwa ne kwana guda bayan da Birtaniya ta amince da Falasɗinu a matsayin kasa mai cin gashin kanta. CAC ta soma yi wa kamfanoni rijista...
Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta yi maraba da amincewar da kasashen Birtaniya, Australia, da Canada suka yi wa kasar Falasdinu, tana mai bayyana hakan a matsayin wani muhimmin mataki na tabbatar da hakkin al’ummar Palasdinu na kasarsu. A cikin wata sanarwa da ta fitar jiya Lahadi, kungiyar ta yi kira ga kasashen duniya da...
Iran ta bakin kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar, ta bayyana cewa “Kisan kare dangi da ake ci gaba da yi a zirin Gaza ya zama babban gwaji ga Majalisar Dinkin Duniya. Idan muna son kungiya mai inganci kuma mai amfani, dole ne mambobinta su dauki matakin gaggawa tare da tsayin daka wajen dakatar da wannan...
A yau Litinin Allah Ya yi wa Sarkin Ruman Katsina kuma Hakimin Batsari, Alhaji Tukur Ma’azu, rasuwa. Marigayin, wanda ya shafe shekaru 74 a duniya, ya daɗe yana fama da jinya gabanin rasuwarsa. Hisbah ta kama masu safarar mata zuwa Saudiyya a Kano Jariri ya mutu a bayan uwarsa yayin tsere wa ’yan bindiga a...
Matsalar tsaro san rufe kasuwannin shanu a yankin Kwara ta Kudu da kuma ɗauke sansanin masu yi wa ƙasa hidima (NYSC) da ke Yikpata, Ƙaramar Hukumar Edu an mayar da ita zuwa Ilorin, hedikwatar jihar. Ƙananan hukumomin biyu na Kwara ta Kudu da arewacin jihar na daga cikin wuraren da matsalolin tsaro suka fi taɓarɓarewa...

Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Ya Jinjinawa Tawagar Kokawar Greco-Roma Ta Iran Murnar Lashe Gasar Cin Kofin Duniya
Jagoran juyin juya halin Musulunci yana taya tawagar kokawa ta Greco-Roma ta Iran murnar lashe gasar cin kofin duniya Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya taya tawagar kokawa ta Greco-Roman ta kasar Iran murnar nasarar da ta samu a gasar cin kofin duniya, yana mai godiya ga ‘yan wasa da masu...

Pezeshkian: Kasashen Da Ba Su Cika Alkawura Da Suka Dauka Ba Suke Zargin Iran Kan Rashin Mutanta Yarjejeniyar Nukiliya
Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Kasashen da ba su cika alkawuran da suka dauka ba suke zargin Iran da rashin mutunta yarjejeniyar makamashin nukiliya Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya bayyana cewa: Kasashen da ba su cika alkawuran da suka dauka ba, a yanzu suke zargin Iran da kin mutunta yarjejeniyar makamashin nukiliyar. A...
Dakarun Kare Juyin Juya Halin Musulunci na Iran sun bayyana cewa: Duk wani sabon kuskuren lissafin makiya zai fuskanci mayar da martani mai muni A cikin wata sanarwa da suka fitar a farkon makon tsaro mai alfarma, na ranar tunawa da arangama da gwamnatin Saddam ta yi da Jamhuriyar Musulunci ta Iran a tsakanin shekarun...
Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya bar Abuja zuwa birnin New York na Ƙasar Amurka, domin halartar taron Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 80. Taron zai gudana daga ranar Litinin, 22 ga watan Satumba, zuwa ranar Lahadi, 28 ga watan Satumba, 2025. Birtaniya za ta amince da ƙasar Falasɗinu Jami’ar European-American ta musanta bai wa...
Aƙalla mutum ne sun rasu, yayin da wasu 16 suka jikkata a wani hatsarin mota da ya auku a Ƙaramar Hukumar Karasuwa, a Jihar Yobe. Kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Yobe, SP Dungus Abdulkareem ne, ya tabbatar da faruwar hatsarin ya faru a ranar Asabar da misalin ƙarfe 2:50 na rana a ƙauyen Zangon Kanwa....
Gwamnan Jihar Gombe, Muhammad Inuwa Yahaya, ya bai wa ƙungiyar maharba ta ƙasa (PROHAN) reshen Gombe, kyautar motoci Hilux guda biyu da kuma babura guda biyar domin taimaka musu wajen yaƙi da ’yan ta’adda da masu garkuwa da mutane. An miƙa wa shugaban ƙungiyar, Rabiu Baushe (Baushen Gombe) kyautar, wanda yana cikin shirin gwamnatin na...
Sabo da irin mawuyacin halin da ake ciki ta fannin tsarin jagorancin duniya musamman a daidai wannan lokaci, ya sa shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da shawarar inganta tsarin jagorancin duniya a kwanakin baya, shawarar da ta yi nuni da cewa, ya kamata a tsaya tsayin daka a kan kin yarda da daukar...
Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya bar Abuja zuwa birnin New York na Ƙasar Amurka, domin halartar taron Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 80. Taron zai gudana daga ranar Litinin, 22 ga watan Satumba, zuwa ranar Lahadi, 28 ga watan Satumba, 2025. Birtaniya za ta amince da ƙasar Falasɗinu Jami’ar European-American ta musanta bai wa...
Ƙasar Birtaniya a wannan Lahadin za ta amince a hukumance da kafa ƙasar Falasɗinu a matsayin ƙasa mai cin gashin kanta. Birtaniya wadda ta daɗe tana goyon bayan Isra’ila za ta juya mata baya, sakamakon hare-haren da Isra’ilar take kai wa Zirin Gaza, wanda ya samo asali bayan da ƙungiyar Hamas ta kai wani mummunan...