Pezeshkian: Martanin Iran Zai Yi Daidai Da Sabon Halin Da Ake Ciki Kan Shirinta Na Makamashin Nukiliya
Published: 26th, September 2025 GMT
Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa; Martanin Iran zai yi daidai da sabon halin da ake ciki idan aka sake dawo da tsohon takunkumi kan kasarsa
Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian a wata ganawa da ya yi da shugaban kasar Bolivia Luis Arce Catacora a birnin New York na kasar Amurka, ya jaddada cewa Iran za ta daidaita ayyukanta daidai da duk wani sauyi na al’amuran kasa da kasa idan aka sake dawo da tsohon takunkumi kan Kasarsa.
Pezeshkian ya bayyana cewa, manufofin bai-daya na Amurka suna yin illa ba wai ga Jamhuriyar Musulunci ta Iran kadai ba, har ma da dukkan kasashen da ba su dace da alkiblarta ba. Ya kuma jaddada bukatar kasashe masu cin gashin kansu su kara karfinsu na kimiyya da na musamman don kare muradunsu da diyaucin kasa.
Ya yi nuni da cewa, makomar huldar dake tsakanin Iran da Bolivia ta dogara ne da ra’ayi daya da kuma kudurin manyan jami’an kasashen biyu. Ya jaddada cewa Iran ta mallaki wannan tsayayyen kuduri, kuma manufofi da hanyoyin jami’an Bolivia za su taka muhimmiyar rawa wajen tantance yanayin hadin gwiwa a nan gaba.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Kasashen Rasha Da China Sun Bukaci A Jinkirta Batun Maido Da Takunkumi Kan Kasar Iran September 26, 2025 Magajin Garin Landan Ya Yi Dirar Mikiya Kan Shugaban Kasar Amurka Donald Trump September 26, 2025 Sojojin Yemen Sun Kai Wani Gagarumin Hari Kan Haramtacciyar Kasar Isra’ila September 26, 2025 Iran ta yi Allah wadai da yunkurin E3 na neman sake dawo mata da takunkumi September 26, 2025 Maduro jaddada hadin kai tsakanin al’ummomin Venezuela da Colombia September 26, 2025 UNRWA: Halin da ake ciki a Gaza ya yi muni matuka September 26, 2025 Sojojin Yaman: Mun kai hari kan sojojin mamaya a Jaffa September 26, 2025 Iran Ta Yi Tir Da ‘Hannun Diblomasiyya’ Na Trump Bayan Farmata Da Yaki September 25, 2025 Pezeshiyan: Babu Amfanin Tattaunawa Idan An Maida Takunkuman Tattalin Arziki A Kan Iran September 25, 2025 Iran Ta Nuna Bayanan Sirri Na Cibiyoyin Nukiliyar HKI September 25, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Makaman Iran Masu Linzami Ne Kandagarkon Dake Takawa Makiya Birki
Kwamandan rundunar soja ta “Sayyidush-shuhada” dake Tehran Janar Qurbani Muhammad Wali Zadeh ya bayyana cewa; makamai masu linzami da Iran take da su ne, da kuma jiragen sama marasa matuki suke takawa makiya birki.”
Janar Qurbani Muhammad Wali Zadeh ya kuma ce; Albarkacin sadaukar da jinanai da shahidai su ka yi ne da kuma kwazon kwararrun masana, su ka sa Iran samun wannan karfin da take da shi.
Wali Zadeh wanda ya halarci taron girmama rundunar sa-kai ta Basiji da kudancin birnin Tehran, ya kara da cewa, Iran ta samu matsayin da take da shi ne a wannan lokacin daga jihadin shahidai da tsayin dakar al’ummar Iran, sannan kuma ya kara da cewa; A halin yanzu karfin Iran a fagen makamai masu linzami ya kai kolin da makiya suka kwana da sanin cewa duk wata barazana ta kawo wa jamhuriyar musulunci hari, zai fuskanci martani mai tsanani.
Haka nan kuma ya ce; Al’ummar Iran ba ta taba zama mai tsokana da fara kai hari ba a cikin kowane fada, amma kuma ba ta ja da baya a gaban barazanar makiya.
Janar din sojan na Iran ya yi Ishara da martanin da Iran din ta mayar bayan shahadar Janar Shahid Kassim Sulaimani da ya tabbatar da karfinta na kare kai. Wannan karfin ne yake hana abokan gaba tarbar aradu da ka, su kawo wa Iran din hari.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Najeriya: Allah Ya Yi Wa Babban Malamin Addini Shehu Dahiru Bauchi Rasuwa November 27, 2025 An Zabi JMI A Cikin Majalisar Zartarwan Ta Hukumar Yaki Da Makaman Guba Ta Duniya CWC November 27, 2025 HKI Tana Amfani Da Tsagaita Wuta A Gaza Don Sake Shata Kan Iyakokin Yankin November 27, 2025 Yawan Falasdinawa Da Suka Yi Shahada Na Karuwa Saboka Keta Yarjeniyar Tsagaita Wuta November 27, 2025 An Rutsa Da Tsohon shugaban Kasar Najeriya A Guine Bissau Bayan Juyin Mulki November 27, 2025 Iraki: An Dakatar Da Tura Iskar Gas Zuwa Injunan Bada Wutan Lantarki A Yankin Kurdistan November 27, 2025 Ma’aikatar Harkokin Wajen Falasdinu Ta Sanar Cewa Akalla Yan Mata 33000 Ne Isra’ila Ta Kashe A Gaza November 26, 2025 Mataimakin Shugaban Nijeriya Ya Dawo Gida Bayan Kammala Taron G20 A Afrika Ta Kudu. November 26, 2025 Aljeriya Tayi Kira Da A Dakatar Da Israila Game Da Hare-haren Da Take Kaiwa November 26, 2025 Sojoji Sun Sanar Da Kwace Mulki A Kasar Guinea Bissau November 26, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci