Matatar Dangote ta janye ƙudirin sayar da man fetur a naira
Published: 28th, September 2025 GMT
Matatar Dangote ta janye ƙudirin dakatar da sayar da man fetur a naira, tana mai cewa abokan hulɗarta za su iya sayen man ta hanyar amfani da naira maimakon dala.
Lamarin na zuwa ne ƙasa da kimanin sa’o’i 24 bayan matatar ta sanar da dakatar da cinikayyar man fetur da naira.
Makon gobe za a dawo jigilar jirgin ƙasan Abuja zuwa Kaduna — NRC NECO ta sake jaddada nasarar ɗaliban Kano a jarrabawar banaBayanai sun an samu wannan sauyi ne bayan Shugaban Hukumar Tattara Haraji na Najeriya (FIRS), kuma shugaban kwamitin amfani da naira a kasuwancin man fetur, Dokta Zacch Adedeji ya shiga tsakani.
Gwamnatin Najeriya ce ta hannun kamfanin man fetur na ƙasar wato NNPCL ta kafa kwamitin domin ganin ana sayar da man fetur ga dilolin cikin Najeriya a naira maimakon dala.
Tun a ranar Juma’ar ce Matatar Dangote ta sanar da dakatar da amfani da naira wajen sayar da fetur, lamarin da ta ce zai fara aiki a ranar Asabar, 28 ga watan Satumba saboda a cewarta nauyin ya mata yawa, kuma ba za ta iya ci gaba ba.
Sai dai kuma a yammacin jiya Asabar ɗin matatar ta sake fitar da wata sanarwa, inda ta ce za ta ci gaba da sayar da fetur ɗin a naira.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Matatar Dangote Naira
এছাড়াও পড়ুন:
NAJERIYA A YAU: Amafani Da Karfin Soji Ko Tattaunawa Ne Zai Kawo Matsalar Tsaro A Najeriya?
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba
A cikin shekarun nan, matsalolin tsaro a Najeriya—kamar ta’addanci, da garkuwa da mutane, da rikicin manoma da makiyaya, da kuma ayyukan ’yan bindiga—suna kara ta’azzara, lamarin da ya sanya al’umma da masana tsaro ke tambayar wace hanya ta fi dacewa gwamatani ta yi amfani da shi wajen kawo karshen wadannan matsaloli da suka ki ci suka ki cinyewa tsawon shekaru.
Yayin da wasu ke ganin amfani da karfin soji ne kadai hanyar da zai kawo karshen wannan matsala, wasu na ganin tattaunawa ne kadai mafita, wasu har ila yau na ganin idan aka yi amfani da gaurayen biyun zai fi dacewa.
NAJERIYA A YAU: Irin Radadin Da Masu Cutar Amosanin Jini Ke Fuskanta DAGA LARABA: Shin Ya Kamata A Biya Kudin Fansa Ga Masu Garkuwa Da Mutane?Ko wanne daga cikin wadannan hanyoyi ne idan gwamnati ta yi amfai dashi ko da su don magance wannan matsala?
Wannan shine batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi duba a kai.
Domin sauke shirin, latsa nan