Aminiya:
2025-10-13@15:53:30 GMT

Matatar Dangote ta ci gaba da sayar da man fetur a naira

Published: 28th, September 2025 GMT

Matatar Dangote ta janye ƙudirin dakatar da sayar da man fetur a naira, tana mai cewa abokan hulɗarta za su iya sayen man ta hanyar amfani da naira maimakon dala.

Lamarin na zuwa ne ƙasa da kimanin sa’o’i 24 bayan matatar ta sanar da dakatar da cinikayyar man fetur da naira.

Makon gobe za a dawo jigilar jirgin ƙasan Abuja zuwa Kaduna — NRC NECO ta sake jaddada nasarar ɗaliban Kano a jarrabawar bana

Bayanai sun an samu wannan sauyi ne bayan Shugaban Hukumar Tattara Haraji na Najeriya (FIRS), kuma shugaban kwamitin amfani da naira a kasuwancin man fetur, Dokta Zacch Adedeji ya shiga tsakani.

Gwamnatin Najeriya ce ta hannun kamfanin man fetur na ƙasar wato NNPCL ta kafa kwamitin domin ganin ana sayar da man fetur ga dilolin cikin Najeriya a naira maimakon dala.

Tun a ranar Juma’ar ce Matatar Dangote ta sanar da dakatar da amfani da naira wajen sayar da fetur, lamarin da ta ce zai fara aiki a ranar Asabar, 28 ga watan Satumba saboda a cewarta nauyin ya mata yawa, kuma ba za ta iya ci gaba ba.

Sai dai kuma a yammacin jiya Asabar ɗin matatar ta sake fitar da wata sanarwa, inda ta ce za ta ci gaba da sayar da fetur ɗin a naira.

 

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Matatar Dangote Naira

এছাড়াও পড়ুন:

Macron Na Ci Gaba Da Shan Matsin Lamba Daga ‘Yan Adawa Da Tsofaffin Na Hannun Damansa

 

‘Yan sa’o’i kafin sanarwar da Jam’iyyar ta RN ta yi ne dai, tsohon Firaministansa Edouard Philippe ya ce yana goyon bayan shirya sabon zaben shugaban kasa a gaggauce.

 

Wannan matsin lamba dai kari ne kan wadda shugaban na Faransa ke fusakanta daga bangaren masu sassaucin ra’ayi, wadanda su kuma bukatarsu ita ce a zabi sabon Firaminista daga cikinsu.

 

Sai dai a iya cewa akwai ragowar fatan kawo karshen rudanin da siyasar Faransar ta shiga, la’akari da bayanan da suka ce a dazu an shiga tattaunawa tsakanin jagoran jam’iyyar masu ra’ayin ‘yan mazan jiya Bruno Retailleau da Firaminista Lecournu, kwana guda bayan murabus din da ya yi. Yayin da kuma a gefe guda rahotanni suka ce a gobe Laraba wakilan masu sassaucin ra’ayi na jam’iyyar Socialist za su gana da Firaminista Lecournun mai murabus.

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai Ko Afirka Za Ta Samu Kujerar Dindindin A Kwamitin Tsaro Na Majalisar Dinkin Duniya? October 12, 2025 Manyan Labarai Gwamna Sani Ya Gana Da Ministan Ayyuka Domin Ganin An Kammala Aikin Titin Abuja Zuwa Kaduna  October 12, 2025 Rahotonni Masana Sun Bayyana Yadda Za A Magance Ficewar Kamfanoni Da Masana’antu Daga Nijeriya October 11, 2025

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Yaƙin Gaza: Hamas da Isra’ila sun fara sakin fursunoni
  • Ta’addanci: Ana Fuskantar Ƙarancin Man Fetur A Mali Sakamakon Datse Hanyoyin Shiga Bamako
  • Ƴan Bindiga Sun Amince Da Dakatar Da Hare-Hare A Ƙananan Hukumomi 5 A Katsina
  • Kungiyar Malaman Jami’o’in Najeriya ASUU ta Shiga Yajin Aiki
  • Mutumin da ya sayar da ɗansa kan N1.5m ya shiga hannu a Ebonyi
  • Macron Na Ci Gaba Da Shan Matsin Lamba Daga ‘Yan Adawa Da Tsofaffin Na Hannun Damansa
  • Shugaban Kasar Najeriya Ya Yi  Afuwa Ga Wasu Mutanen Da Kotuna Su Ka Hukunta
  • Sojoji Sun Kashe Ƴan Ta’adda 9, Sun Ƙwato Naira Miliyan 5 A Borno
  • Dalilin IFAD Na Zuba Naira Biliyan 16 A Fannin Noma A Benuwe
  • 2027: INEC Ta Nemi A Gaggauta Amincewa Da Ƙudirin Sake Fasalin Tsarin Zaɓe