“Daga baya kuma sai ta fada cikin lamarin yin Takalma, sai dai abin ban takaici, ba tada isassun kudaden da za su taimaka mata don sabuwar harkar yin Takalma sana’ar da tasa kanta. Tana fatan idan ta samu isassun kudade, za ta sake komawa harkar.”

Miss Oforbiike ta kara yin bayanin ta hadu da abubuwan takaici, an maida ta wata ba kome ba, sai bakaken maganganu da ta fuskanta lokacin da take tafiyar da harkar.

Mista Celab Ogodo ya ce ‘Ina samun kudade da yawa ta hanyar tuka KekeNapep fiye da ma’aikatan gwamnati’

Ya kammmala karatunsa ne daga Kwalejin ilimi ta Jihar Ebonyi, ya ce shi bai dauki aikinsa kamar wanda bai dace ba, domin kullum yana samun Naira 15,000 bayan wasu kudaden da ya kashe.

AKWA IBOM: Wadanda suka kammala jami’a suna aiki kamar, Direbobin motar daukar fasinja, da kuma saayar da Kifi

Duk da Jihar tana daga cikin Jihohin da suke samar da Manfetur a Kudu maso Kudu, wadanda suka kammala Jami’oi suna tafiyar da rayuwarsu ta kudaden da suka samu ta hanyar kananan ayyukan da basu samun kudaden da za su ishe su tafiyar da rayuwa, irinsu suna da yawa a Jihar ta Akwa Ibom, musamman ma zirga – zirga, bangaren shari’a, sana’ar da bata taka kara ta karya ba a harkar ruwa, a wuraren da suke kusa da ruwa.

Wasu daga cikinsu,wadanda suke harkokin zurga- zurga domin samun abin rufawa kai asiri, sun bayyana wahalhalun da suka sha, bayan kammala karatun jami’a fiye da shekara 10 “amma babu wani ci gaban da ak samu.”

Ekene Stephen, shi ya karanta Philosophy ne kamar yadda ya ce: “Na kammala Jami’ar UYO tun shekarar 2011, amma har yanzu ban samu wani aiki mai nagarta ba.Na yi kokarin samun aikin gwamnati matsayin Malamin makaranta, amma har yanzu ban samu ba. An dauke ni aikin Malamin makaranta mai zaman kanta a God’s Power International School, amma albashi Naira 35,000 ne suke bani.

 

BENUWE:

A Jihar Benuwe, wasu daga cikin wadanda suka kammala Jami’a suna tuka Okada ne da kuma sayar da ruwan fiyo water da snack, domin kawai su samu damar na abinci da sauaran wasu abubuwa.

A tattaunawar da aka yi da shi, Ijiir-Iter Thomas, da ya kammala karatu, ya kuma karanta Geography daga Jami’ar Jihar Benuwe, 2007 ya ce tun da ya gama aikin yiwa kasa hidima (NYSC), ya nemi bukatar daukje shi ayyuka daban daban ciki da wajen Jihar, amma bai samu sa’ar samu ba, don haka ya yanke shawarar ya fara, da sayar da snacks (shawarma) a bakin titi, sana’ar daya koya a sansanin masu yiwa kasa hidima.

 

Kamar yadda ya ce da farko, naji tsoron irin maganganun da mutane za su yi – Dan Okada

 

RIBAS: Wadanda suka kammala Jami’a suna sana’ar sayar da manfetur a gidajen mai da kuma Malamai a makarantu masu zaman kansu.

Yawancin wadanda suka kammala Jami’a a Jihar Ribas suna yin wasu ayyukan da wasu kudade ake samu masu yaw aba, abinda ya fara daga msu sayar da man fetur a gidajen mai, da kuma kasancewa masu gadi, wadanda za su rika canjin iki saboda su rika zuwa aiki a makarantu masu zaman kansu.

Da take hira da Jaridar LEADERSHIP ta karshen mako, Ifeoma Cletus, da ta karanta Philosophy, tana koyarwa ne a wata makaranta mai zaman kanta a Fatakwal, tace rashin samun aikin ya sa ta yanke shawarar aikin koyarwa.

 

KADUNA:

A jihar Kaduna wasu daga cikin wadanda suka kammala Jami’a wadanda suka zanta da LEADERSHIP ta krshen mako sun bayyana rashin ingantattun ayyuka, da kuma irin matsin tattalin arzikin d ake fuskanta yanzu, na daga cikin manyan dalilan da suka sa su shiga irin su ayyukan da suke yi, domin kawai su samu damar tafiya da rayuwa, Wadanda suka kammala jami’a suna yin aiki ne a matsayin masu shara da goge a Otel ko kuma sana’ar Okada.

Mark Bala ya karanta Turanci ne a Jami’ar Ahmadu Bello Zariya, shi ma shi yake tukawa domin ya rufawa kan sa asiri abinda aka fi sani da Okada Rider, cewa ya kwashe shekara shida yana neman aiki amma bai samu ba.

Ya ce “Bayan ya kammala yiwa kasa hidima, a shekarar 2019, Ina nemi ayyukan yi, daga gwamanti da kuma wurare masu zaman kansu ba tare da ya samu ba. Ni yanzu mai sana’ar Okada ne.Ina ci da kaina da kuma iyalina, a a halin yanzu wannan shi ne aiki na. Wani lokaci na kan koma gida da Naira ku san 10,000 kowace rana bayan idan akwai gyare- gyare da kuma sayen mai.”

 

DELTA: Wadanda suka kammala jami’a suna aikin gyran mota, masu hana hatsaniya a gidajen shakatawa (Otel) da kuma kashe Beraye

Lokacin da Kareem Usman ya iso, birnin Benin, a shekarar 2015 bayan ya kammala yiwa kasa hidima, ya yi tsammanin ai shi zai samu kwanciyar hankali. Bayan shekarun da yayi na karade Nijeriyta wajen neman aiki, aiki da Kamfanin tayis na Chaina a gundumar Utesi a lokacin yana yiu ma kan sa kallon babu wanda ya fi shi sa’a.

“Ya zo birnin Benin ne saboda yayi aiki da Kamfanin Chaina wanda yake yi tayis,” ya tuna da wata ganawar da aka yi ma shi. “Kamfanin yana gundumar Utesi ne.”

Amma kuma daga baya sai farincikin da yake da shi ya koma bakin ciki.

“Saboda albshin bai taka kara ya karya bane ba zai ishe shi yin wani abu ba,” kamar yadda ya bayyana.“Ya yi shekara biyar kafin ya bar wurin. Saboda wurin da ya yi aiki idan ya yi kwana biyar bai je aiki ba, shikenan ya rasa albashin watan ke nan.”

 

ANAMBRA: Wadanda suka kammala jami’a suna aikin direbobin motocin fasinja da masu lura cunkoson abubuwan hawa

Chidiebere Chibueze, mai shekara 31, da Chioma Ifediorah suna daga cikin wadanda suka kammal akaratun Jami’a masu yawa a Awka, Jihar Anambra , wadanda dole ce ta sa, su ayyukan da suke yiu yanzu domin neman su tsira da mutuncinsu.

Yayin da Chibueze ya yi karatuns a a Jami’ar Jihar Imo 2015 da digirin din lamarin kasuwanci, Chioma ita kuma ta kammala Jami’ar Azikiwe Unibersity (UNIZIK), a Awka, shekarar 2009 da digiri din yadda za’a tafiyar da harkokin kudi.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: Wadanda suka kammala Jami a suna Wadanda suka kammala jami a suna wadanda suka kammala Jami a suna yiwa kasa hidima

এছাড়াও পড়ুন:

Rashin Amincewa Da Kasashen Yamma Yana Haifar Da Sabon Tunani Kan Huldar Kasa Da Kasa

A zahiri, zamanin da kasashen yammacin duniya ke ba da umarni ga kasashe masu tasowa ya riga ya wuce. An taba bin tsare-tsaren da kasashen yamma suka tanada, amma ba a samu nasarar da aka sa ran samu ba, wannan sakamako ya sa kasashe masu tasowa daina amincewa da huldar kasa da kasa da kasashen yamma suka tsara. Sai dai, ko wace irin sabuwar dangantakar sassan kasa da kasa muke bukata a zamanin yau?

 

A matsayinta na daya daga cikin kasashe masu tasowa, kasar Sin ta sha yin kira da a kafa sabon nau’in huldar kasa da kasa bisa tushen mutunta juna, da adalci, da hadin gwiwa don tabbatar da moriyar juna. Wannan tunani shi ma ya bayyana sarai a cikin babbar shawarar inganta jagorancin duniya da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar a watan jiya.

 

Yayin da ake kawo karshen tsohon zamanin da kasashen yammacin duniya ke taka rawa a matsayin masu ba da umarni a duniya, kasashe masu tasowa, ciki har da kasashen Afirka da kasar Sin, za su kara kawo ci gaba mai inganci, da adalci, da daidaito ga duniya, yayin da suke kokarin aiwatar da wasu sabbin tunani, gami da raya su a kai a kai. (Bello Wang)

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Ra'ayi Riga Cikar Wa’adin AGOA Ta Nuna Ra’ayin Amurka Kan Afirka October 7, 2025 Ra'ayi Riga Labaran Xinjiang A Zane: Manyan Sauye-Sauye A Fannin Ba Da Ilmi A Xinjiang September 30, 2025 Ra'ayi Riga Alfanun Harshen Mandarin A Kasashen Afirka September 29, 2025

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • ASUU ta tsunduma yajin aikin mako 2
  • Kungiyar Malaman Jami’o’in Najeriya ASUU ta Shiga Yajin Aiki
  • Mutumin da ya sayar da ɗansa kan N1.5m ya shiga hannu a Ebonyi
  • Rashin Amincewa Da Kasashen Yamma Yana Haifar Da Sabon Tunani Kan Huldar Kasa Da Kasa
  • ASUU za ta fara yajin aikin mako 2 daga ranar Litinin
  • Za A Yi Wa Masu Lalurar Ido Aiki Kyauta A Jihar Jigawa
  • Masana Sun Bayyana Yadda Za A Magance Ficewar Kamfanoni Da Masana’antu Daga Nijeriya
  • Ranar Malamai Ta Duniya: Rashin Kulawa Ke Sa Malamai Barin Aiki
  • Rashin wutar lantarki ta kassara kasuwanci a Kaduna, Kano da Katsina
  • Guguwar Ritaya Na Barazana Ga Ayyukan Hukumar Kwastam Yayin Da Jami’ai 825 Za Su Yi Ritaya