2025-07-11@06:40:32 GMT
إجمالي نتائج البحث: 105

«tsarin tarayya»:

(اخبار جدید در صفحه یک)
    Gwamnatin tarayya ta ce za ta hada gwiwa da gwamnatin jihar Jigawa wajen bunkasa kiwon dabbobi domin dorewar samar da abinci da ci gaban tattalin arzikin kasar nan. Ministan kula da ci gaban harkokin dabbobi Alhaji Idi Mukhtar Maiha ya bayyana haka, a lokacin da ya karbi bakuncin gwamnan jihar Jigawa Malam Umar Namadi a ma’aikatarsa da ke Abuja. Ya yi nuni da cewa, wani bangare na shirin shi ne kafa jami’an hadin gwiwa don gano wuraren da za a ba da fifiko da kuma samar da manufofin da za a iya aiwatarwa cikin gaggawa. Da yake yabawa jihar Jigawa bisa manufofinta na kiwo, ministan ya ce tsarin da gwamnatin jihar ta bullo da shi na bunkasa kiwon dabbobi...
    A na sa jawabin Ministan Bunkasa Hakar Ma’adanai Dakta Dele Alake, ya godewa Gallezot, kan yin aikin da ya yi dashi, wajen tabbatar da rattaba hannun wannan yarjejeniyar, duk da karancin lokacin da ake dashi na lokacin da yake da shi, a lokacin da Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya ziyarci Shugaban kasa Bola Tinubu. Adeleke ya yi nuni da cewa, sake sabunta wannan yarjejeniyar ta kawo karshen yunkurin ‘yan adawar siyasa na kasar nan, kan yunkurinsu na gayawa ‘yan Nijeriya bayanan karya kan manufar wannan yarjejeniyar. Ministan ya ci gaba da cewa, Kungiyar ta Makomar Ma’adanan Kasa, za ta bai wa kasashen biyu damar fahimtar yadda za a samar da tsare-tsare da dabaru da kuma ayyukan da ya kamata...
    Idris ya ce: “Waɗannan bala’o’i ne da yawancin su ɗan’adam ke haddasawa, kuma ba za mu bari su ci gaba da faruwa ba.   “Shugaban Ƙasa ya umarci Hukumar Wayar da Kai ta Ƙasa (NOA) da ta ƙara ƙaimi wajen faɗakar da jama’a da wayar da kan ‘yan Nijeriya, musamman masu wannan haramtacciyar sana’a. Wannan yanki yana da albarkatun ma’adinai da dama.   “Kwanan nan, Ma’aikatar Raya Ma’adinai ta Tarayya ta fara gyaran tsarin haƙar ma’adinai a faɗin ƙasar nan, kuma muna fatan za su ɗauki wannan darasi da muhimmanci.”   Ministan ya bayyana cewa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayar da umarni ga Ma’aikatar Raya Ma’adanai ta Tarayya da ta ƙara ƙaimi wajen tsaftace harkar haƙar ma’adanai don...
    Kungiyar Manyan Ma’aikatan Jami’a (SSANU) ta bayyana cewa jami’o’in gwamnati da dama a Najeriya sun shafe sama da watanni uku ba tare da wutar lantarki ba da za su gudanar bincike ko darussa ba. Kungiyar ta kuma yi barazanar ɗaukar tsattsauran mataki kan gwamnatocin jihohi da kamfanoni da suka ki fara biyan sabon mafi ƙarancin albashi ba na Naira dubu 70 da sauran sauye-sauye da ke tattare da shi zuwa ƙarshen watan Maris na shekarar nan ta 2025.   Shugaban Ƙungiyar SSANU ta Kasa, Kwamred ohammed Ibrahim, ne ya sanar da haka a yayin taron Majalisar Tuntuba ta Ƙasa (NAC) da ƙungiyar ta gudanar a Abuja. Kwamred Ibrahim ya bayyana cewa har yanzu Gwamantin Tarayya da na wasu jihohi ba...
    Sai dai, an kwashe fasinjoji 53 da ke cikin jirgin ba tare da jin wani rauni ba cikin aminci.   Ita ma Hukumar kula da Tsaro ta Nijeriya (NSIB) ta fara gudanar da bincike kan lamarin.   Amma hukumar da ke kula da harkokin tsaro, NCAA, a wata sanarwa da ta tabbatar da faruwar lamarin, ta ce za ta bayar da duk wani tallafin da ake bukata ga NSIB domin gudanar da cikakken bincike kan wannan lamarin.   Daraktan Hulda da Jama’a, Michael Achimugu a cikin wata sanarwa ya ce, “NSIB ce kadai za ta iya bayyana musabbabin wannan hatsarin idan ta kammala bincikenta.”