Fashewar Tayar Jirgi A Kano: Gwamnatin Tarayya Ta Dakatar Da Kamfanin Max Air Na Tsawon Watanni Uku
Published: 29th, January 2025 GMT
Sai dai, an kwashe fasinjoji 53 da ke cikin jirgin ba tare da jin wani rauni ba cikin aminci.
Ita ma Hukumar kula da Tsaro ta Nijeriya (NSIB) ta fara gudanar da bincike kan lamarin.
Amma hukumar da ke kula da harkokin tsaro, NCAA, a wata sanarwa da ta tabbatar da faruwar lamarin, ta ce za ta bayar da duk wani tallafin da ake bukata ga NSIB domin gudanar da cikakken bincike kan wannan lamarin.
Daraktan Hulda da Jama’a, Michael Achimugu a cikin wata sanarwa ya ce, “NSIB ce kadai za ta iya bayyana musabbabin wannan hatsarin idan ta kammala bincikenta.”
এছাড়াও পড়ুন:
Babban Jirgin Ruwan Kasar Sin Ya Nufi Yankin Tekun Kudancin Kasar Domin Gwaji Da Samar Da Horo
Kakakin ma’aikatar tsaron kasar Sin Jiang Bin, ya ce a baya bayan nan babban jirgin ruwan dakon jiragen sama na kasar Sin mai suna Fujian, ya doshi yankin tekun kudancin kasar, inda ya ratsa ta zirin Taiwan, a kan hanyarsa ta gudanar da gwaje-gwaje da samar da horo.
Jami’in wanda ya bayyana hakan a Talatar nan, ya ce hakan bangare ne na ayyukan da aka saba gudanarwa lokaci-lokaci a wani bangare na kirar jirgin.
Jiang Bin, ya yi tsokacin ne yayin da yake amsa wata tambaya mai nasaba da hakan da aka yi masa, yana mai cewa, bulaguron jirgin ya dace da dokokin kasa da kasa da ayyuka masu nasaba, kuma ba shi da wata nasaba da tunkarar wani sashe. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp