Kotun Tarayya Ta Dakatar Da Majalisar Dokokin Jihar Zamfara Daga Tsige Honarabul Ango
Published: 24th, February 2025 GMT
Babbar kotun tarayya da ke Gusau a jihar Zamfara ta dakatar da majalisar dokokin jihar daga tsige Honarabul Aliyu Ango Kagara, dan majalisar APC mai wakiltar mazabar Talata Mafara ta Kudu.
A wata sanarwa da Sakataren Yada Labarai na Jam’iyyar APC na Zamfara, Yusuf Idris Gusau ya fitar, ya bayyana cewa hukuncin ya biyo bayan wata kara mai lamba FHC/GSCS/10/2025 da Kagara ya shigar kan Majalisar Dokokin Jihar Zamfara, da Kakakinta, da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC).
Ta ce shari’ar da mai shari’a Salim Olasupo Ibrahim ya jagoranta ta kalubalanci tsige Kagara da shugabannin majalisar suka yi.
A cewar sanarwar, kotun ta bayar da umarnin wucin gadi na hana INEC gudanar da zaben cike gurbi na mazabar Talata Mafara ta Kudu, wanda Kagara ke wakilta a halin yanzu.
Mai shari’a Olasupo ya kuma bayar da umarnin tsayawa kan wannan hukunci har zuwa lokacin da za a ci gaba da sauraron karar da aka shigar a gaban kotu.
An dage sauraron karar zuwa ranar 12 ga watan Maris na 2025.
A halin da ake ciki, majalisar dokokin jihar Zamfara ta dakatar da ‘yan majalisa 9 da suka fito daga jam’iyyu daban daban, lamarin da ya rage yawan mambobinta da ke kasa da kashi biyu bisa ukun da ake bukata wajen zartar da kudiri.
Duk wata doka da aka zartar a ƙarƙashin wannan yanayi, ana iya ɗaukarta sabawa tsarin mulki.
Daga Aminu Dalhatu
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Majalisar Dokoki Zamfara
এছাড়াও পড়ুন:
Babu Wata Karamar Hukumar Dake Ƙarƙashin Ikon Ƴan Ta’adda A Filato -Gwamna Mutfwang
Gwamnan Jihar Filato, Barr. Caleb Mutfwang, ya bayyana cewa babu wata ƙaramar hukuma a cikin jihar da ƴan ta’adda ko ƴan bindiga ke da iko da ita. Ya bayyana hakan ne a yayin wata ganawa da ƴan jarida da aka gudanar a sabon gidan gwamnati da ke Little Rayfield, Jos, a ranar Talata.
Gwamna Mutfwang ya ce gwamnatinsa ta ƙara ƙaimi wajen yaƙi da matsalar tsaro, musamman ta hanyar farfaɗo da rundunar tsaron cikin gida ta jihar wato Operation Rainbow, domin tallafa wa sauran hukumomin tsaro wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
Ana Ci Gaba Da Alhinin Mutuwar Malam Adamu Fika Sojoji Sun Ƙi Karɓar Cin Hancin Miliyan 13 Daga Ƴan Ta’adda A FilatoYa ƙara da cewa, gwamnatinsa ba za ta yi ƙasa a gwuiwa ba wajen ganin an dawo da zaman lafiya a sassan jihar da rikice-rikicen ƙabilanci ko na addini suka taɓa. Ya ce gwamnati na aiki tare da hukumomin tsaro da shugabannin gargajiya domin tabbatar da fahimtar juna da daidaiton al’umma.
Gwamnan ya sake jaddada buƙatar kafa ƴansandan jiha, yana mai cewa hakan zai taimaka wajen rage matsalolin tsaro a faɗin Nijeriya. Ya ce kafa ƴansandan jiha zai bai wa gwamnatocin jihohi damar yin tsari da ɗaukar matakan da suka dace da yanayin tsaron yankunansu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp