Yadda Jami’an Tsaro Suka Fara Gyara Wa ‘Yan Jari Bola Zama A Abuja…
Published: 7th, February 2025 GMT
Obuah ya ce, makasudin yin bayanin shi ne don tabbatar da cewa masu aiki da doka ne kawai ke aiki a Babban Birnin Tarayya Abuja da kuma yaki da matsalar masu varna a yankin.
Ya ci gaba da cewa, wani samame da ‘yansanda suka kai a wasu kasuwannin Pantaker a baya-bayan nan ya yi nasarar kwato dukiyar al’umma da aka sace da suka kai sama da Naira biliyan daya.
“Saboda haka, Hukumar Babban Birnin Tarayya Abuja, tare da jami’an tsaro, ta bayar da umarnin cewa duk wani ma’aikacin pantaker dole ne a yi rajista da kuma bayyana sunansa. Wannan zai ba mu damar gano masu aiki na gaske kuma mu fahimci ayyukan kasuwancinsu.
“Haka zalika za a bukaci masu gudanar da aikin su rike rajistar masu saye da masu kaya. Muna bukatar mu san su wanene masu samar muku da kaya kuma wa kuke sayarwa. Samun wannan bayanin zai taimaka a kokarinmu na tsaro,” Obuah ya kara da cewa.
Ya shawarci masu sana’ar pantaker da su guji yin mu’amala da wasu mutane ba bisa ka’ida ba ko sayen kayan sata, yana mai gargadin cewa duk wanda aka samu da irin wannan kayan zai fuskanci kamawa tare da gurfanar da shi gaban kuliya.
Obuah ya kuma kara karfafa gwiwar ma’aikatan da su hada kai a karkashin wata kungiya domin samar da ingantaccen hadin gwiwa da gwamnati da hukumomin tsaro.
Daraktan Sashen Tsaro na Hukumar Babban Birnin Tarayya Abuja, Adamu Gwary, ya jaddada cewa masu sana’ar sayar Jari Bola ne kawai da aka sani za a yi musu bayani kuma a ba su izinin sake bude kasuwancinsu.
Ya umurci duk ma’aikatan da ba su yi rijista ba da su bi tsarin tantancewa kafin su ci gaba da aiki.
Da yake mayar da martani, Shugaban Masu Sana’ar Pantaker Operators na Kasa, Alhaji Abbas Bello, ya bayyana kudirin ma’aikatan na tallafa wa kokarin da suke yi na inganta sana’o’insu.
Ya yarda cewa akwai masu aikata laifuka a cikinsu kuma ya yi maraba da shirin a matsayin hanyar kawar da su.
Sakataren Kungiyar Malam Salisu Abubakar ya tabbatar da shirinsu na hada kai da jami’an tsaro domin yakar wannan varna a Babban Birnin Tarayya Abuja
কীওয়ার্ড: Tsaro Babban Birnin Tarayya Abuja
এছাড়াও পড়ুন:
Tinubu Ya Nuna Farin Cikinsa Bisa Bayyanar Daliban Kebbi, Ya Bukaci a Ceto Sauran
Daga Bello Wakili
Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya bayyana farin cikinsa bisa dawowar ’yan mata 24 da ’yan ta’adda suka sace a Maga, Jihar Kebbi.
’Yan ta’addan sun kai hari makarantar ranar 17 ga wantan Nuwamban 2026, inda suka yi awon gaba da ’yan matan, jim kaɗan bayan wata rundunar soji ta bar harabar makarantar.
Lamarin Kebbi ya haifar da wasu sace-sace makamanta a Eruku da ke Jihar Kwara da kuma Papiri a Jihar Neja.
An sako dukkan mutune 38 da aka sace a Eruku ranar Lahadi, inda a wannan ranar ce shugaban kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) Jihar Neja ya ce an samu yara 50 daga cikin ɗaliban makarantar Katolika da suka ɓace a gidajen iyayensu.
Shugaba Tinubu ya yaba wa jami’an tsaro bisa ƙoƙarin da suka yi wajen ganin an kubutar da dukkan mutanen da ’yan ta’adda suka sace.
Ya umarci jami’an tsaro da su ƙara ɗaukar matakan gaggawa don ceto sauran ɗaliban da har yanzu ke hannun ‘yan bindiga.
“Ina farin cikin cewa an samu dukkan ’yan mata 24. Ya zama wajibi mu ƙara tura jami’an tsaro yankunan da ke da rauni don hana sake faruwar irin wannan lamari. Gwamnatina za ta bayar da dukkan tallafin da ake buƙata don cimma haka,” in ji Shugaba Tinubu.