An Sace Dalibin Jami’ar Tarayya Birnin Kebbi
Published: 10th, April 2025 GMT
Rundunar ‘yan sandan jihar Kebbi, ta tabbatar da sace wani dalibi dan aji 4 na Jami’ar Tarayya ta Birnin Kebbi, mai suna Augustine Madubiya, mai shekaru 23 da haihuwa, wanda ke Sashen Tattalin Arziki zuwa inda ba a san inda aka nufa ba.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Nafiu Abubakar, ya shaida wa manema labarai cewa, wasu gungun ‘yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun kai farmaki gidan Istijaba Villa da ke karamar hukumar Kalgo a jihar inda suka yi garkuwa da wani dalibi a dakin kwanan dalibai a harabar jami’ar, kuma abin bakin ciki, wani Malam Siddi Hussaini, wanda ke kusa yana kiwon shanun sa, a lokacin da yake kokarin shiga tsakani, shi ma likita ya samu rauni a harin.
A cewarsa, yayin da yake samun rahoton, jami’in ‘yan sanda na yankin, Kalgo, ya tara tawagar jami’an tsaro hadin gwiwa zuwa wurin da lamarin ya faru, kuma a halin yanzu rundunar jami’an tsaro na ci gaba da sintiri dazuzzuka da kuma hanyoyin da ke kusa da wurin da nufin ceto wanda aka yi garkuwa da shi ba tare da jin rauni ba tare da damke wadanda suka aikata wannan ta’asa.
Hakazalika, a ranar Lahadin da ta gabata ne wasu ‘yan bindiga da ake kyautata zaton ‘yan bindiga ne na Lakurawa da ke dauke da manyan muggan makamai suka kai farmaki kauyukan Tungan Taura da Tungan Ladan, a karamar hukumar Augie a jihar Kebbi, inda suka yi awon gaba da wasu shanu da ba a tantance adadinsu ba, suka kashe mutum goma sha shida.
SP Nafiu Abubakar ya ce, tun daga lokacin an dawo da zaman lafiya a yankunan da lamarin ya shafa kuma an fara gudanar da cikakken bincike.
Abdullahi Tukur
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
এছাড়াও পড়ুন:
Ƴansanda Sun Kama Wani Mai Wasa Da Bindiga AK-47 A Cikin Wani Bidiyo A Adamawa
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Kifewar Kwalekwale: Gwamnan Gombe Ya Jajanta Wa Al’ummar Nafada Kan Mutuwar Matasa Biyar October 31, 2025
Manyan Labarai NPA Da Ƙungiyar Injiniyoyi Ta Yi Haɗaka Don Bunƙasa Tashoshin Jiragen Ruwa October 31, 2025 Labarai Ranar Foliyo Ta Duniya: Muna Fatan Ganin Karshen Cutar Foliyo A Jihar Katsina -Zulaihat Dikko Radda October 31, 2025