Gwamnatin Tarayya Ta Bai Wa Jihar Jigawa Kayayyakin Noma Na Sama Da Naira Biliyan 5
Published: 19th, February 2025 GMT
Gwamnatin tarayya ta ce ta bai wa gwamnatin jihar Jigawa tallafin kayayyakin noma na sama da naira biliyan 5 domin bunkasa noman abinci a fadin jihar.
Ministan noma da samar da abinci Sanata Abubakar Kyari ya bayyana haka a lokacin da yake jawabi a garin Dabi da ke karamar hukumar Ringim a bikin ranar manoman alkama ta bana.
Ya bayyana cewa, matakin na daga cikin kudirin gwamnatin tarayya na tallafawa jihar wajen bunkasa noma domin kasuwanci.
Sanata Kyari ya yi nuni da cewa, gwamnatin tarayya ta gamsu sosai da yadda gwamnatin jihar Jigawa da manoma suka yi, na rungumar ayyukan noman rani.
Ministan ya yaba da kokarin gwamnatin jihar Jigawa da manoma, bisa goyon bayan shirin gwamnatin tarayya na bunkasa noman alkama, ta hanyar samar da kayan amfanin gona da dabarun zamani.
A nasa jawabin, Gwamna Umar Namadi ya jaddada kudirin gwamnatin jihar na bullo da wasu tsare-tsare da za su samar da guraben ayyukan yi da wadata kasa da abinci.
A cewarsa, tuni ya sayo taraktoci 300, ingantattun irin shuka, da sauran kayayyakin aikin gona domin noman amfanin gona daban-daban a fadin kananan hukumomin jihar 27.
Tun da farko a jawabinsa na maraba kwamishinan noma da albarkatun kasa na jihar Alhaji Muttaqa Namadi ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta bayar da tan 3,500 na ingantaccen irin alkama, da injinan ban ruwa 10,000 domin tallafawa noman alkama a jihar.
Ministan da mukarrabansa da Gwamna Umar Namadi sun ziyarci gonakin alkama da dama a Yakasawa da Dabi a karamar hukumar Ringim.
Rediyon Najeriya ya ruwaito cewa, kayayyakin da gwamnatin tarayya ta bayar sun hada da injinan ban ruwa 10,000, da lita 10,000 ta maganin kwari, taki na ruwa da injinan feshi.
Wasu daga cikin manyan baki da suka halarci bikin sun hada da, Darakta Janar na Gidan Rediyon Tarayya FRCN, Dr Mohammed Bulama, da sarakuna da malaman addini, da wakilan kungiyar sarrafa fulawa ta kasa, da manoman alkama da wasu manyan jami’an gwamnati.
Usman Muhammad Zaria
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Gwamnatin tarayya Jigawa gwamnatin tarayya ta gwamnatin jihar jihar Jigawa
এছাড়াও পড়ুন:
An shawarci Manoman Kwara Da Su Yi Taka-Tsan-Tsan Saboda Hasashen Ruwa Da Tsawa A Jihar
An yi kira ga manoma a jihar Kwara da su yi taka tsan-tsan domin hasashen za a samu ruwan sama da kuma tsawa da ake hasashen nan da kwanaki masu zuwa.
A wata sanarwa da kwamishinan noma da raya karkara na jihar, Dr, Afees Abolore ya fitar, ya ce a cewar hukumar kula da yanayi ta Najeriya, NiMet, ana sa ran wasu sassa na jihar za su fuskanci ruwan sama da kuma yiwuwar tsawa.
Ya ce za a fuskanci ruwan sama ne da rana da yamma, tsakanin Litinin 28 ga Yuli da Laraba 30 ga Yuli, 2025.
Ya yi bayanin cewa duk da cewa ba a sami ruwan sama ba tukuna, yanayin da ke gaba zai iya kawo cikas ga ayyukan noma da ake ci gaba da yi, musamman ga masu sharefilaye, da watsin taki, ko girbin amfanin gona.
Ya yi nuni da cewa wuraren da ke da ƙarancin magudanar ruwa ko kuma waɗanda ke kusa da hanyoyin ruwa na iya zama mafi haɗari ga ambaliya.
Sanarwar ta shawarci manoman da su daina amfani da takin zamani domin gujewa wankewa da almubazzaranci, da kuma girbi manyan amfanin gona da wuri domin hana lalacewa daga ruwan sama.
Yana ƙarfafa manoma da su ɗauki hasashen da gaske kuma su hanzarta yin aiki don rage cikas da kiyaye rayuwarsu.
REL/ALI MUHAMMAD RABIU