Gwamnatin Tarayya Ta ƙaryata Zargin Tigran Gambaryan Kan Jami’an Gwamnatin Nijeriya
Published: 15th, February 2025 GMT
Sai dai ya ce, dole ne a fayyace gaskiya don hana wannan yaudarar samun gindin zama.
Ya ce: “Karo na farko da Mista Gambaryan da tawagar sa suka zo Nijeriya, sun zo ne karan kansu ba tare da wata gayyata daga gwamnati ba. Sai dai da aka sanar da gwamnati wani batu na neman cin hanci a lokacin, sai aka buɗe bincike nan take, ko da yake babu wanda ya shigar da ƙorafi kai-tsaye.
Ya bayyana cewa, ziyarar Gambaryan ta biyu ta kasance wani ɓangare na bincike kan yadda ake amfani da kamfanin hada-hadar kuɗi na Binance don sarrafa darajar naira.
Ya ce, amma binciken ya gamu da cikas sakamakon dabarun da Gambaryan da tawagar sa suka yi amfani da su.
Ministan ya ƙara da cewa, Gambaryan ya samu ‘yanci a watan Oktoba na 2024 bisa dalilai na jinƙai, bayan cimma matsaya tsakanin Nijeriya da Amurka da ta kawo fa’ida ga Nijeriya.
Ya kuma ce gwamnati ta yi watsi da tayin da Binance ya yi na biyan dala miliyan 5 domin a saki Gambaryan, inda ta amince da wata yarjejeniya mai amfani da gwamnatin Amurka.
“Muna ƙaryata duk wata magana da Mista Gambaryan ke yi kan jami’an gwamnati da ke da hannu a shari’ar sa, kuma muna kira ga jama’a da su yi watsi da waɗannan ƙarairayi baki ɗaya,” inji Idris.
Ministan ya bayyana cewa zargin da Gambaryan ke yi babu hujja, kuma bai da inganci duba da cewa yana ƙoƙarin ɓata suna da razana waɗanda suka tabbatar an gurfanar da shi a gaban shari’a ne.
Ministan ya ce yana da yaƙinin cewa, tsarin shari’a na Nijeriya da na Amurka za su ba Gambaryan damar gabatar da hujjoji kan zarge-zargen da yake yi.
A halin yanzu, ya buƙaci ‘yan ƙasa da su yi hankali kada su faɗa tarkon waɗannan ƙarairayi da ƙazafi da wannan Ba’amurken yake yaɗawa.
এছাড়াও পড়ুন:
Takht Ravanji: Iran Ba Za Ta Taba Yin Tattaunawa Akan Dakatar Da Tace Sanadarin Uranium Ba
Mataimakin ministan harkokin waje mai kula da bangaren siyasa, ya bayyana cewa; Ko kadan ba a bijiro da batun dakatar da tace sanadarin uranium a Iran ba, ko kuma batun makamanta masu linzami.
Mataimakin ministan harkokin wajen na Iran ya tabbatar da cewa, wadannan abubuwan biyu wato dakatar da ci gaba da tace sanadarin uranium da kuma makamai masu linzami, jan layi ne da jamhuriyar musulunci ta Iran ba za ta bari a ketara su ba ba kuma za ta bari a bude tattaunawa akansu ba.
Kwamitin da yake kula da tsaron kasa da kuma siyasar waje a majalisar shawarar musulunci ta Iran a karkashin jagorancin dan majalisar Ibrahim Ridhazi ya yi taro a ranar Lahadin da ta gabata, inda aka gayyaci mataimakin ministan harkokin wajen domin jin ta bakinsa akan abubuwan da suke faruwa a tattaunawar da ake yi ba kai tsaye ba da Amurka.
Ridha’i ya fada wa ‘yan jarida cewa Takht Ravanji ya kammadar da rahoto akan yadda tattaunawar take gudana a tsakanin Amurka da Iran da kasar Oman take shiga Tsakani.
Haka nan kuma ya ce; Tace sanadarin Uranium a cikin gida wani jan layi ne da ba za a tsallake shi ba.