An kama ’yan ina-da-kisa 47 a Kwalejin Tarayya a Kebbi
Published: 11th, February 2025 GMT
’Yan sanda sun kama gungun wasu makiyaya 47 ɗauke da makamai kan zargin kutse da yunƙurin aikata kisa a Kwalejin Kimiyya da Ƙere-kere ta Tarayya ta Umaru Waziri da ke Shinkafi a Jihar Kebbi.
Kakakin ’yan sandan Jihar Kebbi, CSP Nafi’u Abubakar ya ce makiyayan sun haɗa baki ne da wani mutum wajen rusa katangar makarantar suka kutsa cikinta da garken shanu sama da 300.
Ya ce da shigarsu ke da wuya. sai suka zarce zuwa ɓangaren gidajen ma’aikata suka lalata musu haki.
Ya ƙara da cewa makiyayan sun kuma sari wani jami’in tsaron makarantar da adda a ƙafarsa ta dama a hannunsa na dama.
Dalibai 179 sun kammala Dirigi da Daraja ta Ɗaya a Jami’ar Bayero Gwamnan Zamfara ya gindaya sharaɗin sulhu da ’yan bindiga“A sakamakon haka ya samu karaya a ƙafar damsa kuma yanzu ana jinyar sa a Asibitin Koyarwa na Tarayya da ke Birnin Kebbi,” in ji CSP Nafi’u Abubakar.
Ya ce Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kebbi, Bello M Sani, ya jagoranci tawagar masu bincike zuwa wurin domin tantance abin da ya faru.
Sanarwar ta ce, “A yayin da ake ci gaba da bincike, mutum 47 daga cikinsu sun riga sun shiga hannu kuma nan gaba za a gurfanar da su a kotu.”
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Yan Sanda
এছাড়াও পড়ুন:
Sojoji Sun Kama Mutum 2 Da AK-47 A Taraba
A yayin bincike, waɗanda ake zargin sun taimaka wajen gano bindiga ƙirar AK-47 guda ɗaya da wata bindiga mai harsashi 16, wayar salula ƙirar Tecno guda ɗaya, da babur ƙirar Bajaj guda ɗaya.
Kwamandan ya ƙara da cewa suna ci gaba da binciken su, kuma ya tabbatar da cewa rundunar ba za ta bar masu laifi su samu wurin fakewa ba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp