FERMA Ta Sake Jaddada Sadaukarwar Da Take Yi Na Kula Da Hanyoyin Tarayya
Published: 13th, March 2025 GMT
Hukumar kula da tituna ta tarayya (FERMA) ta jaddada kudirinta na kula da titunan gwamnatin tarayya da inganta ababen more rayuwa a fadin kasar nan.
Daraktan hukumar ta FERMA, Injiniya Kabiru Iliyasu Dan-Mulki ne ya bayyana haka a lokacin da ya karbi bakuncin shugabannin kungiyar ‘yan jarida ta kasa (NUJ) daga gidan rediyon tarayya (FRCN) da kuma gidan talabijin na Najeriya (NTA) Kaduna a ofishinsa da ke Kaduna.
Injiniya Dan-Mulki ya jaddada babban nauyin da ya rataya a wuyan hukumar ta FERMA na tabbatar da cewa titunan gwamnatin tarayya sun kasance masu kyau domin saukaka zirga-zirga a fadin kasar nan. Ya bayyana muhimmancin hada hannu da masu ruwa da tsaki, musamman kafafen yada labarai, domin wayar da kan jama’a game da ayyukan hukumar da kuma muhimmiyar rawar da take takawa wajen ci gaban kasa.
A nasu jawabin, shugaban kungiyar ta NUJ FRCN na Kaduna, Kwamared Umar Sarkin Fada, da sakataren kungiyar ta NUJ NTA Kaduna, Haruna Mohammed, sun jaddada bukatar hada kai wajen inganta ayyukan FERMA. Sun bayyana cewa ziyarar na da nufin karfafa hadin gwiwa wajen tallata ayyukan hukumar da karfafa gwiwar ‘yan kasar da su bayar da tasu gudummawar wajen kiyaye ababen more rayuwa.
Shugabannin kungiyar ta NUJ sun kuma bayyana damuwarsu kan rashin kyawun wasu hanyoyin gwamnatin tarayya da kuma harabar manyan cibiyoyin gwamnatin tarayya da suka hada da FRCN da NTA Kaduna. Sun bukaci FERMA da ta magance wadannan matsalolin a matsayin wani bangare na alhakinta na zamantakewa (CSR).
Sun yabawa hukumar ta FERMA bisa jajircewarta na kula da tituna tare da bada tabbacin hukumar na cigaba da bayar da goyon bayan kafafen yada labarai wajen sanar da ‘yan Najeriya kokarin da take yi na inganta ababen more rayuwa a fadin kasar.
Shamsuddeen Mannir Atiku
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: gwamnatin tarayya
এছাড়াও পড়ুন:
Nazarin CGTN: Ana Kara Bayyana Rashin Gamsuwa Da Sabuwar Gwamnatin Amurka Daga Ciki Da Wajen Kasar
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp